Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Sojoji sun tabbatar da yunƙurin yi wa Tinubu juyin mulki

    Tinubu

    Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

    Hukumomin tsaron Najeriya sun ce sun samu wasu jami'an soji da laifin kisat juyin mulki a ƙasar a shekarar da ta gabata.

    Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce ta samu wasu ƙananan hafsoshi 16 da laifin yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Tinubu cikin watan Oktoban 2025.

    Cikin watan Oktoban ne rundunar sojin ƙasar ta kama sojojin tare da ƙaddamar da bincike a kan su bayan zarginsu da rashin ladabi da saɓa wa dokokin aikin soji.

    Shalkwatar tsaron ƙasar ta ce a yanzu an kammala binciken, inda da dama cikin sojojin da aka tsaren suka tabbatar da yunƙurin juyin mulkin, wani abu da rundunar sojin ƙasar ta ce ya saɓa wa ƙa'idojin aikin soji da kundin tsarin mulkin Najeriya.

    Rundunar sojin ƙasar ta ce nan gaba za a gurfanar da jami'an gaban kotun soji don yi musu hukunci.

    A shekarun baya-bayan an riƙa samun zarge-zargen yunkurin juyin mulki a Najeriya, sakamakon tashe-tashen hankulu da rigingimu da matsin rayuwa, zargin da sojojin suka sha musantawa.

    Najeriya ta fuskanci juyin mulki masu yawa - tun bayan samun ƴancin kan ƙasar - a tsakanin shekarun 1966 zuwa 1993.

    Sai dai tun bayan da ƙasar ta koma mukin dimokraɗiyya a 1999, sojojin ƙasar suka ɗauki batun yunƙurin juyin mulki ta matuƙar muhimmanci.

  2. Trump ya ce zai iya janye jami'an shige da fice daga Minniapolis

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya nuna alamun cewa nan gaba zai iya janye jami'an hukumar shige da fice daga Minneapolis, a yayin da ake kara nuna fushi a game da kisan da aka yi wa wani ma'aikacin jinya Alex Pretti.

    Cikin wata hira da ya yi da gidan jaridar Wall Street Journal, Mr Trump ya kuma ce gwamnatinsa na nazarin abubuwan da suka biyo bayan harbin da aka yi wa mutumin.

    Da yake magana da BBC, shugaban rundunar 'yan sandan Minneapolis, ya yi zargin cewa tun da farko an hana 'yan sandan da aka dorawa alhakin binciken harbin da aka yi samun damar kai wa ga inda aka yi shi.

    Ana dai samun karuwar kiraye-kiraye daga wajen 'yan siyasa a jam'iyyar Republican akan a gudanar da cikakken bincike akan harbin mutumin.

  3. Aƙalla mutum 15 sun rasu a haɗarin jirgin ruwa a Philippines

    PHILIPPINE COAST GUARD SOUTHWESTERN MINDANAO / HANDOUT

    Asalin hoton, PHILIPPINE COAST GUARD SOUTHWESTERN MINDANAO / HANDOUT

    Akalla mutum 15 sun rasa ransu bayan wani jirgin ruwan fasinja ya nitse a Philippines. An ceto mutane fiye da 300 to ana ci gaba da aikin neman wadanda har yanzu ba a gani ba.

    Wakilin BBC ya ce bidiyon da aka sanya a kafafan sada zumunta sun nuna mutanen da suka tsira na ta ihun neman a kawo musu dauki a cikin dare inda kuma aka kwashesu zuwa bakin tekun.

    Hadarin jirgin ruwan ya afku ne a safiyar yau Litinin a gabar ruwan kudancin Phillipine da ke lardin Basilan.

    Nan gaba ne kuma za a fara bincike akan abin da ya haddasa hadarin to amma masu tsaron tekun sun tabbatar da cewa mutane ne suka yi wa jirgin yawa.

  4. Kwamishinan tsaron cikin gida na Kano ya ajiye aiki

    Hon Abduljabbar Umar

    Asalin hoton, Hon Abduljabbar Umar

    Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida, Air Vice Marshan Ibrahim Umaru mai ritaya ya ajiye aikinsa na muƙamin kwamishina a gwamnatin jihar Kano.

