Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/01/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/01/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Mu kwana lafiya

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Lahadi.

    Muna nan tafe da sababbin rahotonni gobe da safe.

    Kafin lokacin, Ibrahim Yusuf Mohammed ne ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Takaddamar zaɓe ta haifar da zanga-zanga a Romania

    Dubban mutane ne suka yi tattaki a Bucharest babban birnin ƙasar Romania, suna kira da a ci gaba da gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a zagaye na biyu.

    An gudanar da zagayen farko ne a watan Nuwamba, inda dan takara mai ra'ayin mazan jiya, Calin Georgescu, ya zo na ɗaya a wani lamari da ba a yi tsammani ba.

    Ya kamata ya sake fuskantar wanda ya zo na biyu a wani zagayen zaɓen makonni biyu bayan haka, amma kotun tsarin mulki ta Romania ta soke zaɓen, bisa hujjar cewa akwai Rasha ta yi katsalandan cikin lamarin.

    Zanga-zangar ta ranar Lahadi dai ta samo asali ne daga jam'iyyar Alliance for the Union of Romanians Party wadda shugabanta ya dage kan cewa ya kamata shugaba mai ci ya yi murabus.

  3. Gobarar Los Angeles: Ƴansanda sun kama masu sace kayan jama'a

    Ƴansanda a Los Angeles sun yi gargaɗi a kan fakewa da aikin taimako domin satar dukiyar jam'a.

    Babban jami'in rundunar ƴan sandan, Robert Luna, ya shaidawa manema labarai cewa akwai masu zuwa da sunan kai agaji a wuraren da gobara ta tashi, amma suna fakewa da hakan wajen aikata ɓarna.

    Ya kuma sanar da cewa jami'ansa sun kama mutane 30 masu satar kayan mutane a wajen kashe gobarar.

    Robert Luna ya kuma yi gargaɗin cewa yawan mutanen da suka mutu bayan tashin gobarar zai iya ƙaruwa.

    Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Donald Trump, ya bayyana gobarar a matsayin ɗaya daga cikin bala'i mafi muni a tarihin Amurka.

  4. Ambaliyar ruwa ta sake mamaye tsibirin Mayotte

    Yankin tekun Indiya na Mayotte da ke ƙarkashin ikon Faransa ya sake fuskantar mamakon ruwan sama, wanda ya haifar da ambaliya da zaftarewar ƙasa, wata guda bayan guguwar Chido ta lalata sassan tsibiran tare da halaka mutane da dama.

    Bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna kwantattun turakun lantarki da wasu yankuna da ambaliyar ta mamay baki ɗaya.

    Gidan talabijin na cikin gida ya ruwaito cewa ƙauyen Mbouini da ke kudancin ƙasar, wanda shi ne yanki daya tilo da Cyclone Chido bai mamaye ba, yana ƙarƙashin ruwa.

    Guguwar ta baya-bayan nan mai suna Dikeledi ta afkawa arewacin ƙasar Madagascar a ranar Asabar, inda ta kashe aƙalla mutane uku.

    A ranar 14 ga watan Disamba, guguwar Chido ta zama guguwa mafi muni da ta afkawa Mayotte cikin shekaru 90 da suka wuce, inda ta zo da iskar da ke gudun kilomita 260 a cikin sa'a guda.

  5. Ƴan bindiga sun sace wata ƴar Tanzania a Kenya

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty International ta ce wasu mutane ɗauke da makamai a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya.sun sace wata fitacciyar ƴar gwagwarmaya ƴar kasar Tanzania.

    Ƙungiyar ta ce an tafi da Maria Sarungi a mota a ranar Lahadi da yamma. Ms Sarungi ta kasance mai sukar shugabar ƙasar Tanzaniya Samia Suluhu, inda take fafutukar kare haƙƙin mallakar filaye da ƴancin faɗin albarkacin baki.

    Hukumomi a Kenya da Tanzania ba su ce komai ba kan lamarin ba.

    A shekarar da ta gabata jami'an tsaron Uganda sun yi awn gaba da madugun ƴan adawar Uganda Kizza Besigye a birnin Nairobi, inda aka ƙetara iyakar ƙasar domin ya fuskanci shari'a a gaban kotun soji.

  6. Saudiyya ta buƙaci a cirewa Syria takunkumi

    Ministan harkokin wajen Saudiyya ya yi kira da a ɗage takunkumin da aka ƙaƙabawa ƙasar Syria.

    Yarima Faisal bin Farhan yana magana ne a Riyadh, a taron ƙasa da ƙasa na farko da ya kunshi sabbin shugabannin Syria da manyan jami’an diflomasiyya na ƙasashen yammacin duniya tun bayan hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad.

    Hambararren shugaban ya fuskanci tsauraran takunkumai saboda murƙushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a cikin 2011.

    Yanzu haka ƴan tawayen da suka hamɓarar da shi suna ƙoƙarin ganin an kawar da matakan, don taimakawa wajen sake gina ƙasar bayan yaƙin basasa da aka kwashe shekaru da dama ana gwabzawa.

  7. Mahara sun sace wata ƴar Australia a Nijar

    Ma'aikatar harkokin wajen Australia ta tabbatar da sace wata 'yar asalin ƙasar a garin Agadez da kje jamhuriyar Nijar.

    Rahotonni daga ƙasar na cewa wasu mutane ɗauke da makamai suka je har gidan matar mai suna Eva Gretzmacher, suka kuma yi awon gaba da ita.

    Mutanen ɗauke da muggan makamai sun tilasta wa mai gadin gidan mai buɗe musu ƙofar gidan, inda suka shiga sannan suka ɗauke ta a motarsu ƙirar Toyota Land Cruiser V6.

    Matar mai shekara 73 ta shahara wajen ayyukan sadaukarwa da tallafi, inda har ta kafa ƙungiyar "Amanay", ta kirkiro cibiyar fasaha a shekarar 2010, inda take jagorantar ayyuka daban-daban, musamman a fannonin ilimi da karfafawa mata da ilimin halittu da al'adu da fasaha.

  8. Ɓangaren Aminu Ado Bayero ya ce zai ɗaukaka ƙara

    Bangaren sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ɗaukaka ta yanke kan dambarwar masarutun jihar.

    A ranar Juma’a ne kotun ɗaukaka ƙara ta yankee hukuncin cewa babbar kotun tarayya – da ta yi hukuncin dakatar da gwamnatin Kano daga soke masarautun jihar – ba ta da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi masarautu a jihar.

    To sai dai a wani taron manema labarai da Aminu Babba Dangundi – wanda tun da farko ya shigar da gwamnatin Kano ƙara a madadin masarautun da aka rushe – ya yi, ya ce za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

    Ya ce tun da farko gwamnatin Kano da majalisar dokokin jihar ba su bi ƙa’ida ba wajen soke masarautun jihar.

    ‘’Bai kamata a sauke sarki ba tare da ba shi damar kare kansa daga laifin da aka zarge shi a kai ba’’, in ji shi.

    Ya ce tun a ranar da aka yanke hukuncin suka buƙaci kotun ta ba su kwafin takardun hukuncin, kuma a gobe Litinin za su garzaya gaban kotun ƙolin ƙasar domin ɗaukaka ƙarar.

    A ranar Asabar ne dai gwamnatin Kano ta buƙaci ɓangaren Aminu Ado ya yi biyayya ga hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar.

    To sai dai Aminu Babba ya ce Idan aka yi hukunci, kuma aka ɗaukaka ƙara to akan tsaya ne a matsayin da ake har sai kotun ta yi hukunci kan hakan.

    ‘’Saboda ita kotun ɗaukaka ƙara ba ita ce ƙarshe ba, akwai kotun ƙoli – wanda daga ita kuma shikenan dole a yi biyayya da hukuncinta’’, in ji shi.

  9. Trump ya zargi 'yan siyasar California da kasa magance gobarar Los Angeles

    Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi 'yan siyasa a California da rashin ƙwarewa, kan yadda suke tafiyar da gobarar da ke ci gaba da ruruwa a Los Angeles.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ɗan jam'iyyar Republican ɗin ya ce me ya sa aka kasa kashe wutar?

    Gwamnan jihar, Gavin Newsom - wanda ɗan jam'iyyar Demokrats ne - da jami'an gundumar sun ce Mista Trump ya ƙi amsar tarin gayyatar da ake yi masa don ziyartar yankin domin ganin mummunar ɓarnar a wutar ta yi.

    Mutum 16 ne suka mutu a cikin kwana biyar da wutar ta yi tana ci.

    Jami'an kashe gobara na fargabar lamarin ka iya ƙara muni nan da kwana uku masu zuwa, yayin da ake sa ran samun iska mai ƙarfi cikin kwanakin masu zuwa.

  10. Sojoji sun ce sun lalata sansanin Bello Turji tare da kashe 'yanbindiga 25

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar lalata sansanin gawurtaccen ɗan bindigar nan Bello Turji a yankin Fakai na ƙaramar hukumar Shinkafi.

    Cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar da ke yaƙi da 'yanbindiga a arewa maso yamma 'Operation Fansan Yamma' ya fitar, ya ce dakarun sojin sun ƙaddamar da hare-haren ne kan maɓoyar 'yanbindigar a ranar 10 ga watan Janairu.

    ''Bisa taimakon dakarun sojin sama, mun samu nasarar lalata sansanonin wasu 'yanbindiga a yankin Fakai na ƙaramar hukumar Shinkafi'', in ji sanarwar.

    Ya ƙara da cewa daga cikin sansanonin da aka lalata har da na Bello Turji da Mallam Ila, inda aka kashe 'yanbindiga 25 tare da raunata fiye da 18.

    Haka ma ya ce a lokacin samamen sojojin sun kuɓutar da mutum bakwai da 'yanbindigar suka yi garkuwa da su.

  11. Ƙasashen duniya na taron tallafa wa sabuwar gwamnatin riƙon ƙwaryar Syria

    Manyan jami'an Diplomasiyya daga ƙasashen Yamma da Gabas ta Tsakiya na ganawa da ministan harkokin wajen Iran a Riyadh, babban birnin Saudiyya.

    Ana sa rana ganawa za ta mayar da hankali kan hanyoyin da zai tallafa wa gwamnatin riƙon ƙwaryar Siriya.

    Shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Siriyar ya yi kira ga kasashen duniya su ɗage wa ƙasar tarin takunkuman da suka ƙaƙaba mata lokacin mulkin hamɓararren shugaban ƙasar Bashar al-Assad.

    Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ce dole a ci gaba da aiwatar da takunkuman ga ƙasashen ƙawayen hamɓararren shugaban waɗanda suka aikata laifukan yaƙi lokacin yaƙin basasar ƙasar.

  12. An yi jana'izar mutanen da harin jirgi ya kashe bisa kuskure a Zamfara

    Rahotanni daga ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun ce an yi jana'izar 'yan aikin sa kai da wani jirgin yaƙi da ake zargin na sojojiin Najeriya ya kai musu hari bisa kuskure a ƙauyen Tungar Kara.

    Wani mazaunin ƙuyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa tuni aka yi jana'aizar 'yan sa kan su 17 da suka mutu a harin, yayin da wasu ke kwance a asibiti.

    A ranar Asabar da maraice ne wani jirgi da ake kyautata zaton na sojin ƙasar ne ya kai hari bisa kuskure kan 'yan sa kai a ƙauyen na Tungar Kara.

    Lamarin ya auku ne, yayin da suke ƙoƙarin daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai garin, suna ƙoƙarin kore wasu dabbobi.

    Wani mutum - da ya rasa ɗan'uwansa a harin, ya bayyana wa BBC cewa ƴan sa kai da dama ne lamarin ya rutsa da su yayin da suke yunƙurin tunkarar ƴan bindigan da aka ce suna ɓarna a yankin, inda ya kara da cewa ƴan bingidan sun riga sun bar yankin a lokacin da jirgin ya fara ɓarin wuta..

    Ya ce: ''Muna zaune sai muka ga jirgi ya nufi wuraren da aka ce ƴan bindigan suke, amma ko a lokacin sun riga wuce. Waɗannan yaran da mutanen da ke ƙasa ne wannan jirgin yake ta harbi, yanzu haka ga ɗan yaya na an kawo mun shi a mace.''

    Jami'in watsa labarai na rundunar operation Fansar Yamma da ke gudanar da ayyukan tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, inda ya ce zai bincika ya tuntuɓe mu. Haka shi ma mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya shaida mana.

    To sai dai wata majiyar gwamnatin jihar, wanda ta buƙaci a sakaya sunanta, ya tabbatar wa BBC aukuwar wannan lamari, amma bai yi wani cikakken bayani ba.

  13. Kamala Harris na cikin masu gidaje Brentwood

    Yayin da hukumomi suka bayar da umarci washe mutane a Brentwood sakamkon barazanar gobara a yankin.

    Daga cikin waɗanda suka mallaki gida a wurin har da mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, da tsohon gwamnan California, Arnold Schwarzenegger da kuma fitaccen ɗan wasan ƙwallon kwando, LeBron James.

    Shugaban hukumar kashe gobara na gundumar Pasadena, Chad Augustin, ya ce mazauna yankin su zama cikin shirin ko-ta-kwana.

  14. Adadin waɗanda suka mutu a gobarar Los Angeles ya kai 16

    Jami'an lafiya a birnin Los Angeles na Amurka sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon gobarar da ke ci gaba da ruruwa a yankin ya kai 16.

