Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Ofishin hukumar ƴan gudun hijirar Falasɗinawa a gaɓar yamma ya kama da wuta

    Hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa ta ce ginin shalkwatarta da ke Gabar yamma da kogin Jordan da aka fara rushewa yanzu yakama da wuta.

    A makon daya gabata ne mahukuntan Isra'ila suka lalata wanu ɓangare na ginin hukumar.

    Cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X, shugaban hukumar Philippe Lazzarini,ya ce wutar da aka sanyawa ginin na su a yanzu shi ne hari na baya bayan nan da aka kai musu a wani yunƙuri na tarwatsa hukumar.

    Ba dai a bayar da cikakken bayani akan yadda wutar ta tashi a ofoshin hukumar ba.

  2. Lokuta bakwai da aka ɓaɓe tsakanin 'ubangida da yaronsa' a siyasar Najeriya

    Nan gaba a yau ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sanar da komawa jam'iyyar APC a hukumance bayan raba gari da ubangidansa a siyawa, Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP.

    A ranar Juma'a ne Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP da aka zaɓe shi a karkashinta a shekarar 2023.

    Gwamnan ya bayyana rikicin cikin gida da fifita ci gaban al'ummar jihar Kano a matsayin dalilansa na ficewa daga NNPP.

    Tuni dai jam'iyyar ta yi masa martani, cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta masu kaɗa ƙuri'ar da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen gwamna na 2023.

    Ba wannan ne karon farko da aka samu sabani, wanda ya kai ga ɓaɓewa tsakanin ubangida da yaronsa a siyasar Najeriya ba.

    Saɓani tsakanin ubangida da yaro a siyasar Najeriya abu ne da ya daɗe yana faruwa, inda akasari hakan ke faruwa bayan yaron ya hau mulki kuma ya fara ƙoƙarin cin gashin kansa.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.