Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/08/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. 'Aƙalla ƴanjarida 186 aka kashe a Gaza'

    Ƙungiyar kare ƴanjarida ta Committee to Protect Journalists (CPJ) ta ce aƙalla ƴanjarida 186 ne aka tabbatar da kashewa tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙinta a Gaza a watan Oktoban 2023.

    Ƙungiyar CPJ ta ce tsakankanin yaƙin ne lokaci mafi muni ga ƴanjarida tun daga shekarar 1992 da ta fara bibiyar halin da ƴanjarida suke shiga.

    "Ƴanjarida na fuskantar babbar barazana, wasu lokutan barazanar rayuwarsu a wajen ɗauko rahoton yaƙin, ciki har da luguden wuta ta sama da Isra'ila ke yi," kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata.

    A watan jiya, BBC da wasu kafofin sadarwa - Reuters da AP da AFP - sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa, inda a ciki suka bayyana takaikinsu kan halin da ƴanjarida ke shiga a zirin, waɗanda suka ce suna kwanaki ba tare da samun abinci ba.

    Wakilan BBC na wucin-gadi guda uku daga zirin sun ce sukan yi kwanaki ba su ci komai, har ma akwai wani wanda ya yanke jiki ya faɗa a daidai lokacin da yake ɗauko rahoto.

    Sama da ƙungiyoyin agaji na duniya guda 100 ne suka yi gargaɗin cewa Gaza za ta faɗa matsananciyar yunwa, lamarin da Isra'ila ta zargi ƙungiyoyin da yarda da farfagandar ƙungiyar Hamas.

  2. Abin da muka sani kan yunƙurin juyin mulki a Mali

    Rahotanni daga Mali na cewa gwamntin ƙasar ta kama gomman sojoji da take zargi da yunƙurin juyin mulki domin kifar da gwamnatin sojin ƙasar.

    An ce daga cikin sojojin da aka kama har da manyan janarorin sojin ƙasar.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunanin takun-saƙa na faɗaɗa a tsakanin sojojin ƙasar wadda ke fama da matsalolin tsaro.

    "An kama aƙalla mutum 20 da ake zargi suna da hannu a juyin mulkin," kamar yadda wata majiya ta shaida wa AFP.

    Majiyar ta ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka kama, "akwai Janar Abass Dembele." Sannan ɗanmajalisar ƙasar ya ce dukka waɗanda aka kama sojoji ne.

    Gwamnatin sojin ƙasar, a ƙarƙashin Janar Asimi Goita ta ƙwace mulki ne bayan hamɓarar da gwamnatin ƙasar a shekarar 2020 da 2021.

    Kamar yadda AFP ta ruwaito ta hanyar samun bayanai daga wasu majiyoyi daga cikin sojojin ƙasar da ɓangaren gwamnati, sojojin na yunƙurin kifar da gwamnatin ne kafin aka samu nasarar daƙile su.

    Kamar Nijar da Burkina Faso, ita ma Mali dai wadda ke da alaƙa da Rasha tana cigaba da fuskantar matsalolin tsaro daga mahara a wasu sassan ƙasar.

  3. Gwamnati na ƙoƙarin jefa rikici a cikinmu - ADC

    Jam'iyyar ADC ta musanta zargin da ta ce ana yaɗawa cewa tana aiki ne domin mayar da mulkin ƙasar zuwa arewacin Najeriya.

    Kakakin jam'iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana haka a zantawarsa da tashar Channels, inda ya bayyana maganar da shashi-faɗi mara tushe.

    "ADC jam'iyya ce ta kowa da kowa. Mun faɗa tun da farko cewa ba jam'iyya ba ce ta arewa ko ta kudu. Ba jam'iyya ba ce ta musulmi ko kirista, ba jam'iyya ba ce ta yara ko tsofaffi, jam'iyya ce da aka tsara domin gina Najeriya da tabbatar da muradun ƴaƴanta."

    Wannan na zuwa ne bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar jam'iyyar a zaɓen baya, Dumebi Kachikwu ya zargi jam'iyyar da yunƙurin tabbatar da ɗan arewa a matsayin shugaban ƙasa.

    Abdullahi ya kuma zargi jam'iyya mai mulki da yunƙurin jefa saɓani a jam'iyyar ADC, inda ya ce suna sane, kuma ba su bari ta samu nasara.

  4. Australia ta amince da kafa ƙasar Falasɗinu a taron MDD

    Australia ta shiga cikin jeren ƙasashen duniya da ke shirin amincewa da kafuwar ƙasar Falasɗinu a babban taron MDD na watan Satumba.

    Firaminista, Anthony Albanese ya ce sun yanke wannan shawarar la'akari da yanayi na bala'in bukatar jin-kai a Gaza da kuma mamayar da Isra'ila ke yi wanda ya saɓa ƙa'ida a gabar yamma da Kogin Jordan.

    Ya ce zamu yi aiki da ƙasashen duniya wajen tabbatar da wannan 'yanci, ganin yanayin da ake ciki a Gaza ya zarta fargabar da ƙasashen duniya suka nuna, sannan Isra'ila ta bijirewa dokokin duniya kan bada agaji.

    Mista Albanese ya ce Hamas ba ta da makoma a ƙasar Falasdinu kuma bai dace fararan-hula su kasance masu biyan laifukan da wata ƙungiya ta aikata ba.

  5. Trump na so a kori waɗanda ba su da muhalli daga Washington

    Donald Trump ya ce yana son a kori mutanen da basu da gida daga Washington da masu laifi a gidan yari.

    A wani saƙo da ya wallafa ɗauke da hoton tantuna da kayan bola, Mista Trump ya rubuta cewa za a kwashe marasa muhalli su kasance sun yi nisa sosai da birnin ƙasar, wanda ya ce hakan zai tsaftace birnin da ƙara tsaro.

    Kafar watsa labaran Amurka na cewa ana shirin tura dubban jami'an tsaron zuwa birnin, duk da cewa Magajin Birnin, Murial Bowser, ta ɗage kan cewa ba a wani fuskantar barazana ta.

  6. Buɗewa

    Barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa kai-tsaye.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumuta irin su Facebook da X da Instagram da ma zaurenmu na Whatsapp domin karanta wasu labaran da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.