Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 27/02/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello Diginza, Isiyaku Muhammed, da Umar Mikail

  1. An sake zama domin sabunta yarjejeniyar zaman lafiya a Birnin Gwari

    Rahotanni na cewa al'ummar Birnin Gwari na jihar Kaduna da Dugun Mu'azu na ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina da wasu yankunan jihar Neja sun sake zama jiya Laraba da ƴan bindigar yankunan domin jaddada yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar Kaduna ta cimma.

    Waɗanda suka halarci taron sun bayyana cewa ƴanbindigar sun bayyana dalilan da ya sa suka riƙa kai hare-hare duk da yarjejeniyar, inda daga bisani suka nemi yafiya tare da neman a sake bude wasu kasuwannin yankin.

    Zubairu Abdulra'uf Ɗanmasanin Birnin Gwari wanda ke cikin waɗanda suka halarci zaman ya yi wa BBC Hausa ƙarin bayani, inda ya ce an sake tattaunawa, sannan an sabunta yarjejeniyar domin ci gaba da zaman lafiya a yankunan.

  2. Firaministan Birtaniya zai gana da Trump kan Ukraine

    Firaiministan Birtaniya Kia Starmer ya isa Washinton domin tattaunawa da Shugaban Amurka Donald Trump a yau Alhamis.

    Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan yaƙin Ukraine kamar yadda aka shirya.

    Kia Starmer ya shaida wa manema labarai cewa akwai buƙatar Amurka ta tabbatar ta dakatar da Rasha daga kai wa Ukraine hare-hare idan aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Wakilin BBC ya ce Starmer ya ce za su yi iya baƙin ƙokarinsu sai dai suna buƙatar goyon bayan Amurkar domin samun nasara.

    Tunda farko dai Trump ta bayyana cewa Turai ta yi iya yinta wajen kare Ukraine, inda ya ce babu tabbas kan ko Amurka za ta taimaka.

  3. BBC ta buɗe gasar Komla Dumor ta shekarar 2025

    BBC ta buɗe damar shiga domin neman kyautar lambar yabo ta Komla Dumor na hazaƙan ƴan jarida na Afirka, a karo na 10.

    Ƴan jarida daga dukkan sassan Afirka ne za su iya shiga domin shiga neman lashe lambar yabon, wanda aka assasa domin ganowa da kuma ƙarfafa gwiwar haziƙan ƴan jarida daga nahiyar.

    Wanda ya lashe kyautar zai shafe watanni uku a babban ofishin BBC da ke Landan, inda zai samu ƙwarewa da gogewa.

    Za a rufe karɓar shiga gasar a ranar 20 ga Maris da misalin ƙarfe 23:59 GMT.

    An samar da lambar yabon ne domin karrama Komla Dumor, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye na BBC ɗan asalin ƙasar Ghana, wanda ya rasu yana da shekara 41, shekara 11 da suka gabata.

    Matar Dumor, Kwansema Dumor, ta ce tana alfahari da irin tasirin da mijinta ya yi a BBC, sannan ta ce suna suna godiya ga BBC da take tunawa da gudunmuwar shi ta hanyar assasa karramawar.

    BBC na ƙarfafa gwiwar ƴan jarida a faɗin Afirka da su shiga gasar, wadda ke neman bunƙasa da kuma karrama fitattun ƴan jarida da ke rayuwa tare da aiki a nahiyar.

    Baya ga samun horo, wanda ya samu nasarar lashe kyautar, zai samu damar tafiya zuwa wata ƙasa a Afirka domin yin rahoto kan wani labari, wanda za a yaɗa a BBC ga masu bibiyar ta a faɗin duniya.

    Shahararren ɗan jarida mai fafutuka, da kuzari, na da jajircewa wurin bayar da sahihan rahotonni kan labaran Afirka baki ɗaya, Dumor ya yi matuƙar tasiri a Afirka da sauran ƙasashen duniya.

