Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/09/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/09/2025.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Habiba Adamu

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu nan za mu rufe shafin namu a yau.

    Kuna iya dubawa ƙasa domin karanta rahotonnin da muka kawo muku a wunin na yau.

    Mu kwana lafiya.

  2. Jihar Kano ce kan gaba a sakamakon jarrabawar NECO ta 2025

    Gwamnan Kano

    Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf

    Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar da sakamakon jarrabawar wannan shekara ta 2025.

    Sakamakon ya nuna cewa kashi 60.26 cikin 100 na waɗanda suka samu kiredita biyar zuwa sama ciki har da darussan Lissafi da Turanci.

    Shugaban hukumar Farfesa Ibrahim Wishishi ya shaida wa BBC cewa jihar Kano ce kan gaba a yawan ɗaliban da suka samu nasara a jarrabawar a faɗin wuraren da hukumar ke shirya jarrabawar da suka haɗa da wasu ƙasashen Afirka.

    Cikin wata sanarwa da gwamnatin Kanon ta fitar ta ce wannan ne karon farko cikin shekara 25 da jihar ta samu wannan nasara.

    Shugaban na NECO ya ce cikin ɗalibai 1,358,339 da suka rubuta jarrabawar, yayin da 818,492 ne suka samu kiredit a darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.

  3. Sojojin Lebanon sun gano wani magani mai yawa da aka haramta a ƙasar

    Rundunar sojin Lebanon ta ce ta ƙwace ƙwayar wani haramtaccen magani mai suna Captagon har guda miliyan sittin da huɗu.

    Wani mai magana da yawun sojin ya ce sun kai wani samame a birnin Boudai, inda su ka kuma gano sinadarai da injinan da ake buƙata wajen haɗa ƙwayoyin.

    Ƙasar ta Lebanon na ta shan matsi daga ƙasashen yankin Gulf don kawo ƙarshen haɗa ƙwayar Captagon, wanda ake yawan amfani da shi a yankin domin ƙara kuzari.

    A baya ana ganin gwamnatin Bashar al Assad ce ke samar da ƙwayoyin, amma tun bayan da aka kifar da gwamnatinsa, ana zargin Hezbollah da karɓe ragamar samar da ƙwayar domin samun kuɗaɗen shiga.

  4. Fasahar AI ta gano cutar da za ta kama mutane a shekara 10 masu zuwa

    Wani mutum mutumi na duba marasa lafiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu bincike a Turai sun yi amfani da fasahar ƙirƙirariyyar basira ta AI don yin hasashen matsalolin lafiya da ɗaiɗaikun mutane za su iya fuskanta cikin shekaru goma masu zuwa ko fiye na rayuwarsu.

    Sun ce fasahar na amfanin da bayanan rashin lafiyar da mutum ya yi a baya, domin hasashen cutuka fiye da dubu ɗaya da ke barazanar kama mutum, tun ma kafin soma bayyana.

    An wallafa cikakkun bayanan binciken - da suka bayyana da gagarumar nasara - a mujallar kiwon lafiya ta Nature.

    An horar da fasahar AI ɗin ta hanyar amfani da bayanan lafiyar mutane dubu ɗari huɗu - da ba a bayyana sunayensu ba - a Birtaniya da Denmark.

    Zuwa yanzu ba a soma amfani da fasahar ba, sai dai ana sa ran yin amfani da ita wajen gano cutuka da wuri a mutanen da suka fi barazanar kamuwa da cutuka.

  5. Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da sabbin jiragen ruwa na zamani a jihar

    Gwamnan da wasu mutanensa cikin sabon jirgin

    Asalin hoton, Sokoto State Gov.

    Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙaddamar da sabbin jiragen ruwa masu ɗaukar mutum 20 da rigunan kariya 2,000 a yankunan jihar da ke kusa da koguna.

    Yayin ƙaddamar da aikin a garin Dundaye da ke yankin ƙaramar hukumar Wamako, gwamnan jihar Ahmad Aliyu ya ce gwamnatinsa da ɗauki matakin ne da nufin kare lafiya da dukiyoyin al'ummomin jihar da ke rayuwa a kusa da koguna.

    Wasu daga cikin jiragen ruwan

    Asalin hoton, Sokoto State Gov.

    Gwamnan ya ce matakin zai taimaka wajen inganta lafiyar sufurin ruwa da nufin rage yawan hatsuran da ake yawan samu a kwale-kwale a gokuna da tafkunan jihar.

    Ya ƙara da cewa sabbin jiragen za su taimaka wa manoma don zuwa gonakinsu, musamman a yanayin ambaliya.

