Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/10/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. Abin da ya sa 'yansanda ba za su taya EFCC kama Yahaya Bello ba - Fadar shugaban Najeriya

    Kakakin shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya ce jami'an tsaron Najeriya ba su da damar kama tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello saboda ''sarƙaƙiyar'' da ke tattare da shari'ar da ake yi masa.

    Yayin da yake hira da gidan Talbijin na Channels ta cikin shirin ' Inside Sources' a ranar Lahadi, Mista Onanuga ya ce Yahaya Bello na ɓoye ne a gidan gwamnan jihar Kogi wanda shi kuma kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi kariya.

    A watan Afrilun da ya gabata ne hukumar EFCC, mai yaƙi da cin hanci da almundahanar kuɗaɗe ta Najeriya, ta ayyana neman tsohon gwamnan ruwa a jallo, saboda zargin laifukan badaƙalar kuɗi da suka kai naira biliyan 80.2

    Jami'an hukumar EFCC sun taɓa mamaye gidan Yahaya Bello a yunƙurin kama shi, to amma sai sai aka yi zargin cewa gwamnan jihar wanda ya gaje shi, Usman Ododo ya je gidan domin tseratar da shi zuwa gidansa, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

    ''To wannan shi ne dalilin'' a cewar bayo Onanuga, ''saboda matsalar ita ce idan dai Yahaya Bello na gidan gwamna Ododo, to 'yansanda ba za su iya kama shi ba, saboda yin hakan ya saɓa wa kariyar da gwamnan ke da ita''.

    ''Usman Ododo na da kariya, kuma ana ganin Yahaya Bello na ɓoye a gidansa, don haka 'yansanda ba za su iya zuwa gidan domin kama wani ba''.

    ''Batun yana da sarƙaƙiya, EFCC a matsayinta na hukumar gwamnatin tarayya, ba za ta iya kama shi ba idan yana cikin gidan gwamnan da yake da kariya daga tuhuma ko kamu'', in Onanuga.

    Yahaya Bello ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Kogi na tsawon wa'adi biyu.

  2. Shugaban Masar ya buƙaci musayar Isra'ilawa da fursunonin Falasɗinawa

    Shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi ya bayar da shawarar dakatar da buɗe wuta ta kwana biyu a Gaza domin musayar 'yan Isra'ila huɗu da aka yi garkuwa da su, da wasu fursunonin Falasɗinawa.

    Al-Sisi na magana ne da 'yan jarida a Alkahira, babban birnin Masar, yayin da shugaban hukumar leƙen asiri ta Israila, da takwaransa na Amurka, da kuma Firaministan Qatar suka haɗu a babban birnin Qatar, Doha domin shirya sabuwar tattaunawar da za a yi ta tsagaita wuta da yarjejeniyar sakin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su.

    Shugaban na Masar ya ce a bisa shawarar da ya gabatar, za a koma kan cikakkiyar tattaunawa ta tabbatar da dakatar da buɗe wuta ta dindindin cikin kwana 10 da cimma takaitacciyar yarjejeniyar tsagaita faɗan.

    Tun da farko Ministan tsaron Isra'ila, Yoav Gallant, ya ce sakin waɗanda aka yi garkuwa da su zai buƙaci sadaukarwa ko sassautowa mai ciwon gaske.

  3. Za mu mayar da martani kan harin Isra'ila 'daidai wa daida' - Iran

    Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce kodayake ba yaƙi ne a gaban ƙasarsa ba, amma za ta mayar da martani ''daidai wa daida'' kan hare-haren Isra'ila.

    Iran ta yi kiran gaggauta taron kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna batun harin, wanda Isra'ila ta kai a matsayin martanin hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai mata a farkon watan da muke ciki.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce hare-haren na ranar Asabar sun faɗa inda aka buƙace su, wato kan masana'antar ƙera makamai masu linzami na ƙasar.

  4. Shugabar Georgia ba ta gamsu da sakamakon zaben majalaisar dokokin ƙasar ba

    Shugabar Georgia, Salome Zourabishvili, ta ce 'yan ƙasar, sun gamu da kutungwilar aikin musamman na Rasha, inda ta bayyana zaɓen majalisar dokoki da aka yi ranar Asabar a ƙasar a matsayin ƙarya tsagwaronta.

    Shugabar wadda take tare da jagororin 'yan hamayya, ta yi kira ga jama'a su yi gangami a gobe Litinin a kofar majalisar dokokin a Tbilisi domin kin amincewa da sakamakon.

    Shi ma tsohon shugaban ƙasar da aka ɗaure, Mikheil Saakashvili, ya yi kira da ayi gagarumar zanga-zanga ta ƙin jinin gwamnati , tare da ƙaurace wa zaman majalisa.