    Ma'aikatan lafiyar sun kuma yi gargaɗin cewa adadin ka iya zarta haka, yayin da wutar da ci gaba.

    Jirage masu saukar ungulu da marasa matuƙa dai na ta ƙoƙarin kashe gobarar wadda ta tashin tun a ranar Talata.

    Tuni hukumomi suka bayar da umarnin kwashe ƙarin mutane yayin da suke fargabar gobarar za ta isa Brentwood, ɗaya daga cikin wuraren mafiya muhimmanci a birnin.

  15. Malala ta buƙaci shugabannin musulmai kada su halasta gwamnatin Taliban

    Fitacciyar 'yar gwagwarmayar ilimin 'ya'ya mata, kuma wadda ta taɓa lashe kyautar Nobel, Malala Yousafzai ta buƙaci shugabannin musulmai kada su halasta gwamnatin Taliban da ke Afghanista.

    Yayin da take jawabi a wani taro da aka shirya kan ilimin yara mata a ƙasashen musulmi a Islamabad, babban birnin Pakistan, Malala ta ce ƙungiyar Taliban ba ta ɗauki mata a matsayin ɗan'adam ba.,

    Ta kuma yi kira ga ƙasashen Musulmi su nuna kyakkyawan jagoranci game da batun bai wa mata ilimi.

    An fitar da Malala Yousafzai daga Pakisatn a lokacin tana da shekara 15, bayan da wani ɗan Pakistan kuma ɗan ƙungiyar Taliban ya harbe ta a lokacin da take cikin motar ɗaukar ɗalibai.

  16. Ukraine ta ce ta kai hari kan wata babbar matatar mai a Rasha

    Ukraine ta ce ta kai hari kan wata babbar matatar mai ta Rasha mai nisan fiye da kilomita 1,000 daga gabashin birnin Moscow.

    Wani jami'in Ukraine Andriy Kova-lenko ya ce matatar man ta Taneko da ke Tatar-stan ta taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa sojojin Rasha.

    Bidiyon da aka yi ta yaɗawa ya nuna wata babbar gobara bayan wani hari da ake kyautata zaton na jirgi maras matuƙi ne.

    A shekarar da ta wuce ma jiragen saman Ukraine marasa matuƙa sun afka wa matatar.

    Babu wani martani daga Rasha har kawo yanzu game da batun.

  17. Sojojin Sudan sun ƙwace birnin Wad Madani daga hannun dakarun RSF

    A karon fakro, shugaban rundunar RSF a Sudan ya amince da cewa dakarunsa sun yi rasa birnin Wad Madani ga rundunar sojin ƙasar da suke yaƙa, a wani koma-baya mafi girma da rundunarsa ta fuskanta tun bayan ɓarkewar yaƙin basasar ƙasar.

    A cikin wani sakon murya, an ji Janar Mohamed Hamdan Dagalo, na magana cikin fushi da takaici, yana lasar takobin ci gaba da yaƙi ko nan da zuwa shekara 20 ne.

    ''A yau mun yi rashin nasara a filin daga, amma ba mu yi nasara a wannan yaƙi ba, watanni 21 kenan muna yakar sojin Sudan, don haka za mu ci gaba da yaƙarsu ko da nan da shekara 21 ne'', in ji Janar Dagalo.

    Ya ƙara da cewa sojojin Sudan yi nasara ne saboda ƙarfinsu a sama, da kuma jirage marasa matuƙan da Iran ke ba su.

    An yi ta gudanar da bukukuwa a wasu sassa daban-daban na Sudan bayan da sojoji suka sanar da kwace birnin.

  18. Jami'ai na ƙoƙarin hana gobarar Los Angeles kaiwa wani wuri mai muhimmanci

    Jami'an kashe gobara a Amurka na ƙoƙarin hana gobarar nan da ke ci gaba da ci a Los Angeles kaiwa Brentwood, ɗaya daga cikin wurare masu muhimmanci a birnin.

    Masana na hasashen dawowoar iska mai ƙarfin gaske, a dai dai lokacin da wutar ke ci gaba da karuwa.

    Ya zuwa an tabbatar da mutuwar mutum 16, sannan ba a san inda kimanin 10 suke ba bayan shafe kwana biyar wutar na ci ganga-ganga.

    Ɗaruruwan jirage na ta zubo ruwa da sinadaran kashe gobara daga sama, a ƙoƙarinsu kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

  19. Marabanku

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Muna fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin sanar da ku halin da duniya ta wayi gari.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhara kan labaran da muke wallafawa.