    Ahmad Aliyu ya ce a yau gwamnatinsa ta raba sabbin jiragen 20 da rigunan kariya 1,000 ga ƙananan hukumomi 10.

    Gwamnan da wasu mutane a cikin jirgin ruwa

    Asalin hoton, Sokoto State Gov

    To sai dai gwamnan ya gargaɗi matuƙa sabbin jiragen ruwan su guji loda fasinjoji fiye da abin da aka ƙayyade wa jirage, yana mai cewa duk direban da ka samu da kauce wa dokar zai ɗanɗana kuɗarsa.

    A shekarun baya-bayan nan ana yawaitar samun hatsarin kwale-kwale a kogunan Najeriya, wani abu da masana ke alaƙantawa da rashin ingancin jiragen da ƙarancin riguan kariya.

  6. Ya kamata FRSC ta binciki bayanan hatsuran motocin Dangote - DAPPMAN

    motoci

    Asalin hoton, Dangote

    Ƙungiyar masu defo-defon man fetur ta Najeriya (DAPPMAN) ta yi kira da hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta ƙasar ta binciki bayanan zirga-zirga da haɗuran motocin kamfanin Dangote.

    Kiran na zuwa ne kwana biyu bayan matatar mai ta Dangote ta ƙaddamar da manyan motocin dakon man fetur masu amfani da gas, daga matatar zuwa gidajen mai a faɗin ƙasar.

    “Yayin da DAPPMAN ke goyon bayan fara amfani da motoci masu amfani da gas, saboda rashin gurɓata muhalli, amma bai kamata a yi watsi da kiyaye hatsura ba'', a cewar ƙungiyar kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

    DAPPMAN ta zargi direbobin kamfanin Dangote da haddasa munanan haɗurra a kan titunan Najeriya.

    “Kamfanin Dangote na da tarihin munanan haɗurra sakamakon rashin ƙwarewar direbobin kamfanin'', kamar yadda sanarwar kungiyar ta yi bayani.

    Ta ƙara da cewa ƙara manyan motoci 4,000 zuwa kan titunan Najeriya da suka riga suka lalace ba tare da bai wa direbobin horo ba, babban hatsari ne da zai iya ƙara haifar da munanan hatsura ga motocin, kuma a wannan karo suna ɗauke da fetur.

  7. 'Binciken kimiyya ya nuna guba ce ta kashe Alexei Navalny'

    Alexei Navalny

    Asalin hoton, Reuters

    Matar marigayi Alexei Navalny - ɗan fafutukar kare haƙƙin bil'adama a Rasha - ta ce sabbin bayanan kimiyya sun tabbatar da cewa mijinta ya mutu ne sakamakon gubar da aka sanya masa.

    Mista Navalny ya mutu a watan Fabrairun 2024 ba-zato ba tsammani, a yayin da yake zaman gidan yari na tsawon shekara 19 a wani gidan yari da ke wani yanki mai tsananin sanyi a ƙasar.

    Sai dai matar marigayin, Yulia Navalny ta ce a lokacin da ya mutu an yi nasarar fitar da samfurin ƙwayoyin halittar jikinsa a sirrance.

    A cikin wani bidiyo da ta wallafa, ta ce an gwada ƙwayoyin halittar a ɗakunan gwaje-gwaje a ƙasashe biyu, kuma dukkaninsu sun tabbatar cewa guba ce ta kashe shi.

  8. Tinubu ya kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

    Fubara da Tinubu da Wike

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kawo ƙarshen dokar ta-ɓaci na tsawon wata shida da ya sanya wa jihar Rivers da ke kudu maso kudancin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa daga fadar shugaba ƙasar, ta ambato Tinubu na cewa dokar ta gama aiki daga tsakar daren yau.

    ''Don haka daga gobe Alhamis 18 ga watan Satumba, Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Nma Odu, da mambobin majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagoracin kakakin majalisar jihar, Martins Amaewhule, za su koma aikinsu'', in ji Tinubu.

    A ranar 18 ga watan Maris ɗin da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar bayan rikicin siyasar jihar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin tsagin gwamnan jihar da na ministan Abuja, Nyesom Wike - wanda shi ne tsohon gwamnan jihar.

    Shugaban ƙasar ya ce yana sane da irin ƙararrakin da aka kai saboda ya ayyana dokar ta-ɓacin, to amam ya ce ya ɗauki matakin ne domin kawo ƙarshen halin rikicin siyasa da jihar ta shiga a lokacin.