    Kwamishinan ya ajiye aikin ne a daidai lokacin da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf yake gudanar da bikin komawa jam'iyyar APC mai mulki a matakin tarayya.

    Tsohon sojan na sama ya bar gwamnatin ne domin cigaba da nuna goyon bayansa ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwanso.

    A wata takarda da ya fitar, ya ce "ganin yadda abubuwa suke faruwa, ina ganin zai fi kyau in ajiye muƙamina in koma gefe."

    Ibrahim Umaru ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagoransa kuma abin koyi, "kuma koyi da shi ne wajen aiki da adalci da fifita buƙatun al'umma."

  5. Gawuna da Garo ba za su yi takara da Abba ba - Ganduje

    Facebook/Nasiru Yusuf Gawuna

    Asalin hoton, Facebook/Nasiru Yusuf Gawuna

    Toshon shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce tsoffin waɗanda suka yi wa APC takarar gwamna da mataimaki a jihar cikin APC ba za su yi takara da Abba Kabir Yusuf ba.

    Yayin da yake jawabi a wurin taron komawar Abba APC, Ganduje - wanda shi ne ubangidan Gawuna da Garo - ya ce sun tabbatar masa cewa ba za su yi takara da Abba a 2027 ba.

    A shekarar 2023 takara ta yi zafi tsakanin Gawuna da Abba, inda har aka sake zaɓe a wasu akwatunan jihar.

    Abba Kabir Yusuf ya koma APC ne bayan raba gari da jam'iyyar NNPP da Sanata Rabi'u Kwankwanso ke jagoranta.

  6. Isra'ila ta ce an gano gawar ƙarshe cikin mutanenta da ke hannun Hamas

    Isra'ila

    Asalin hoton, Bring Them Home Now/Handout via REUTERS

    Isra'ila ta ce ta gano gawar da ta rage daga cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza, lamarin da zai bayar da damar shiga mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta da Shugaba Trump ke jagoranta.

    Gano dukkanin waɗanda da ake riƙe da su, a mace ko da rai, na daga cikin manyan sharuɗɗan da aka gindaya domin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

    An kai gawar Ran Gvili, wanda ɗan sandan ne da aka kashe lokacin harin ranar bakwai ga watan Oktoba, zuwa Isra'ila.

    Ƙungiyar Hamas ta ce ta taimaka wajen gano inda gawar take domin ta nuna jajircewarta domin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wutar.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana gano gawar a matsayin cika alƙawarin da ya ɗauka na dawo da dukkanin waɗanda aka yi garkuwa da su.

  7. Za mu yi wa sojoji 16 shari'a kan yunƙurin juyin mulki a Najeriya - Rundunar tsaro

    Tinubu

    Asalin hoton, @officialABAT

    Rundunar tsaron Najeriya ta ce ta kammala binciken da take yi kan yunƙurin kifar da gwamnati a Najeriya wanda aka yi a shekarar da ta gabata, inda ta ce nan gaba kaɗan za ta gabatar da sojoji a gaban kotun sojoji domin fuskantar shari'a.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Litinin, wanda wannan ne karo na farko da ta fito ta tabbatar da an yi yunƙurin juyin mulkin.

    A cikin sanarwar, wadda mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar, ya ce tuni rundunar tsaron ta miƙa rahoton bincike zuwa ga shugaban ƙasa.

    "Rundunar tsaron Najeriya na sanar da al'umma cewa an kammala binciken yunƙurin juyin mulkin da aka yi. Mun samu hafsoshi guda 16 da aikata laifuka da suka saɓa da tsare-tsaren aikin soji, kuma mun miƙa rahotonmu zuwa ga mataki na gaba kamar yadda doka ta tanada," in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa binciken ya gano tare da tabbatar da cewa wasu sojoji sun yi yunƙurin kifar da gwamnati, "sannan da sannu waɗanda aka gano sun aikata laifi za su bayyana a gaban kotun soji ta musamman domin fuskantar shari'a kamar yadda kundin tsarin soji ya tanada."

  8. Abba ne jagoran APC a Kano - Ganduje

    Ganduje

    Asalin hoton, Aminu Dahiru Ahmad

    Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ya koma APC a yau yanzu shi ne jagoran jam'iyyar a Kano.