    BBC ta ƙuduri aniyar ci gaba da tunawa da shi ta hanyar bai wa ƴan jarida daga Afirka damar bayar da labarai daga Afirka don isa ga masu sauraro da ke faɗin duniya.

    Rukia Bulle ce ta lashe kyautar a shekarar da ta gabata.

    A lokacin da take samun horo a BBC, ƴar jaridar ta je ƙasar Senegal inda ta yi rahoto kan Baye Fall, domin fahimtar da duniya yanayin yadda suke gudanar da ibadarsu.

    Babban daraktan sashen labarai, kuma mataimakin babban jami'in gudanarwa na BBC, Jonathan Munro ya ce, "muna farin cikin sanar da buɗe shiga wannan karramarwar ta Komla Dumor ta bana.

    "Wannan ne karo na 10 na bayar da wannan kambun domin karrama hazaƙan ƴan jarida na Afirka da suka yi rahotanni masu tasiri daga nahiyar.

    "Waɗanda suka lashe kyautar a baya, sun nuna basira da ƙwarewa matuƙa, don haka nake farin cikin sanar da buɗe na wannan shekarar domin samun sabon angon kyautar.

    Dumor ya kasance mai gabatar da shirin Focus on Africa, shirin labarai na gidan talabijin na BBC na farko da ake yaɗa shi a kullum cikin harshen Ingilishi ga masu sauraro a Afirka. An watsa shi a tashar Labaran Duniya na BBC, wanda a shekarar da ta gabata ya haɗe da tashar yaɗa labarai ta BBC don samar da labaran talabijin na tsawon sa'o'i 24.

    Ya kuma kasance ɗaya daga cikin jagororin masu gabatar da shirye-shirye na shirin safe na Turai a BBC.

    Ya fara aiki a BBC ne a shekara ta 2007 bayan ya shafe shekara 10 yana aikin jarida a ƙasarsa Ghana inda ya lashe kyautar gwarzon ɗan jarida na Ghana.

    A tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009 ya gabatar da shirin 'Network Africa' a sashen ƙasa da ƙasa na BBC, kafin ya shiga shirin 'The World Today'.

    A shekarar 2009 Dumor ya zama mai gabatar da labaran kasuwanci na Afirka na farko a shirin Labaran Duniya na BBC, Mai suna 'Africa Business Report'. Ya karaɗe nahiyar Afirka, inda ya gana da manyan ƴan kasuwar nahiyar, ya kuma bayar da rahotanni kan sabbin hanyoyin kasuwanci a Afrika.

    A shekarar 2013 mujallar New African ta sanya Dumor a cikin jerin ƴan Afirka 100 wanda suka fi tasiri a nahiyar.

    Waɗanda suka lashe kyautar a baya

    • 2024: Rukia Bulle daga Kenya
    • 2023: Paa Kwesi Asare daga Ghana
    • 2022: Dingindaba Jonah Buyoya daga Zambia
    • 2020: Victoria Rubadiri daga Kenya
    • 2019: Solomon Serwanjja daga Uganda
    • 2018: Waihiga Mwaura daga Kenya
    • 2017: Amina Yuguda daga Najeriya
    • 2016: Didi Akinyelure daga Najeriya
    • 2015: Nancy Kacungira daga Uganda
  4. Yau za a ci gaba da sauraron ra'ayin jama'a kan ƙudurin haraji

    A yau Alhamis ne ake sa ran za a ci gaba da sauraron ra’ayin jama’a kan batun ƙudurin haraji da shugaban Najeriya ya aike wa majalisun dokokin ƙasar, domin dubawa su, kafin a amince su zama doka.

    Kwamitin kuɗi na majalisar wakilan ƙasar ya fara zaman ne a a jiya Laraba.

    Sada Soli, ɗan majalisar wakilai ne daga jihar Katsina, kuma ɗan kwamitin kuɗi na majalisar, ya yi wa BBC Hausa ƙarin bayani kan zaman, inda ya ce ana ta samun bayanai, sannan ya bayyana cewa akwai wuraren da wasu suka bayyana buƙatar a gyara, musamman batun haraji a kuɗin haraji.