  9. Democrats ta yi kankankan da Republican a majalisar jihar Minnesota

    Jam'iyyar Democrats ta lashe zaɓen cike gurbin ɗan majalisa da aka yi a jihar Minnesota da ke Amurka.

    XP Lee ya samu nasarar ne domin maye gurbin gurbin Melissa Hortman, 'yar jam'iyyar da aka kashe a watan Yunin daya gabata.

    Nasarar XP Lee, ta kawo raba dai dai a tsakanin manyan jam'iyyun ƙasar a majalisar dokokin jihar.

    Wani mutum da ya yi shigar burtu a matsayin ɗan sanda ne ya harbe Ms Hortman da mijinta a gidansu.

    Mutumin da ake zargi da kisan, Vance Boelter, an kuma zarge shi da raunata wani ɗan jam'iyyar ta Democrats a ranar da ya kashe Ms Hortman da mijinta.

    Ya dai ki amsa laifukan da aka tuhume shi da aikatawa ciki har da kisa.

  10. Kotu ta yanke wa ɗan TikTok hukuncin ɗauri a Ghana

    ,,,,

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a ƙasar Ghana ta yankewa wani mashahurin ɗan Tik Tok, David Kwodow Prah Afful, wanda aka fi sani da Kwame Nkrumah II, ɗaurin wata bakwai a gidan kurkuku.

    Kotun ta same shi da laifin barazanar kashe shugaban ƙasar da wasu ƴanmajalisar dokokin ƙasar a wani faifan bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta.

    Afful ya amince da tuhume-tuhumen da aka yu masa, sai dai ya nuna nadama ya kuma nemi afuwan shugaban ƙasar da ƴanmajalisar.

    A wata shari'ar ta daban kuma, an gurfanar da wasu ƴan TikTok biyu bisa zarginsu da amfani da kalamai masu kaushi kan shugaban ƙasar.

    Inda a wani bidiyon da suka watsa kai tsaye suka ce " Da za mu fi farin ciki da ace shugaba John Dramani Mahama ne ya mutu a hatsarin jirgi mai saukar ungulun da ya faru, kuma wadanni su cinye shi"

    Shugaban ƙasar ya ce gwamnati na duba yiwuwar yadda za ta tsaftace kafafen sada zumunta, inda ya umarci wata hukuma ta bibiyi masu kalaman ƙiyayya a shafukan.

  11. Mali za ta ɗauki mataki kan hanyoyin da ƴanta'adda ke rufewa

    ,,,,

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin mulkin sojin Mali na ƙoƙarin kwantar da hankali bayan fusatar da aka yi kan rufe manyan hanyoyin da ƴanta'adda ke yi, suna yiwa direbobin manyan motoci kwanton-ɓauna da ƙona musu motoci.

    Firaiministan ƙasar, Abdoulaye Maïga ya ce za su ɗauki matakai don inganta tsaro a manyan hanyoyin.

    Kalaman da ke nuni da cewa gwamnatin ta fito ta amince da munin yanayin da ake ciki.

    Rufe manyan hanyoyin na nuni da yadda ayyukan masu ikirarin jihadin ke ta'azzara, lamarin da ya gurgunta rarraba man fetur a ƙasar.

    Yankin Sahel da ke Afrika ta yamma ya yi ƙaurin suna wurin ayyukan ta'addanci, inda ya ke da kashi 50 cikin ɗari na mace-macen da ake samu sakamakon ayyukan ta'addanci a duniya.

    Masu sharhi da dama na ganin manufar ƙungiyar da ke da alaƙa da Alqa'ida uta ce ta rufe hanyar da ke kaiwa ga babban birnin ƙasar, Bamako.

  12. Sojojin Najeriya sun cafke kwamandan IPOB

    ,,,,

    Asalin hoton, HQ Nigerian Army

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama Ifeanyi Eze Okorienta, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB mai neman ɓallewa daga Najeriya.

    Dakarun sun damƙe kwamandan wanda ake yi wa laƙabi da "Gentle de Yahoo, sun kuma kwato makamai da suka hada da bindigogi kirar Turai da albarusai da kuma kakin sojoji da na 'yan sanda.

    Jama'an tsaron sun bayyana cafke Eze a matsayin wani babban koma-baya ga ƙungiyar ta IPOB da sashen ƙungiyar mai ɗauke da makamai da ke kudu-maso-gabashin ƙasar.

    Hakan na zuwa ne makonni bayan wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa wani jagoran ƙungiyar, Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari, bisa samunsa da aikata laifukan ta'addanci.