    Yayin da yake jawabi a wajen taron bikin komawar gwamnan APC da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar, Ganduje ya ce jam'iyyar APC na maraba da shigar Abba tare da mutanensa zuwa APC.

    Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce kamar yadda tsarin jam'iyyar yake cewa gwamna shi ne jagoran jam'iyyar a kowace jiha ba.

    ''Don haka a nan ma yanzu kai ne jagoran jam'iyyar APC a jiharmu ta Kano'', in Ganduje.

  9. Mustapha Rabiu Kwankwaso ya ajiye muƙaminsa na kwamishina

    Mustapha Rabiu Kwankwaso

    Asalin hoton, Mustapha Rabiu Kwankwaso

    Ɗan Rabiu Musa Kwankwaso, kwamishinan matasa da wasanni ne jihar a Kano ƙarƙashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya ajiye muƙaminsa.

    Matakin na zuwa ne daidai lokacin da gwamnan ke komawa jam'iyyar APC a wani sabon babin siyasar Kano.

    A wani saƙo da ya fitar, ya ce yana godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi domin bayar da gudunmuwarsa wajen hidimta wa al'ummar Kano.

    "Ina matuƙar alfahari da damar, sannan na koya darussa da dama a lokacin da na ɗauka a matsayin kwamishina a gwamnatin jihar Kano."

    Ya ƙara da cewa, "a yanzu da na ajiye aiki, ina addu'a tare da fatan ganin matasan Kano sun cigaba da samun goyon bayan da suke buƙata. Allah ya dawwamar da zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a jiharmu ta Kano," in ji shi.

  10. Abba Kabir na dab da komawa APC

    ...

    An kammala shirye-shiryen komawar gwamnan jihar Kano Abba Kabir zuwa jam'iyyar APC mai mulki bayan ficewarsa daga jam'iyyar NNPP.

    An kafa manyan alluna ɗauke da hoton Gwamna Yusuf haɗe da shugaban Najeriya Bola Tinubu da kuma jiga-jigan jam'iyyar APC, kamar tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa Abdullahi Ganduje.

    ...

    An sauya tutocin jam'iyyar NNPP da na APC tare da ƙawata babban ɗakin taro na gidan gwamnan jihar da hotunan Shugaba Tinubu da kuma na gwamna Yusuf ɗauke da tambarin jam'iyyra ta APC.

    Anjima kadan ne ake sa ran Abba zai koma jam'iyyar bayan raba gari da jam'iyyar ANPP wadda aka zaɓe shi a matsayin gwamna a ƙarƙashinta.

    ...

    Jama’a da ‘yan siyasa na ci gaba da dakon sanarwa a hukumance daga gwamnandomin kawo ƙarshen tsawon lokacin da aka kwashe ana raɗe-raɗin komawarsa jam'iyyar mai mulki.

    ...

    Abba Kabir ya bayyana rikicin cikin gida na jam'iyyar ANPP a matsayin ɗaya daga cikin dalilansa na ficewa daga jam'iyyar.

    Haka nan ya ce ya sauya sheƙar ne domin amfanin jihar ta Kano da mutanenta.

  11. A daina yaɗa jita-jitar sauya Kashim Shettima - APC

    ...

    Asalin hoton, KASHIN SHETTIMA/FACEBOOK

    Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai yiwuwar za ta sauya Mataimakin Shugaban Ƙasar, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekara ta 2027.

    Jam’iyyar ta ce rahotannin ba su da tushe, "kuma tsantsar jita-jita ce da ke da nufin haddasa ruɗani da rikici a harkokin siyasar ƙasar".

    APC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Felix Morka, ya fitar.

    A Najeriya an daɗe ana raɗe-raɗin cewa jam'iyyar za ta iya sauya mataimakin shugaban ƙasar gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.

    Tun farko haɗin Bola Tinubu da Kashim Shettima ya sha suka daga wasu ɓangarorin ƙasar kasancewar ana ganin hakan ya saɓa da al'adar da aka saba da ita ta saɓawar addinin shugaban ƙasa da mataimakinsa.

