Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce farashin mai bai tashi sosai ba duk da rufe mashigin ruwa na Hormuz, yana mai cewa: “Mun karɓi mai mai yawa daga gare su. Mutane ba su san haka ba, kuma duk wannan ya faru ne cikin wata ɗaya da rabi kacal.”
A wata hira da ya yi ta talabijin, Shugaban Amurkan ya sake jaddada cewa ya lalata jiragen ruwan yakin Iran da kuma dukkan jiragen saman rundunar sojin saman Iran.
“Daga ƙarshe sun fahimci cewa ba su da na’urorin hangen jirage na rada kuma, domin an lalata tsarin radarsu. Saboda haka muka kai musu hari cikin dare da kuma a cikin duhu.”
“Rundunar ruwanmu mai ƙarfi ta ƙaƙaba mafi girman takunkumi da aka taɓa gani, inda suka yi wa tashoshin Iran ƙawanya kuma tsawon watanni biyu babu wani jirgin ruwa da ya iya ketare ƙawanyar. Daga baya muka kusan cimma yarjejeniya, sai muka sassauta ƙawanyar. Ban sani ba, wataƙila za mu iya cimma yarjejeniya.”
Mista Trump ya nace cewa: “Za mu yi nasara ta kowace hanya ce. Ko dai mu cimma yarjejeniya, ko kuma mu kammala lamarin.”
Ya ce kammala murƙushe Iran abu ne mai sauƙi: “Ba zai yi wahala mu gama da ita ba. Amma tabbas, na fi son a samu yarjejeniya, domin ba na son mutane miliyan 91 su fuskanci illa.”
“Za mu iya rusa gadojinsu cikin sa’a guda. Za mu iya lalata cibiyar samar da wutar lantarkinsu. Dukkan waɗancan tashoshin wutar lantarki da suka gina manyan, kyawawa kuma na zamani. Suna da kuɗi da yawa a baya, amma yanzu ba su da kuɗi. Ba mu ba su ko sisin kwabo ba, amma za mu iya katse musu wutar lantarki da kuma lalata tashoshin samar da wutar nasu.”
A kwanaki kaɗan da suka gabata, Mista Trump ya ce ya bai wa Iran mako guda domin ta binne tsohon shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.