  13. An ceto yaran da aka sace daga arewaci zuwa kudancin Najeriya

    ,,,,

    Asalin hoton, DSS/Facebook

    Hukumar da ke yaƙi da safarar mutane a Najeriya, NAPTIP, ta ce ta ceto wasu yara takwas da ake zargin an sace su ne daga wasu jihohin arewacin ƙasar ciki har da jihar Kano.

    Kakakin hukumar, Vincent Adekoye, ya ce an gano yaran ne a wani gidan marayu da ya yi suna a garin Asaba da ke jihar Delta a kudancin ƙasar.

    Hukumar farin kaya ta DSS da jami'an ƴansanda da na civil defence ne suka ceto yaran a yayin wani samame da suka kai a gidan marayun.

    Ƙawancen jamu'am tsaron sun kai samamen ne bayan ƙorafe-ƙorafen da iyayen yara suka kai na cewa ƴaƴansu sun ɓata a jihar Kano da wasu maƙwabtan jihohi.

  14. Fari na barazanar janyo mummunar yunwa a Syria

    ,,,

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar kula da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana fargabar cewa matsalar yunwa za ta munana a Syria, muddin ba a kai musu ƙarun tallain abinci ba ko kuma ƙasar ta sami damar shigar da alkama ba.

    Babban jami'in hukumar a ƙasar, Piro Tomaso Perri ne ya bayyana hakam, yayin da ƙasar ke fuskantar ƙamfan ruwan sama.

    Wani rahoto na hukumar ya yu ƙiyasin cewa Syria zata fuskanci raguwar tan miliyan 2.73 na alkama a wannan shekarar, abin da zau iya wadatar da nuƙatar mutane miliyan 16.25.

    Gonaki alkama a wajen Seqalbia, da ke kusa da birnin Hama da ke Syria sun bushe sun yi fayau .

    Wani manomi, Maher Hadda ya ce gonarsa mai eka 40 ta samar masa da kashi ɗaya ne bisa uku na abin da ya saba nomawa.

    " Matsalar ta fi muni a bana saboda fari," a cewar manomin mai shekara 46. "ba mu farfado daga abin da muak kashe a harkar noma ba, mun yi asarar kuɗi don ba zan iya noma a badi ba, kuma sai na nemi abinci a bana."

    Haka batun yaki a fadin Syria, inda farin da ba'a taɓa gani ba a cikin shekara 36 ta zaftare alkamar da ake samu da kash 40 cikin ɗari, a ƙasar da kusan kashi 90 cikin dari na al'umarta ne ke fama da talauci. Kuma a yanzu take gab da shiga matsalar ƙarancin abinci.

  15. Saudiyya ta saki ƴan Najeriya da aka zarga da safarar miyagun ƙwayoyi

    ,,,

    Hukumomin Saudi Arabia sun saki wasu ƴan Najeriya uku da aka tsare a Jidda, bayan an zarge su da safarar miyagun ƙwayoyi

    Mutanen da aka saka su ne Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddieq.

    Wasu gungun mutane da ke aiki a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Mallam Aminu da ke Kano (MAKIA) ake zargi da manna sunayen mutanen uku a wasu akwatuna da ke ƙunshe da muyagun ƙwayoyin.

    Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ce ta sanar wa manema labarai batun sakin mutanen uku.

    Unda ta ƙara da cewa mutanen uku ce sun ɗauki akwatunan miyagun kwayoyin sun shiga jirgin Ethiopian Airline ET940 da ya bar Kano zuwa Jidda a ranar 6 ga watan Agusta, 2025, domun yun umara.

    Kuma bayan isarsu Jidda ne aka kama su.

    Binciken da aka yi ya kai ga kama wani mai shekara 55 Mohammed Ali Abubakar da aka fi sani da Bello Karama, wanda shi ne jagoran waɗanda ake zargi da musanya akwatunan da wasu mutum uku, ciki har da ma'aikacin jirgin.

    Tuni aka gabatar da tuhume-tuhume a kan mutanen da ake zargi, Mohammed Ali Abubakar da Celestina Emmanuel Yayock da Abdulbasit Adamu Sagagi da kuma Jazuli Kabir.

  16. Colombia ta gaza yaƙi da muyagun ƙwayoyi - Amurka

    ,,,

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka a hukumance ta ɗauki ƙasar Colombia a matsayin "wadda ta nuna gazawa" wurin ɗaukar nauyin da ya rataya a kanta na yaƙi da safarar muyagun ƙwayoyi.

