Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Rufewa

    Masu bin shafin namu, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonni na yau Juma'a 27/06/2025.

    Sai kuma gobe, Asabar idan Allah ya kai mu.

    Amma kafin nan ku ci gaba da kasancewa da shafin BBChausa.com don samun labarai da kallon bidiyo da hotuna.

  2. Trump zai yi watsi da tattaunawar kasuwanci da Canada

    Shugaba Trump ya ce zai yi watsi da tattaunawar kasuwanci da Canada ba tare da ɓata wani lokaci ba.

    Shugaban na Amurka ya ɗora alhakin wargajewar tattaunawara a kan tsarin harajin intanet wanda ya ce ya hari manyan kamfanonin fasaha.

    Trump ya ce zai sanar da sabon tsarin haraji a kan kayan da Canada ke shigarwa Amurka nan da mako ɗaya.

    Firaminitan Canada Mark Carney, ya ce Ottawa za ta ci gaba da tattaunawar kasuwanci domin kare muradin 'yan ƙasarsa.

  3. Iran ta yi watsi da buƙatar hukumar nukiliya ta duniya ta ziyarar wuraren nukiliyarta

    Iran ta yi watsi da buƙatar hukumar kula da nukiliya ta duniya ta neman ziyartar cibiyoyinta na nukiliya da Amurka da Isra'ila suka kai wa hari, inda Iran ɗin ta ce da wata muguwar manufa hukumar ke son zuwa wuraren.

    Ministan harkokin waje na Iran Abbas Araghchi, ya ce ziyarar ba ta da wani amfani, bayan da hukumar ta ki yin Allah-wadarai da hare-haren.

    A farkon wannan watan majalisar dokokin Iran ta jefa ƙuri'ar dakatar da mu'amulla da hukumar nukiliyar ta duniya (IAEA).

    Shugaba Trump, wanda ya ce an share gaba ɗaya cibiyoyin nukiliya na Iran, ya ce yana son ganin hukumar ta samu cikakkiyar damar duba wuraren.

  4. An kashe mutum 13 a hare-haren RSF a Sudan - Likitoci

    Likitoci a birnin El-Fasher na Sudan sun ce mutum 13 ciki har da yara sun mutu bayan da dakarun RSF suka kai wani sabon hari.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana ƙoƙarin samar musu kayan jinƙai, yayin da dubban mutane suka maƙale a cikin birnin, yayin da ake fama da yunwa a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke makwabtaka da birnin.

    El-Fasher ce kadai da har yanzu ke karkashin ikon sojojin Sudan.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce shugaban rundunar soji ta Ƙasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya amince da tsagaita wuta na mako guda domin bai wa agaji damar shiga.

  5. Tinubu zai je ziyara yankin Karebiyan da taron BRICS a Brazil

    Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja a gobe Asabar domin ziyarar ƙasashe biyu Saint Lucia da Brazil, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga ta bayyana.

    Sanarwar ta ce da farko shugaban zai yada zango a Saint Lucia a ziyarar da zai yi domin kyautata dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasashen yankin Karebiya.

    Daga nan kuma shugaban zai tashi ya nufi Brazil domin halartar taron ƙoli na 17 na ƙungiyar ƙasashe masu haɓakar tattalin arziƙi ta BRICS a birnin Rio de Janeiro, daga ranar 6 – 7, ga watan Yuli mai kamawa, 2025.

    Zai halarci taron ne a matsayin Najeriya na abokiyar tafiyar ƙungiyar.

    Afirka ta Kudu da Masar da Habasha su ne ƙasashen Afirka da ke zaman mambobin ƙungiyar a Afirka.

  6. Isra'ila ta musanta zargin harbin Falasɗinawa masu karɓar agaji

    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya musanta rahoton jaridar Haaretz da ke cewa, an bai wa wasu sojojin Isra’ila umarnin buɗe wuta kan fararen hula marasa makami, da ke jiran karɓar agajin abinci a Gaza.

    Netanyahu ya ce jaridar ta yi wa rundunar sojin da ta fi kowacce bin doka a duniya, ƙage na ƙiyayya.