    Sai dai a lokuta da dama masu alaƙa da jam'iyyar mai mulki sun ce an yi hadin ne a matsayin wata dabara ta siysa da neman cin zaɓe a shekara ta 2023.

    Ana sa ran harkokin siyasa za su rincaɓe a cikin wannan shekara ta 2026 a Najeriya, gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara mai zuwa, inda ake sa ran Tinubu zai sake yin takara domin neman wa'adin shugabanci na biyu na tsawon shekara huɗu.

  12. 'Gwamnatin tarayya ce ta janyo yajin aikin ma'aikatan asibiti'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Haɗakar ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya ta Najeriya, (JOHESU) ta ce ‘yan Najeriya su ɗora wa gwamnatin tarayya alhakin wahalhalun da marasa lafiya da sauran masu buƙatar kulawar lafiya ke fuskanta sakamakon yajin aikin da mambobinta ke yi.

    Ƙungiyar ta ce buƙatarta ɗaya tilo ita ce aiwatar da rahoton da ya shafi daidaita tsarin albashin ma’aikatan kiwon lafiya na CONHESS.

    Sakataren JOHESU na ƙasar, Martin Egbanubi ne ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

    Ya ce duk da sanin tasirin yajin aikin a kan ƴanƙasa, bai kamata a ɗora musu laifi ba.

    Ya ce, “Mun san irin tasirin da yajin aikin ke yi wa ‘yan Najeriya, amma bai kamata ‘yan ƙasa su ɗora mana laifi ba. Gwamnati ce ya kamata ta ɗauki alhaki, domin ita ce ke da haƙƙin yin abin da ya dace domin kauce wa irin wannan yajin aiki a nan gaba.”

    Egbanubi ya ƙara da cewa JOHESU na fahimtar halin da marasa ƙarfi ke ciki, musamman waɗanda ba su da ƙarfin zuwa asibitoci masu zaman kansu, amma ya ce mambobin ƙungiyar ma suna shan wahala.

    Saboda haka, ƙungiyar ta buƙaci masu kishin kasa su yi kira ga gwamnati ta gaggauta magance buƙatar domin dakatar da yajin aikin.

  13. 'Sun girke bindiga a saman titi suna ɓarin wuta': Abin da muka sani kan sace mutane a Mafara

    ...

    Asalin hoton, FB/Dauda Lawal

    Hukumomi a jihar Zamfara, mai fama da matsalar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da sace mutane 26 a wasu hare-hare da ƴan bindiga suka kai kan ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Talatar Mafara a ƙarshen mako.

    Talatar Mafara na daga cikin ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro a jihar, inda a shekarar 2021 ƴan bindiga suka sace ɗaliban makarantar mata ta Jangebe, kimanin 300.

    A tattaunawa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Talatar Mafara Yahaya Yari Abubakar ya ce ƴan bindigar sun kai hare-hare biyu a cikin ƙarshen mako.

    "Shekaran jiya an shiga wani ƙauye mai suna Matuna, inda suka ɗauki mutum uku suka kuma kashe mutum ɗaya," a cewar Yari Abubakar.

    Ya ƙara da cewa "sai suka sake dawowa suka sake kai hari a wani ƙauye da ake ce wa Tashar Kuturu, suka ɗauki mutum 23 kuma suka harbi wani mutum a hannu da kafa, mun kai shi asibitin cikin garin Jangebe ana nema masa lafiya."

  14. Soludo ya rufe kasuwar Onitsha na mako ɗaya saboda bin dokar hana fita

    ...

    Asalin hoton, Solude/Facebook

    Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya umarci rufe Kasuwar Onitsha na tsawon mako guda, bayan ‘yan kasuwar suni bi dokar hana fita da mayaan IPOB ke sakawa a kowace ranar Litinin.

    Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin yayin ziyarar sa a kasuwar tare da wasu daga cikin masu ba shi shawara da sauran jami’an gwamnati.

    Soludo ya gargaɗi cewa idan ‘yan kasuwar sun ci gaba da bin umarnin, ana iya tsawaita rufe kasuwar, inda ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun rufe kasuwar ne don aiwatar da dokar.