    Masu sanya ido na duniya sun ce fifikon da aka bai wa, jam'iyya mai mulki a ƙasar ta Georgia, wato Dream Party, ya sa rashin yarda da sakamakon zaɓen, da kuma rashin adalci.

    Ana kallon jamiyyar mai mulki - wadda ta samu nasarar kashi 54 cikin 100 na ƙuri'un - da mai ra'ayin alaƙa da Rasha, yayin da 'yan hamayyar ke da ra'ayin Tarayyar Turai.

  5. Sabon salon kisan fararen hula a Sudan abin damuwa ne - MDD

    Babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana matuƙar damuwa kan rahotonnin ''munanan laifuka'' a jihar Gezira da ke tsakiyar ƙasar, ciki har da kisan fararen hula masu yawa da aka zargi dakarun RFS da aikatawa.

    Kalaman Clementine Nkweta-Salami na zuwa ne bayan wata ƙungiyar 'yan gwagwarmaya ta ce aƙalla mutum 124 ne dakarun RSF suka kashe a hare-hare kan wasu ƙauyukan jihar cikin makon da ya gabata.

    Rundunar RSF ta musanta kai wa fararen hula hare-hare, tana mai cewa mayaƙanta na faɗa ne da ƙungiyoyin 'yan tawayen- da suka ce sojojin Sudan na ba su makamai.

    Yaƙin Sudan da ka ɗauki tsawon wata 18 ana gwabzawa, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba fiye da mutum miliyan 11 da muhallansu.

    A makon da ya gabata, jihar Gezira ya koma filin daga, bayan da rundunar RFS ta fuskanci babban koma baya sakamakon komawar wani babban kwamdandanta ɓangaren sojojin ƙasar.

  6. Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin Kano

    Gwanan jihar Kano Abba Kabiry Yusuf ya rantsar da sabbin shugabannin ƙananna hukumomin jihar da aka gudanar da zaɓensu ranar Asabar a faɗin jihar.

    Hukumar zaɓen jihar ta bayyana jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar da lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44 da kansiloli 484.

    Jami'iyyar APC mai hamayya a jihar ba ta shiga zaɓen ba.

    An gudanar da bikin rantsarwar a fadar gwamnatin jihar, a gaban manyan ƙusoshin gwamnatin jihar da wakilin sarkin Kano da sarakunan Gaya da Rano da Karaye.

  7. Muna aiki tukuru don gyara wutar lantarki a arewacin Najeriya - TCN

    Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya ce yana aiki tukuru wajen ganin an gayra wutar lantarki a arewacin Najeriya, duk da irin kaulubale na rashin tsaro da ake fuskanta a yankin.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Ndid Mbah ya fitar, ya ce matsalar da ake samu na rashin wutar lantarki a jihohi da dama na arewa ya faru ne sakamkon lalata layin bayar da wuta na Shiroro-Mando - wanda shi ke samar da wuta a faɗin yankin.

    "Kalubale na rashin tsaro a yankin na janyo tsaiko wajen kammala aikin gyara layin da kuma mayar da wuta nan take," in ji TCN.

    Kamfanin ya ce ya ɗauki matakin wucin gadi na amfani da layin wutar lantarki na Ugwuaji-Apir mai karfin megawatt 330 don samar da wuta, sai dai shi ma ya samu matsala.

    TCN ɗin ya ce yana aikin haɗin gwiwa da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro domin ganin an kai ga wuraren da aka lalata layukan wuta don gyara su cikin gaggawa.

    "Hakan yana da muhimmanci domin kare rayuka yayin aikin gyara layukan wutar lantarkin," a cewar kamfanin.

    Don haka ya buƙaci al'ummar yankin da su ƙara hakuri saboda suna sane da irin tasirin da rashin wutar ya janyo musamman ga rayuwar yau da kullum.

  8. Ana ci gaba da neman mutanen da hatsarin jirgi ya rutsa da su a Rivers

    Ana can ana ci gaba da aikin neman gawawwakin mutanen da hatsarin jirgi ya rutsa da su a jihar RIbas.

    Jirgin mai lamba SK76 ya yi haɗari ne ranar Alhamis.

    Kamfanin mai na NNPCL ne ya ɗauki shatar jirgin mai saukar ungulu domin kai wasu ma'aikatan kwangila wata rijiyar man kamfanin da ke gaɓar teku.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin na NNPCL, Olufemi Soneye ya fitar yau Lahadi, ya ce babu wani ƙarin gawawwaki da aka gano kawo yanzu.

    Sai dai ya ce hukumomi na can suna ci gaba da aikin ceto, inda ya ce har yanzu akwai gawawwakin mutum biyar da ake nema.

    "Muna son mu sanar da al'umma cewa ba mu sake gano wata gawa ba bayan guda uku da muka gano a hatsarin jirgin da ya faku," in ji NNPCL.