    Rundunar sojin Isra’ila ta ce dokokinta sun haramta kai hari kai-tsaye kan fararen hula, amma ta ce za ta binciki zargin da aka yi mata.

  7. WHO ta ce har yanzu China ta ƙi bayar da bayanan binciken asalin Korona

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya ce duk da sun yi ta aika bukatu, har yanzu China ba ta mika bayanan da ake bukata domin gano asalin barkewar cutar Korona (Covid-19) ba.

    Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, Ya ce WHO na bukatar samfurin kwayoyin cutar daga farkon waɗanda suka kamu, da kuma bayanai kan yadda ake aiki da tsaron dakunan bincike a Wuhan, inda aka fara gano cutar.

    Ya ce har yanzu ba a kawar da tsammani a kan dukkanin labaran da ake bayarwa a kan asalin cutar - ciki har da wanda ke cewa an samu ɓullar ta ne daga ɗakin gwaje-gwaje na kimiyya da kuma wanda ke cewa ta ɓulla ne daga dabbobi.

    .Ana ƙiyasin cewa annobar ta Covid-19 ta hallaka sama da mutane miliyan 20 a fadin duniya.

  8. JD Kongo da Rwanda sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya

    Ministocin harkokin waje na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da Rwanda sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a babban birnin Amurka, Washington, inda ake agnin hakan a matsayin matakin farko na kawo ƙarshen rikin da suka shafe shekara 30 suna yi a tsakaninsu.

    An yi yarjejeniyar ne wadda Amurka da Qatar suka shirya bayan da 'yan tawayen M23 waɗanda Rwanda ke mara wa baya sun ƙwace sassan Kongon da dama a farkon shekarar nan.

    A ƙarƙashin sharuɗɗan yarjejeniyar da aka ƙara yi, dakarun Rwanda ba za su fice daga ƙasar ta Kongo ba nan take.

    Shugaba Trump ya ce Amurka za su samu damar haƙar ma'adanai da dama daga Kongo a ƙarƙashin yarjejeniyar.

  9. An yi jana'izar karramawa ga tsohon shugaban Laberiya Samuel Doe shekara 35 bayan kashe shi

    Hukumomin Laberiya sun gudanar da jana'izar karramawa ga tsohon shugaban ƙasar Samuel Doe, kusan shekara 35 da kashe shi.

    Wasu mayaƙan tawaye ne suka kama shi tare da yi masa azaba, kafin daga bisani su ka kashe shi a farkon yaƙin basasan ƙasar.

    Matakin yana daga cikin ƙoƙarin shugaban ƙasa mai ci, Joseph Boakai, na ƙarfafa sulhu da haɗin kan ƙasa.

    Ba'a gano gawar Samuel Doe ba, amma za a binne akwatin gawar da babu komai a ciki a gidan danginsa, tare da akwatin gawar matarsa Nancy da ta rasu a watan da ya gabata.

    A mako mai zuwa, za a gudanar da irin wannan jana’iza ta ƙasa ga William Tolbert, shugaban da Samuel Doe ya kifar a juyin mulki na shekarar 1980.

    An kashe Tolbert kuma aka binne gawarsa a kabari guda tare da wasu.

  10. Zanga-zangar adawa da shugaban ƙasar Togo ta jefa ƙasar cikin ruɗani

    Togo na cikin shirin fuskantar ƙarin tashin hankali yau bayan da ‘yan sanda suka harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati a jiya, waɗanda suka taru domin buƙatar Shugaban ƙasar, Faure Gnassingbé ya sauka daga mulki.

    ‘Yan gwagwarmaya sun kira zanga-zangar kwanaki uku a jere domin nuna rashin amincewarsu da gwamnatin, zanga-zangar da hukumomi suka ce ba ta da izini.

    Masu adawa da gwamnati sun nuna damuwa kan yiwuwar shugaba Faure ya ci gaba da mulki har abada, bayan da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kwamitin ministoci — wani sabon matsayi da ba shi da iyaka na wa’adin mulki.

    Faure Gnassingbé dai ya shafe shekaru 20 yana mulkin ƙasar da ke yammacin Afirka, yayin da danginsa suka shafe shekaru 58 suna mulkin Togo tun bayan samun ‘yancin kai.

    Masu fafutuka na ci gaba da matsa lamba ga gwamnatin, suna buƙatar tsarin mulki mai adalci da mulkin dimokuradiyya na gaskiya a ƙasar.

  11. IGP ya ba da umarnin bincike kan bidiyon ƙorafin wani tsohon ɗansanda kan fansho

    Babban Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun, ya yi umarni a gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da wani tsohon hafsan ƴansanda ya yi cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, dangane da fanshon tsofaffin ƴansanda.

    IGP ya umarci hukumar fanshon ƴansanda ta NPF da ta duba ƙorafin gaggawa, ta gano duk wata matsala, tare da ɗaukar matakin da ya dace don magance matsalolin da aka bayyana.

    Kakakin rundunar ta ƙasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar 26 ga Yuni, 2025.

    A sanarwar, Egbetokun ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi watsi da halin da tsofaffin jami’anta suke ciki ba, musamman duba da irin gudummawar da suka bayar wajen kare rayuka da dukiyar ƴanƙasa.

    Ya ce walwala da jin daɗin jami’ai – masu aiki da waɗanda suka yi ritaya – na daga cikin manyan abubuwan da rundunar ke ɗauka da muhimmanci.

    Ya ƙara da cewa biyan fansho cikin lokaci na da matuƙar tasiri wajen ƙarfafa gwiwa da mutuncin rundunar.

    Ya kuma ce rundunar za ta ci gaba da sauraron ra’ayoyi da ƙorafe-ƙorafe domin inganta tsarin jin daɗin ma’aikata.

    Ya ƙara da cewa NPF za ta haɗa kai da hukumomin da suka dace domin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin da aka jero a cikin bidiyon.

    Egbetokun ya kuma tabbatar wa da dukkan jami’ai – da masu aiki da waɗanda suka yi ritaya – cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da ingantaccen tsarin walwala wanda zai dace da sadaukarwar da suka yi wa ƙasa.

  12. Ministan harkokin wajen Iran ya ce an lalata cibiyoyin nukiliyar ƙasar

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai sun yi "babban lahani" ga cibiyoyin nukiliyar ƙasar.

    A wata tattaunawa da gidan talabijin gwamnati da aka yi da shi da yammacin Alhamis, Araghchi ya ce hukumar kula damMakaman nukiliya ta Iran tana gudanar da cikakken bincike don tantance girman ɓarnar da aka yi.

    Sai dai, awanni kaɗan kafin hakan, shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana cewa hare-haren ba su hana ci gaba da shirin nukiliyan kasar ba.

    Ya mayar da martani ne ga iƙirarin Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya ce hare-haren sun “lalata gaba ɗaya” wurare uku na nukiliyar ƙasar.

    Khamenei ya ce hare-haren Amurka “ba su cimma wani abu mai muhimmanci ba,” tare da zargin Trump da zuzuta girman tasirin hare-haren. Ya kuma ayyana cewa Iran ta samu nasara akan Amurka da Isra’ila.

    Ministan ya ƙara da cewa babu wani shiri na komawa teburin tattaunawa da Amurka.

  13. Sojojin Najeriya sun kai farmakin ramuwar gayya kan ƴan bindiga a Neja

    Dakarun Sojin Saman Najeriya sun ce sun ƙaddamar da gagarumin farmakin sama kan sansanonin ‘yan bindiga a jihar Neja a ranakun Laraba da Alhamis, a wani yunƙuri na kawar da ƴan fashin da suka kai hari kan dakarun ƙasar a baya-bayan nan.

    Wata sanarwa da rundunar sojin saman ta wallafa a shafinta na sada zumunta ta ce an kai harin ne ƙarƙashin shirin FANSAN YAMMA "domin kawar da barazanar tsaro da 'yan ta’adda ke haifarwa.

    "A ranar 26 ga watan Yuni, bayan samun bayanan sirri, rundunar sojin saman Najeriya, bayan haɗa gwiwa da sauran jami'an tsaro ta gano ayyukan ƴan bindiga da suka hada da satar shanu a yankin Kakihun da Kumbashi," in ji sanarwar wadda ta samu sa hannu daraktan yaɗa labarai na rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame.