    Kuma kaɗan ya rage Amurkar ta dakatar da tallafin da take baiwa Colombia.

    A duk shekara gwamnatin Amurkar na dubawa a hukumance ko ƙasashe na bayar da cikakken haɗin kai wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyin da take jagoranta, kuma duk ƙasar da aka samu tana da rauni sai ta dakatar da tallafin da ta ke bata.

    A ranar Litinin Mr. Trump ya ce sarrafa hodar ibilis ɗin da ake yi a Colombia ya yi ƙaruwar da aka daɗe ba a gani ba a ƙarƙashin gwamnatin, Gustavo Petro, abun da gwamnatin ta musanta.

    Sai dai a martanin da ta mayar, gwamnatin Colombian ta ce za ta daina sayen makamai daga Amurka.

    Ministan cikin gaida, Armando Benedetti ya shaida wa kafafen yaɗa labarai na cikin gida cewa za su daina sayen makamai "daga yanzu" daga Amurka.

    Sauran ƙasashen da Amurkar ta ce sun gaza cimma abin da ake so game da yaƙi da miyagun ƙwayoyin sun haɗa da Afghanistan, Bolivia, Myanmar da Venezuela.

  17. Trump na ziyarar aiki a Burtaniya

    ,,,

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya isa Burtaniya a karo na biyu da ya kai ziyarar aiki.

    A lokacin da ya isa gidan jakadan Amurka a Birtaniya da ke London, ya ce ƙasar waje ne mai kyau da kuma sanyaya zuciya.

    A ranar Laraba ne kuma Sarki Charles zai karɓi baƙuncin Mr. Trump, a fadar masarautar Burtaniya da Windsor.

    Wakiliyar BBC ta ce ziyara ce ta aiki da za a yi ta asirrce ba tare da an yi komai a bainar jama'a ba saboda dalilai na tsaro.

    Ziyarar na zuwa ne a yayin da gwamnatin Birtaniya ta sanar da kulla yarjejeniya da wasu kamfanonin Amurka ciki har da Microsoft da kuma Google, inda za a zuba jarin biliyoyin daloli domin bunƙasa ayyukan fasaha da makamantansu.

  18. An gurfanar da wanda ya kashe mai goyon bayan Trump

    ,,,,

    Asalin hoton, Getty Images

    A karon farko mutumin da ake zargi da kashe mai bayan shugaba Trump, Charlier Kirk, ya bayyana gaban kotu a Amurka.

    Tyler Robinson, bai nuna alamun nadama ko tausayi ba a tare da shi a yayin da alkali ke karanta masa tuhumar da ake masa.

    Masu shigar da kara dai na bukatar a yanke masa hukuncin kisa.

    Sun kuma gabatar da wasu sakonni da ake zargin Mr Robinson ya aike wa budursa inda ya ke cewa shi ne ya kashe mutumin a makon da ya gabata.

  19. Ƴanbindiga sun harbe mutum 22 a Nijar

    ,,,,

    Asalin hoton, OTHERS

    Wasu mutane ɗauke da bindigogi a kan babura sun harbe akalla mutum 22 a wani kauye da ke yammacin jamhuriyyar Nijar.

    Wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP, cewa yawancin mutanen an kashe su ne a yayin da suke halartar wani biki.

    Ƙauyen na yankin Tilaberi ne wanda ke da iyaka da Mali da kuma Burkina Faso.

    Shugabannin mulkin sojin ƙasar ya ce gwamnatinsa na ta fadi tashi ganin daƙile ayyukan masu ikirarin jihadi a yankin.

    A ranar Talata ne shugaban ƙungiyar ECOWAS ya kai wata ziyara Burkin Faso don neman haɗin kan ƙsasashen da ke ƙungiyar (AES) ciki har da Nijar wajen yaƙi da mahara da masu tayar da ƙayar baya a yankin na Sahel.

  20. Falasɗinawa na barin Gaza saboda ƙaruwar hare-haren Isra'ila

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban Falasdinawa na ci gaba da tserewa birnin Gaza, kwana guda bayan Isra'ila ta fara kai farmaki ta kasa a kokarin da ta ke na murkushe 'yan Hamas.

    Da ya yawa daga cikinsu sun nufi kudancin Gaza a kafa.

    Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, Shugabannin manyan kungiyoyin agaji fiye da 20 da ke aiki a Gaza ciki har da kungiyar save the children da Oxfam, sun ce halin rashin imanin da ake ciki a Gaza ya munana.

    A mako mai zuwa ne shugabannin kasashen duniya za su tattauna akan yakin da ake a Gaza a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya.