Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kai-tsaye.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Hatsarin jirgin sojan Sudan ya kashe sojoji da fararen hula

    Wani jirgin sojan Sudan ya yi hatsari a yankin Omdurman da yammacin Talata, inda fasinjoji da sojoji da dama suka mutu, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Suna.

    Ba tare da wani ƙarin bayani ba, mai magana da yawun rundunar sojin ya ce jirgin ya faɗo ne yayin da yake yunƙurin tashi daga filin jirgin sama na Wadi Seidna.

    "Mun samu mutanen da suka mutu da waɗanda suka ji rauni da yawa cikin sojoji da fararen hula. An bai wa waɗanda suka ji rauni magani, masu kashe gobara kuma sun daƙile wutar a wurin da ke Al-Iskan," in ji wata sanarwa.

    Jaridar Sudan Tribune da ke birnin Paris ta ruwaito cewa fararen hula aƙalla biyar ne suka mutu sannan da yawa suka ji rauni lokacin da ɓaraguzai suka rikito a kusa da gidajen jama'a.

    Ta ambato wasu majiyoyin soji da suka ce lamarin ya faru ne sakamakon matsalar na'ura, kuma akwai manyan jami'ai a cikin fasinjojin.

  2. Sanata Natasha ta kai ƙarar Akpabio kotu kan 'ɓata mata suna'

    Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya ta shigar da shugaban majalisar ƙara a gaban kotu kan ɓata mata suna.

    A ƙarar da ta shigar gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja ranar Talata, 'yarmajalisar ta zargi Sanata Godswill Akpabio da mataimakinsa na musamman, Mfon Patrick, da yin kalaman ɓata suna a kanta.

    Ta nemi kotun ta tilasta wa mutanen janye kalaman, su nemi afuwarta a wani shafin jarida, sannan su biya ta diyyar naira biliyan 100.

    Ta ɗora zargin nata ne kan wani saƙo da ta ce Mista Patrick ya wallafa a shafinsa na dandalin Facebook, inda ya soke ta cewa "ba ta san komai ba game da zaman majalisa...da kuma saka tufafi masu shara-shara".

    A makon da ya gabata ne sanatar da shugaban suka yi cacar baki a zauren majalaisar bayan Akpabio ya sauya mata wurin zama, abin da ya jawo cecekuce tsakanin 'yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.

  3. Amurka ta cimma yarjejeniyar haƙar ma'adanai da Ukraine

    Ukraine ta ce ta cim ma yarjejeniya tsakaninta da Amurka kan aikin haɗin gwiwa na haƙar albarkatun ƙasa.

    Babu cikakken bayani kan yarjejeniyar, sai dai jami'an gwamnatin Ukraine sun bayyana hakan a matsayin wani mataki mai kyau.

    Rahotonni na cewa Amurka ta jingine wasu daga cikin buƙatunta masu tsauri da ta gabatar da farko.

    Sannan babu tabbacin ko za a samar wa Ukraine din tsaro kamar yadda take buƙata.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ta ƙoƙarin ganin an cim ma yarjejeniyar kwasar ma'adanan ƙasa na Ukraine a matsayin ladan taimakon da Amurkar ta bai wa Ukraine game da yaƙin da take yi da Rasha.

    "Abin da muke yi a yanzu shi ne kare kanmu saboda muna son dawo da waɗannan kuɗaɗe da muka kashe wajen taimaka wa ƙasar kan wannan matsala mai girma," in ji Trump.

  4. Maraba

    Barkanmu da saduwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Laraba - ta bawa ranar samu.

    Muna fatan za ku biyo mu domin sanin yadda duniya ke ciki kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar, da kuma maƙoftansu.

    Umar Mikail ne tare da ku a wannan hantsi, da kuma Usman Minjibir da ke kula da shafin.