    "Nan take rundunar ta ƙaddamar da hare-haren da suka yi sanadin kashe ƴan fashin daji da dama, lalata kayan aikinsu da kuma hana su haɗuwa," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    A cikin makon nan ne aka samu rahotannin da suka ce ƴan fashin daji a jihar ta Neja, arewa maso tsakiyar Najeriya sun kai samame a wasu sansanonin sojin Najeriya inda suka kashe jami'an soji "aƙalla 17".

    Wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriyar ta fitar ta tabbatar da kai harin sai dai ba ta yi bayani kan yawan sojojin da suka rasa rayukansu ba sanadiyyar farmakin.

    Neja na cikin jihohin Najeriya masu fama da matsalar tsaro, inda ƴan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka da dama, lamarin da ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da kawo cikas ga ayyukan tattalin arziƙi.

  14. Jihar Nasarawa ba maɓoyar mahara ba ce - Gwamna Sule

    Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya musanta zargin da ake yi cewa mahara na tserewa zuwa jiharsa ne bayan sun kai hari a jihar Benue.

    Da jihar Nasarawa da jihar Benue maƙwabtan juna ne, wanda hakan ya sa wasu ke zargin maharan da suke addabar yankunan jihar Benue suna guduwa zuwa Nasarawa ne suna ɓoyewa har tashin hankalin ya lafa, sannan su koma su sake wani harin.

    Daga cikin kashe-kashen jihar da aka yi irin wannan zargin, akwai kisan da aka yi a garin Yelwata na Benue na kwanakin baya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

    Sai dai a tattaunawarsa da tashar Channels a shirin Politics Today a daren Alhamis, Gwamna Sule ya musanta zargin, inda ya ce babu wannan maganar.

    "Jihar Nasarawa na da nata matsalolin, me zai sa mu zama maɓoyar wasu mahara?" mu kanmu ta matsalolinmu na cikin gida muke, ba ɗauko matsalolin wasu ba. A Nasarawa ma ba mu da makiyaya da yawa."

    Sai dai ya ce tun lokacin da ya ƙarbi ragamar mulki a shekarar 2019 ya samu zargin, "har ta kai wanda na gada da gwamnan Benue na wancan lokacin, Ortom sun samu saɓani ba sa ma magana da wanda na gada. Da na shiga ofis, sai na kira Ortom muka zauna, ya kawo min ƙorafin, na ce masa za mu yi aiki tare domin magance ta."

  15. DR Congo da Rwanda za su sanya hannun kan yarjejeniyar zaman Lafiya

    Ana sa ran ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC) da Rwanda za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya ta tarihi a yau yayin wata ganawa da za su yi da Shugaban Amurka Donald Trump a fadar White House.

    An cimma wannan yarjejeniya ne bayan watanni na tattaunawa da Amurka ta shiga tsakani a matsayin mai sulhu.

    Ko da yake cikakken bayani game da yarjejeniyar bai bayyana ba a halin yanzu, Trump ya bayyana ta a matsayin dama mai girma don kawo ƙarshen rikici a gabashin DRC.

    Har yanzu ba a san tasirin yarjejeniyar ga halin da ake ciki da 'yan tawayen M23 da dakarun Rwanda da ke cikin DRC ba.

    Gwamnatin Kinshasa dai na zargin Kigali da tallafa wa mayakan M23, waɗanda suka ƙwace manyan birane da dama a bana.

    Ana kyautata zaton cewa yarjejeniyar za ta kunshi raba damar cin gajiyar albarkatun ma’adinai masu daraja da ke yankin gabashin DRC.

  16. Shugabannin Faransa da Jamus na son a cimma yarjejeniyar kasuwanci da Amruka

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz sun ce ya zama dole Tarayyar Turai ta cimma yarjejeniyar kasuwanci cikin gaggawa da Amurka.

    Sun faɗi hakan ne bayan taron Tarayyar Turai a birnin Brussels, yayin da ya rage ƙasa da mako biyu kafin cikar wa'adin Amurka na ƙulla yarjejeniya da kuma kaucewa ƙarin haraji mai nauyi.

    Shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta ce Brussels a shirye take da kowane irin yanayi amma za a kare muradun Turai.

    Shugabannin Tarayyar Turai sun kuma amince su tsawaita takunkuman da aka ƙaƙabawa Rasha na tsawon wata shida.

  17. Takunkumin Amurka kan Sudan saboda amfani da makamai masu guba zai fara aiki

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana cewa daga yau ne takunkumin tattalin arziƙin da Amurka ta sanya wa Sudan kan amfani da makamai masu guba a yaƙin basassar ƙasar zai fara aiki.

    Takunkumin, wanda aka sanar tun ranar 22 ga Mayu, ya haɗa da dakatar da fitar da kaya daga Amurka zuwa Sudan da kuma hana ƙasar samun tallafin kuɗi daga hukumomin gwamnatin Amurka.

    Sai dai, takunkumin ba za shafi agajin gaggawa da abinci da kayan noma ba.

    Rundunar RSF mai fada da dakarun gwamnati ta zargi sojojin Sudan da amfani da makamai masu guba a wurare 11, tare da adana su a cikin wuraren ajiya a birnin Omdurman.

    Amma kuma gwamnatin Sudan ta ce za ta gudanar da bincike kan wannan zargi.

  18. Rundunar sojin Najeriya ta ayyana makokin kwana uku kan kashe jami'anta

    Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana fara zaman makoki na kwanaki uku domin girmama sojoji 17 da suka rasa rayukansu a yayin wani harin da aka kai musu a Kwana Dutse, ƙaramar hukumar da ke jihar Neja.

    Wannan zaman makoki zai gudana ne daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Yuni, 2025, a matsayin alamar juyayi da girmamawa ga sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare martabar ƙasa.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, an umurci dukkan cibiyoyi da ma'aikatan soji a faɗin ƙasar da su yi ƙasa-ƙsa da tutocin sojin Najeriya zuwa a wannan lokacin.

    Rundunar ta ce wannan mataki na nuni ne da yadda ta ke ɗaukar rayuwar jami’anta da muhimmanci tare da nuna alhini ga iyalai da ƴan uwa na waɗanda suka mutu.

    Rundunar Sojin Najeriya dai ta tabbatar da mutuwar sojojin ne sakamakon hare-haren da wasu ƴan bindiga suka kai kan sansanonin soji da ke jahohin Neja da Kaduna.

  19. Japan ta yanke hukuncin kisa kan mutumin da aka fi sani da 'makashin twitter'

    Japan ta zartar da hukuncin kisa a karon farko cikin shekara uku kan wani fursuna.

    An kama Takahiro Shiraishi a 2017 bayan gano sassan jikin bil adama a gidansa.

    A shekarar 2020 ne aka yanke masa hukuncin kisa saboda kisan mutum tara - galibinsu mata matasa.

    An yi wa mutumin mai shekara 34 laƙabi da 'Makashin Twitter' bayan da ya amince cewa yana farautar mutane ne a dandalin sada zumuntarsa na X inda yake yaudararsu ya kai su gidansa sannan ya kashe su ya kuma yi gunduwa-gunduwa da su.

    Mnistan shari'ar Japan ya ce batun ya girgiza al'umma ganin yadda aka rasa mutum tara cikin wata biyu saboda son kai irin nashi don biyan buƙatunsa.

  20. Iran na binciken ɓarnar da aka yi cibiyoyin nukiliyar ƙasar

    Ministan harkokin waje na Iran ya amince an yi wa tashoshin nukiliyar ƙasarsa abin da ya kira gagarumar ɓarna a hare-haren baya-bayan nan da Amurka da Isra'ila suka kai.

    Abbas Araghchi ya ce hukumar kula da makaman nukiliya a ƙasar na gudanar da bincike.

    Kalamansa na zuwa ne yayin da Washington ke ci gaba da jaddada cewa hare-haren da ta kai sun kassara burin Iran kan nukiliya.

    Manyan jami'an gwamnatin Amurka sun yi jawabi ga ƴan majalisar dattawan ƙasar. Ƴan Republicans sun ce a bayyane take ƙarara cewa an yi nasara a hare-haren sai dai wani ɗan Democrat guda, Chris Murphy ya ce abu ne mai wuya a iya rusa ilimi.