Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Amurka za ta ba gidauniyar agaji ta Gaza tallafin dala miliyan 30

    Amurka za ta ba da tallafin dala miliyan talatin ga Gidauniyar agaji ta Gaza, ƙungiya mai cike da taƙaddama da ke samun goyon bayan Amurka da Isra'ila.

    Ita dai wannan gidauniya an kafa ne domin rarraba kayayyakin jin ƙai a Zirin.

    Wannan ne karon farko da Amurka kai-tsaye za ta bai wa ƙungiyar tallafi.

    Tun ƙarshen watan Mayu gidauniyar take gudanar da ayyukanta a Gaza sakamakon toshe hanyoyin kai jin ƙai da Isra'ila ta yi na tsawon mako goma sha ɗaya.

    A cewar wakilin BBC, tun watan Mayu, an kashe sama da Falasɗinawa ɗari huɗu yayin da suke ƙoƙarin karɓar abinci daga cibiyoyin rarraba kayan jin ƙan.

  2. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'atu babbar rana, inda za mu cigaba da kawo muku labaran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta irin su Facebook da X da Instagram da ma zaurenmu na Whatsapp domin karanta wasu labaran da tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.