    Soludo ya ce duk da tabbacin da aka bayar sau da yawa na inganta tsaro da kiran a farfaɗo da buɗe shaguna, ‘yan kasuwa da dama a wannan kasuwar sun zaɓi ci gaba da rufe shagunan su.

    Soludo ya ce, “Gwamnati ba za ta tsaya tana kallo ba yayin da wasu ‘yan mutane ke bin dokokin IPBO, suna barazana ga lafiyar jama’a da watsi da umarnin gwamnati na dawo da zaman lafiya. Wannan cin zarafi ne na tattalin arziki.”

  15. Sudan ta Kudu ta bai wa fararen hula umarnin barin yankunan da ke hannun ƴan adawa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Sudan ta Kudu ta bai wa fararen hula da ƙungiyoyin agaji da ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya wa’adin sa’o’i 48 su bar yankunan da ke ƙarƙashin ikon ƴan adawa a jihar Jonglei da ke gabashin ƙasar, gabanin fara wani babban farmakin soji.

    Wannan umarni na zuwa ne kwanaki biyu bayan da babban hafsan sojin ƙasar ya shaida wa dakarunsa cewa suna da kwanaki bakwai su “murƙushe tawaye” a gabashin ƙasar, wanda hukumomi suka ce na iya zama barazana ga babban birnin ƙasar, Juba.

    A cikin wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Lahadi, kakakin rundunar sojin Sudan ta Kudu SSPDF, Manjo Janar Lul Ruai Koang ya ce dole ne mutanen da ke zaune a yankunan da ke hannun ƙungiyar ƴan adawa ta Sudan wato SPLA-IO, su fice cikin wa’adin da aka bayar.

    Ya ƙara da cewa dole ne kuma fararen hula su koma yankunan da ke ƙarƙashin ikon gwamnati domin tsaron lafiyarsu, yayin da sojoji ke shirin ƙaddamar da farmakin da suka sanya wa suna da "Dorewar Zaman Lafiya".

    Kakakin ya kuma yi gargaɗin cewa duk fararen hula masu ɗauke da makamai su miƙa su ga sojojin gwamnati, yana mai cewa duk wanda aka samu kusa da barikin ƴan adawa SPLA-IO za a ɗauke shi a ɗaya daga cikinsu a haɗa da shi a farmakin.

    Ƙungiyar ƴan adawa SPLA-IO ba ta ce komai ba dangane da wannan umarnin.

  16. Zan iya janye jami'an hukumar shige da fice daga Minneapolis - Trump

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya nuna alamun cewa nan gaba zai iya janye jami'an hukumar shige da fice ICE daga Minneapolis, a yayin da ake ƙara nuna fushi a game da kisan da aka yi wa wani ma'aikacin jinya Alex Pretti.

    Cikin wata hira da ya yi da gidan jaridar Wall Street Journal, Trump ya kuma ce gwamnatinsa na nazarin abubuwan da suka biyo bayan harbin da aka yi wa mutumin.

    Da ya ke magana da BBC, shugaban rundunar 'yan sandan Minneapolis, ya yi zargin cewa tun da farko an hana 'yan sandan da aka ɗorawa alhakin binciken harbin da aka yi samun damar kai wa ga inda aka yi shi.

    Ana dai samun ƙaruwar kiraye-kiraye daga wajen 'yan siyasa a jam'iyyar Republican akan a gudanar da cikakken bincike akan harbin mutumin.

  17. An kama motar da ake zargin ta ɗauki abubuwan fashewa a Oyo

    ...

    Asalin hoton, NPF

    Rundunar ‘Yan Sandan jihar Oyo ta sanar da cewa ta samu nasara kama wata motar dakon kaya da ake zargin tana ɗauke da abubuwan fashewa.

    Jami’an rundunar sun dakatar da motar a yayin bincike a Saki, jihar Oyo bisa sahihan bayanan sirri da suka samu inda suka gano kayan da ake zargin abubuwan fashewa ne

    “Motar da kayan da ake zargin sun kasance suna hannun ‘yansanda.” in ji DSP Olayinka Alayande, mai magana da yawun ‘yan sanda.

    Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce kwamishinan ‘yan sanda, Femi Haruna, ya umarci gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tura ƙwararrun jami’an kunce abubuwan fashewa domin tabbatar da tsaron kayan da kuma gano ainihin nau’in kayan da kuma dalilin da aka nufa da su.

