KAI TSAYE, Jana'izar Khamenei da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kai tsaye dangane da jana'izar Ayatollah Ali Kahamenei da sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 07/07/2026
Za a kai gawar Ali Khamenei zuwa Najaf bayan kammala jana'iza birnin Qom
Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran za a tafi da gawar marigayi Ayatollah Ali Khamenei zuwa birnin Najaf na ƙasar Iraki a yau, bayan kammala jana'izar da ake yi masa a birnin Qom na Iran.
Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ruwaito cewa babban ɗan marigayin, Mustafa Khamenei, da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, da Kakakin Majalisar Dokokin ƙasar, Mohammad Baqer Qalibaf, za su halarci jana'izar da za a gudanar a Najaf.
Rahotanni sun ce za a gudanar da bukukuwan jana'izar Khamenei a ranar Laraba a biranen Karbala da Najaf na Iraki.
Bayan kammala jana'izar a Iraki, ana sa ran za a mayar da gawarsa Iran domin binne ta a ranar Alhamis a harabar Hubbaren Imam Reza da ke garinsu na haihuwa, Mashhad.
Macron yana cikin ƙoshin lafiya bayan wata fashewa a Damascus
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Faransa ta sanar da cewa Emmanuel Macron na cikin koshin lafiya, bayan rahotonnin AFP cewa an ji ƙarar fashewar wani abu a birnin Damascus a ranar Talata.
Hotunan da aka fitar daga Damascus sun nuna hayaki mai ƙauri a kusa da otal ɗin da Emmanuel Macron ya sauka a lokacin ziyararsa zuwa Syria.
Rahotanni daga Syria sun ce aƙalla mutum 18 sun jikkata sakamakon fashe-fashen da suka auku a tsakiyar Damascus.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa BBC cewa fashe-fashen sun samo asali ne daga bama-bamai biyu da aka ƙera da hannu kuma sun jikkata mutane da dama.
Kafofin yaɗa labarai na Syria sun ruwaito cewa jami’an ‘yan sanda huɗu na cikin waɗanda suka jikkata a lamarin.
A halin yanzu Mista Macron yana babban birnin Syria, inda yake tattaunawa da Shugaba Ahmed Sharaa a fadar shugaban ƙasa, a cewar wata sanarwa daga Fadar Elysee.
Fadar Elysee ta kuma ce ziyarar “na ci gaba kamar yadda aka tsara.”
Mista Macron shi ne shugaban wata ƙasa na farko daga ƙasar Tarayyar Turai da ya ziyarci Syria tun bayan da sabuwar gwamnati ta hau mulki.
Za mu iya gamawa da Iran a ƙanƙanin lokaci amma na zaɓi mu tattauna - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce farashin mai bai tashi sosai ba duk da rufe mashigin ruwa na Hormuz, yana mai cewa: “Mun karɓi mai mai yawa daga gare su. Mutane ba su san haka ba, kuma duk wannan ya faru ne cikin wata ɗaya da rabi kacal.”
A wata hira da ya yi ta talabijin, Shugaban Amurkan ya sake jaddada cewa ya lalata jiragen ruwan yakin Iran da kuma dukkan jiragen saman rundunar sojin saman Iran.
“Daga ƙarshe sun fahimci cewa ba su da na’urorin hangen jirage na rada kuma, domin an lalata tsarin radarsu. Saboda haka muka kai musu hari cikin dare da kuma a cikin duhu.”
“Rundunar ruwanmu mai ƙarfi ta ƙaƙaba mafi girman takunkumi da aka taɓa gani, inda suka yi wa tashoshin Iran ƙawanya kuma tsawon watanni biyu babu wani jirgin ruwa da ya iya ketare ƙawanyar. Daga baya muka kusan cimma yarjejeniya, sai muka sassauta ƙawanyar. Ban sani ba, wataƙila za mu iya cimma yarjejeniya.”
Mista Trump ya nace cewa: “Za mu yi nasara ta kowace hanya ce. Ko dai mu cimma yarjejeniya, ko kuma mu kammala lamarin.”
Ya ce kammala murƙushe Iran abu ne mai sauƙi: “Ba zai yi wahala mu gama da ita ba. Amma tabbas, na fi son a samu yarjejeniya, domin ba na son mutane miliyan 91 su fuskanci illa.”
“Za mu iya rusa gadojinsu cikin sa’a guda. Za mu iya lalata cibiyar samar da wutar lantarkinsu. Dukkan waɗancan tashoshin wutar lantarki da suka gina manyan, kyawawa kuma na zamani. Suna da kuɗi da yawa a baya, amma yanzu ba su da kuɗi. Ba mu ba su ko sisin kwabo ba, amma za mu iya katse musu wutar lantarki da kuma lalata tashoshin samar da wutar nasu.”
A kwanaki kaɗan da suka gabata, Mista Trump ya ce ya bai wa Iran mako guda domin ta binne tsohon shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
An nemi Iraniyawa su shigar da ƙorafi kan raɗaɗin rashin Khamenei
Asalin hoton, Getty Images
Ministan Shari'a na Iran: Mutane na iya shigar da ƙara saboda "raɗaɗin tunani da na zuciya da rashin jagora ya haifar."
Ministan Shari'a na Iran, Amin Hossein Rahimi, ya bayyana cewa Ma'aikatar Shari'a da gwamnati sun samar da dukkanin hanyoyin da suka dace domin mutane su shigar da ƙorafe-ƙorafe da ƙara dangane da "lahanin tunani da na ƙwaƙwalwa da rasuwar jagoran ƙasar ta haifar musu".
Ya ce ana iya yin hakan ta hannun lauyoyi ba tare da biyan kuɗi ba, a gaban hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa.
"Ana ci gaba da bibiyar laifukan da maƙiya suka aikata a ƙungiyoyi da kotunan ƙasa da ƙasa da kuma hukumomin cikin gida, kuma an tattara hujjoji masu ƙarfi kan lamarin."
Ya ƙara da cewa:
"Bisa doka, hukumomin shari'a na Jamhuriyar Musulunci ta Iran suna da ikon binciken waɗannan laifuka, kuma akwai yiwuwar gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata su, ciki har da gwamnatin Amurka da kuma gwamnatin Isra'ila."
Ministan ya kuma bayyana akwatin gawar jikar Ali Khamenei a matsayin "shaidar irin zaluncin da aka yi wa jagoran Iran", inda ya kwatanta lamarin da Ali Asghar, ɗan Imam Husaini bn Ali, Imam na uku a wajen mabiya Shi'a.
A ƙarshe, Rahimi ya jaddada cewa "Wannan wata fafatawa ce ta shari'a da za ta gudana tare da sauran fannoni na tinkarar waɗanda suka aikata wannan hari."
An gabatar da hujjoji a gaba kotu kan Charlie Kirk
Asalin hoton, Getty Images
Masu gabatar da ƙara a jihar Utah ta Amurka sun gabatar da hujjoji a gaban wata kotu gabanin shariar da za a yiwa mutumin da ake zargi da kashe fitaccen mai ra'ayin rikau din nan , Charlie Kirk.
Suna ƙoƙarin gamsar da alƙali cewa suna da shaidar da za su iya amfani da ita wajan gurfanar da wanda ake zargin, Tyler Robinson, a gaban kotu domin fara shari'a.
Har yanzu Robinson bai bayyana ko ya amsa ko ya musanta zargin da ake yi masa ba.
Mista Kirk, wanda ke da kusanci da Shugaba Trump, ya mutu ne bayan an harbe shi yayin da yake jawabi ga ɗalibai a harabar wata jami'a a watan Satumban bara.
An fara gudanar da jana'izar Khamenei a birnin Qom.
Asalin hoton, Getty Images
Bayan kammala jana'izar a hukumance da aka yi wa tsohon jagoran Jamhuriyar Musulunci a Tehran, tare da kai akwatin gawarsa da kuma na wasu daga cikin 'yan iyalansa da aka kashe tare zuwa birnin Qom, an fara gudanar da jana'izarsa a hukumance a wannan birni da ke lardin tsakiyar ƙasar.
Kamar yadda aka ruwaito, Ayatullah Javadi Amoli ne ya jagoranci sallar jana'izar a Masallacin Jamkaran da ke Qom, sannan aka fara gudanar da jana'izar a gaban dubban magoya bayan marigayi Ali Kahamenei
Bayan wannan taro, za a gudanar da wani makamancin taron jana'izar a birnin Najaf bayan an kai gawarwakin zuwa Iraki.
Daga bisani kuma, za a kammala jerin jana'izar a birnin Mashhad ranar Alhamis.
BBC ta gano yadda Rasha ke tsare da dubban fararen hula ƴan Ukraine
Wani binciken da BBC ta gudanar ya samu shaidu da suka nuna cewa Rasha na tsare dubban fararen hula 'yan Ukraine a cibiyoyin tsare mutabe , inda ake zargin ana yi wa wasu azabtarwa da cin zarafin ta hanyar fyade.
An kiyasta cewa fararen hula 'yan Ukraine kusan 16,000 ne aka tsare ko kuma suka bace tun daga shekarar 2014.
Wata mata da aka saki a wani shirin musayar fursunoni ta shaida wa BBC cewa an yi mata fyade , sannan an tilasta mata cin ɗanyen abinci da aka gauraya da ƙasa da shara.
Ta ce a cikin tsawon shekaru da kwana goma sha uku na rayuwarta ruhi na da jikina sun kasance cikin matsananciyyar nakasa.
Ofishin Jakadancin Rasha da ke London ya ce Rasha ta dade tana nuna goyon bayan mutunta dokokin yaki , kuma hukumomin ƙasar na bincike kan duk wani zargi da ya shafi aikata laifukan yaƙi."
Shugabannin NATO na taro a Turkiyya kan yaƙin Ukraine da Russia
Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO na taruwa a Turkiyya domin halartar wani taron koli.
Gabanin taron, Babban Sakataren kungiyar ta NATO ya bukaci mambobin ƙungiyar su ci gaba da bai wa Ukraine goyon baya, yayin da Rasha ta ƙara kai hare-hare da makamai masu linzami.
Wakilin BBC ya ce jamian kungiyar ta Nato sun nuna damuwa akan Rasha da Ukraine da kuma matakan da turai za ta dauka domin ta kare kanta.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa na fuskantar ƙarancin makaman kariya da ake amfani da su wajen kakkabo makamai masu linzami.
Buɗewa
Masu bibiyarmu barkan ku da safiyar ranar Talata a watan Yulin 2026. Da fatan kun wayi gari lafiya. Allah ya sa hakan.
Yau ma kamar kullum mun dawo da shafinmu na kai tsaye inda muka kawo muku bayanai dangane da al'amuran da ke faruwa a jana'izar jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Kahamenei da sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.