  5. Dangote ya sake rage farashin man fetur a Najeriya

    Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetru a defo-fetonsa daga naira 890 zuwa N825 kan kowace lita.

    Cikin wata sanarwa da matatar ta fitar a ranar Laraba ta ce ragin fara aiki daga ranar Alhamis, 27 ga watan Fabrairun da muke ciki.

    Ragin – wanda ya kai naira 65 – shi ne irinsa na biyu a baya-bayanan da kamfanin ya yi.

    A cewar sanarwar, za a sayar da man fetur ɗin matatar a giajen man MRS – wanda abokin kasuwancin matatar ne - a jihar Legas kan naira 860 kowace lita.

    “A gidajen man MRS Holdings, za a sayar da shi kan ₦860 a kan kowace lita a Legas, ₦870 kowace lita a Kudu-maso-Yamma, ₦880 kowace lita a Arewa, da ₦890 kowace lita a Kudu-maso-Kudu da Kudu-maso-Gabas’’, kmar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    “Haka kuma za a samu irin wannan samfurin a farashin kamar haka a gidajen mai na AP (Ardova Petroleum) da Heyden: ₦865 kowace lita a Legas, ₦875 kowace lita a Kudu maso Yamma, ₦885 a Arewa, da ₦895 kowace lita a Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas."

    Kamfanin ya bai wa al’umma tabbacin samar da wadattacen man fetur ɗin da zai biya buƙatun ƴan ƙasar, da kuma wanda za a fitar da shi zuwa ƙasashen waje.

    Matatar ta kuma buƙaci ƴan kasuwa su goyi bayan wannan shiri nasa, tare da tabbatar da cewa ‘yan Najeriya za su kasance kan gaba wajen cin gajiyar wannan ragi.

  6. Sarkin Moroko ya buƙaci ƴan ƙasar su ƙaurace wa layya a bana saboda fari

    Sarkin Moroko, Mohammed na shida, ya buƙaci ƴan ƙasar su kaurace wa layya a bana wanda al'ummar Musulmi masu hali ke yanka dabobbi, musamman rago a matsayin nuna godiya ga Allah bisa rayawa da ni'imomin da ya yi wa bayinsa.Sarkin ya ce sanarwar tasa na da alaƙa da karancin raguna da ake fuskanta a ƙasar sakamakon fari.

    A watan Yunin bana ake sa ran gudanar da bikin sallar Layya. Layya ibada ce da al'ummar musulmi ke yi a cikin watan Zhul Hajji.

    A bikin Sallar layyar ana yanka dabobbi da suka danganci raguna da awaki ta hanyar zubar da jini a kuma raba naman a matsayn kyauta da sadaka don neman kusanci ga ubanjigi.

    Sai dai Sarki Mohammed na moroko ya umarci al'ummarsa su jingine batun layya a bana saboda fari ya haifar da karancin dabobbi a kasar.An samu raguwar raguna da kashi 40 cikin 100 a cikin shekaru 10 a ƙasar saboda fari.

    Farashin nama yayi tashin gwaran zabi, kuma a kullum ake shigo da dubban raguna kasar daga Australia

  7. Ƴan Najeriya na kokawa kan ƙara kuɗin kira da 'data'

    Ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda farat ɗaya kamfanonin sadarwar ƙasar suka yi ƙarin kuɗin data a farkon makon nan da kusan kashi 200 cikin ɗari.

    Wannan ƙarin ya taƙaita yadda galibin matasa da ɗalibai suke amfani da kafar intanet.

    A yanzu ƙunshin data na Gigabyte 1 ya kama daga naira 650 zuwa naira 700.

    A baya dai kamfanonin sun bayyana ɗaukar matakin ƙarin kuɗin kiran waya da na data a sakamakon tsadar kayan aiki.

    Wannan ne ya sa ƴan Najeriyar ke ta tambayar ko wane ne ke da alhakin ƙwato musu haƙƙinsu kan ƙarin?

  8. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa irin su Facebook da Instagram da X domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.