    Haka kuma, an kama direban motar wanda ke bayar da cikakken hadin kai ga jami’an a binciken da suke yi.

    Kwamishinan ‘yan sanda ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ƴansandan Najeriya za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin natsuwa kuma su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana.

  18. Dusar ƙanƙara ta mamaye Amurka ta katse wutar lantarki

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da fuskantar tsananin sanyi da zubar dusar kankanra a sassan Amurka inda aka samu daukewar wutar lantarki a wurare da dama da kuma soke tashi da saukar jirage dubu 11.

    Kusan gidaje da wuraren kasuwanci miliyan guda basu da wutar lantarki.

    Yanayin tsananin sanyi ya faro ne daga New Mexico zuwa Maine inda aƙalla a yanzu jihohin kasar 23 sun ayyana dokar ta baci.

    Jihohin da ke kudu maso gabashin ƙasar na shirin fuskantar mummunan yanayi na sanyi inda aka yi hasashen zubar dusar kankara mai yawan gaske a wasu yankuna na jihohin.

    Masu hasashen yanayi sun ce za a shafe kwanaki ana fuskantar tsananin sanyin sannan kuma zai haddasa asara da dama.

  19. Ganduje ya koma Abuja daga Landan 'don bikin karɓar' Abba zuwa APC

    ...

    Asalin hoton, Abdullahi Ganduja/X

    Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, ya koma Najeriya daga Birtaniya a yau Litinin, yayin da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ke shirin karɓar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bayan ficewarsa daga NNPP a makon da ya gabata.

    A yau ne ake sa ran gwamna Abba Kabir zai sanar da komawa jam'iyyar APC a hukumance bayan raba gari da ubangidansa a siyasa, Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ke a tsakanin ɓangarorin siyasa a Kano, jiha mafi yawan al'umma a arewacin Najeriya.

    Wata sanarwa da Kwamared Muhammad Garba, shugaban ma’aikatan Abdullahi Ganduje, ya fitar, ta ce ana sa ran tsohon gwamnan "zai taka muhimmiyar rawa a bikin karɓar Gwamna Abba Kabir, wanda ake sa ran zai sauya sheƙa zuwa APC" a yau Litinin.

    Ganduje ya tafi Birtaniya ne domin halaratar bikin kammala karatun digiri na biyu na ‘yarsa Fatima Ganduje a jami’ar King’s College, London. wadda ta kammala karatunta a ranar Alhamis da ta gabata.

    A jiya Lahadi ne Sanusi Bature, mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya sanar da cewa gwamnan zai sake komawa jam'iyyar APC a yau Litinin.

    A ranar Juma'a ne Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP da aka zaɓe shi a karkashinta a shekarar 2023.

    Gwamnan ya bayyana rikicin cikin gida da fifita ci gaban al'ummar jihar Kano a matsayin dalilansa na ficewa daga NNPP.

  20. Tinubu zai tafi Turkiyya a yau Litinin

    ...

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai yi tafiya a yau Litinin, 26 ga Janairu, zuwa ƙasar Turkiyya domin ziyarar aiki ta ƙasa, a wani yunkuri na ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

    A cewar wata sanarwa da mai bai wa Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a jiya Lahadi, ziyarar na da nufin faɗaɗa haɗin gwiwa a muhimman fannoni da suka haɗa da tsaro da ilimi da ci gaban al’umma da kirkire-kirkire da kuma harkar sufurin jiragen sama.

    Sanarwar ta ce wannan ziyara na zuwa ne bayan ziyarar aiki da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya kai Najeriya a ranakun 19 zuwa 20 ga Oktoba, 2021, wadda ta ƙara ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

    A yayin ziyarar, ana sa ran ƙasashen biyu za su gudanar da tattaunawar siyasa da diflomasiyya kan muhimman batutuwa da suka haɗa da harkokin kuɗi, sadarwa, kasuwanci da zuba jari.

    Daga cikin tawagar Shugaban Ƙasar da ke halartar tattaunawar diflomasiyyar akwai ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar da ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, SAN da ministan tsaro, Janar Christopher Musa, da Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Jimi Benson.