  9. Madrid za ta binciki zargin cin zarafi da aka yi wa Lamine Yamal

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta buɗe bincike kan cin zarafin wariyar launin fata da ake zargin an yi wa matashin ɗan wasan Barcelona Lamine Yamal a wasan El-Clasico da aka buga ranar Asabar a Bernabeu.

    Bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna wani bangare na magoya bayan Madrid suna furta kalamun ɓatanci kan ɗan kasar Sifaniyan mai shekaru 17 da haihuwa yayin da yake murnar ƙwallon da ya ci a minti na 77.

    Sanarwar da Real Madrid ta fitar ta ce: "Real Madrid ta yi kakkausar suka ga duk wani nau'in halayya da ya shafi nuna wariyar launin fata, da kyamar baƙi ko tashin hankali a fagen ƙwallon ƙafa da wasanni, kuma ta yi matukar baƙin cikin cin mutuncin da wasu tsirarun magoya bayan ƙungiyar suka yi a daren asabar a wani ɓangare na filin wasan.''

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya (RFEF) da La Liga sun ɗauki matakai don magance ƙaruwar cin zarafin wariyar launin fata wanda suka haɗa da rufe wani ɓangare na filin wasa.

    A makon da ya gabata, an kama wasu mutane huɗu bisa zarginsu da gudanar da wani gangami a shafukan intanet domin nuna ƙyama da wariyar launin fata a kan ɗan wasan Real Madrid Vinicius Jr.

    Haka kuma an yanke wa wasu magoya bayan Valencia uku hukuncin ɗaurin watanni takwas a gidan yari a watan Yuni saboda cin zarafin ɗan wasan gaban na Madrid a wani wasa a watan Mayun 2023.

  10. Gomman mutane sun jikkata bayan hatsarin babbar mota a Isra'ila

    Gomman mutane ne suka jikkata bayan da wata babbar mota ta yi karo da wajen da fasinjoji ke hawa mota kusa da cibiyar sojin Isra'ila.

    Sai dai ana zargin cewa wani hari ne aka kai dagan-gan kan cibiyar.

    Aƙalla mutum shida na cikin mawuyacin hali yayin da wasu ke ci gaba da maƙale a wurin da lamarin ya faru a yankin Glilot, a arewa da birnin Tel Aviv.

    Ƴansanda sun ce har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano abin da ya janyo hatsarin.

    Sai dai kafafen yaɗa labaran ƙasar ta Isra'ila sun ce wasu mutane ɗauke da maƙamai sun harbi direban motar bayan da kutsa cikin mutane.

    Kafar talabijin ta Isra'ila ta nuna ƴansanda a wajen da lamarin ya faru yayin da jami'an ba da agaji ke taimakawa waɗanda suka jikkata, inda jirgi mai saukar ungulu kuma ke shawagi a sama.

    Wata sanarwa da aka fitar, ta ce ana ci gaba da kula da gomman mutanen da suka jikata.

    Wani mai magana da yawun jami'an motocin ɗaukar marasa lafiya a Isra'ila ya ce yawancin waɗanda suka jikata sun kunshi manya waɗanda suka sauka daga motar bas domin ziyara zuwa shingen dakarun tsaron Isra'ila a Glilot.

  11. Gwamnatin Zamfara za ta yi bincike kan zargin askarawan jihar da 'wuce gona da iri'

    Gwamnatin jihar Zamfara ta ce tana gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa askarawan jihar cewa suna wuce gona da iri wajen gudanar da ayyukansu na tabbatar da tsaro a yankunan jihar.

    Wannan na zuwa ne bayan zargin da wasu mazauna Tsafe suka yi cewa, Askarawan sun kama tare da kashe musu 'yan uwa a lokacin da suke tsare da su.

    Ƴan uwan waɗanda abin ya shafa sun zargi Askarawan da ke aiki a karamar hukumar Tsafe da kashe wani matashi mai suna Hamza bayan kama shi.

    "Wani kaninmu ya tafi gona nan Tsafe, dama bisashe na masa ɓarna kullum yana can yana tsare gonar tasa. Ranar sai ya faɗa wa mai bisashen cewa idan suka sake masa ɓarna zai kai su ga huƙuma," in ji ɗan uwan mamacin.

    Ya ce matan da ya kai karar wurinsu a ce matan ƴan askarawan ne, inda matan suka kira mazajensu suka ce matashin na musu ɓarazana.

    "Daga nan ne suka zo suka kama shi su ka je da shi ofis ɗin su suka riƙa dukansa, jini yana fita ta kunnesa," in ji ɗan uwan.

    Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun faruwar irin haka da ya shafi askarawa a yankin Tsafe ba, inda ko a kwanan baya an samu wani al'amari da ya shafi wani magidanci da ake zargin ya rasa ransa lokacin da yake tsare a hannun askarawan.

