Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Madrid ko Barca: Wa zai lashe Spanish Super Cup?
Real Madrid da Barcelona za su kara a wasan karshe a Spanish Super Cup a yau Lahadi a Saudi Arabia.
Real Madrid ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta doke Mallorca 3-0 ranar Alhamis a filin wasa na King Abdallah a karawar daf da karshe ta biyu.
Ita kuwa Barcelona ta kai wannan gurbin, saboda cin Athletic Club 2-0 da ta yi ranar Laraba a wasan daf da karshe na farko a dai Saudi Arabia.
Wannan shi ne wasan farko na El Clasico a 2025, karo na huɗu a jere da za su fafata a Spanish Super Cup.
Wannan wasan dama ce ga Barcelona ta ɗauki fansa kan Real Madrid, wadda ta lashe kofin na Spanish Super Cup a bara a kan ƙungiyar Camp Nou.
Shi kuwa Carlo Ancelotti na fatan zai rama doke shi 4-0 da Barcelona ta yi a bara a cikin watan Oktoba a La Liga a Santiago Bernabeu.
Kociyan Barcelona, Hansi Flick na fatan ɗaukar kofi a karon farko a ƙungiyar, wanda ya fara aiki kan fara kakar bana, wanda ya maye gurbin Xavi Hernandez.
Barcelona ce kan gaba a yawan ɗaukar Spanish Super Cup mai 14 jimilla, sai Real Madrid mai 13 da Athletic Bilbao da Deportivo La Coruna da kowacce keda uku.
Jerin waɗanda suka lashe Spanish Super Cup:
- FC Barcelona 14
- Real Madrid 13
- Athletic Bilbao 3
- Deportivo de La Coruna 3
- Atlético de Madrid 2
- Sevilla 1
- Real Zaragoza 1
- Valencia 1
- RCD Mallorca 1
- Real Sociedad 1
Wasa uku baya a jere da aka yi tsakanin Real da Barca a Spanish Super Cup:
Kakar 2023/24 Ranar Lahadi 14 ga watan Janairu 2024
- Real Madrid 4 - 1 Barcelona
Kakar 2022/23 Ranar Lahadi 15 ga watan Janairun 2023
- Real Madrid 1 - 3 Barcelona
Kakar 2021/22 Ranar Laraba 12 ga watan Janairu 2022
- Barcelona 2 - 3 Real Madrid
Da zarar an kammala Spanish Super Cup, Barcelona za ta fafata da Real Beetis a Copa dey Rey zagayen ƴan 16 ranar Laraba 15 ga watan Janairu.
Ita kuwa Real Madrid za ta karbi bakuncin Celta Vigo a Copa del Rey ranar Alhamis 16 ga watan Janairu a Santiago Bernabeu.
Daga nan kuma Barcelona za ta je Getafe a La Liga ranar Asabar 18 ga watan Janairu, ita kuwa Real za ta fafata da Las Palmers ranar Lahadi 19 ga watan Janairu a babbar gasar tamaula ta Spaniya.