    Mazauna yankin sun buƙaci hukumomin Zamfara da su yi wa mamatan adalci ta hanyar ɗaukar mataki akan waɗanda ake zargi ta hanyar hukunta su idan aka same su da laifi.

    Sai dai gwamnatin jihar ta Zamfara ta shaida wa BBC cewa ba ta da matsaniya kan al'amarin, amma a shirye take domin gudanar da bincike.

  12. Ana gudanar da babban zaɓe a Japan

    Jama'a a Japan na kaɗa kuri'a a babban zaɓen kasar, wanda sabon Firaministan ƙasar, Shigeru Ishiba ya kira kwanaki kaɗan bayan an zaɓe shi a matsayin shugaban jam'iyyar Liberal Democratic Party.

    Kuri'ar za ta yanke hukunci kan jam'iyyar da ke iko da majalisar wakilai.

    Ana dai kallon hakan a matsayin wata muhimmiyar jarrabawa ga Mista Ishiba da jam'iyyarsa, wadda ta shiga cikin zargin badakalar kuɗaɗen siyasa.

    Haka kuma ƴan ƙasar na ci gaba da kokawa kan hauhawar farashin kayayyaki da kuma durkushewar tattalin arziki.

    Sai dai duk da damuwar da mutane ke nunawa har yanzu jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayi ta Democratic Party da ke mulkin ƙasar tun bayan kammala yaƙin duniya na biyu, ta fi farin jini a zaɓen.

    A gefe guda jam'iyyun adawa suna ci gaba da fama da yadda za su gamsar da masu kaɗa kuri'a cewa su ne zaɓin da ya dace, sakamakon rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.

  13. 'Najeriya na asarar dala biliyan 26 duk shekara saboda ƙarancin lantarki'

    Najeriya na asarar dala biliyan 26 a duk shekara sakamakon ƙarancin wutar lantarki.

    Wannan na kunshe ne cikin wani sabon rahoton kasuwanci na Afirka da aka fitar.

    Sai dai ya ce asarar ba ta shafi kuɗaɗen da ake kashewa kan na'urorin samar da wutar lantarki ba.

    Rahoton ya ce 'yan kasuwa suna kashe kusan dala biliyan 22 a duk shekara kan fetur don magance tasirin ƙarancin wutar lantarki. Wannan yana ƙara taɓarɓara al'amura.

    Ya bayyana samar da wutar lantarki a matsayin babban kalubale ga harkokin kasuwanci a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya.

    Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun lalacewar babban layin wuta na ƙasa a 'yan kwanakin nan.

    A cikin wannan watan kaɗai, an samu ɗaukewar wutar lantarki a sassa da dama na Najeriya bayan lalacewar babban layin, abin da ya sa hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasar ta danganta hakan da lalacewar transifoma.

  14. Sabbin zaɓaɓɓun shugabannin kananan hukumomi a Kano na shirin shan rantsuwa

    Sabbin zaɓaɓɓun shugabannin kananan hukumomi a Kano na shirin karɓar rantsuwa bayan nasara a zaɓen da aka gudanar jiya Asabar.

    Jam’iyyar NNPP mai mulki ce dai ta lashe duka kujerun a zaɓen.

    Jam'iyyu shida ne suka shiga zaɓen da aka yi ta kai ruwa rana saboda umarnin kotuna daban-daban da ke cewa ka da a yi zaɓen da kuma wadda ke cewa a yi.

    An gudanar da zaɓen ne duk da rashin tsaro daga ‘yan sanda kuma rahotanni na cewa ba a samu tashin hankali ba.

  15. 'Akwai yiwuwar a fuskanci mummunan bala'i a arewacin Gaza'

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi gargaɗin wani “mummunan bala’i” a arewacin Gaza.

    Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce aikin sojin Isra'ila a cibiyoyin kiwon lafiya da kuma ƙarancin kayayyaki na hana ceton rayukan mutane.

    Sojojin Isra'ila sun janye daga asibitin Kamal Adwan ɗaya daga cikin asibitocin karshe da suka rage suna aiki a Jabaliya.

    Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta zargi sojojin da tsare ɗaruruwan ma'aikata, da marasa lafiya da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu.

    Shugaban na WHO ya ce an lalata kayayyakin aiki a asibitocin da dama lokacin da aka yi masu ƙawanya.

  16. Mu muka zaɓi wuraren da muka kai wa hari a Iran - Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce su da kansu suka zaɓi wuraren da Isra'ila ta kai wa hari a Iran jiya Asabar, bisa maslahar ƙasar.

    Yana mayar da martani ne ga masu ganin baiken gwamnatinsa, kan kin kai hari ga cibiyoyin man fetur da tashoshin Nukiliyar Iran, saboda matsin lambar Amurka.

    An shafe makonni ana jiran martanin da Isra'ila za ta mayar, kan harba wa ƙasar maƙami mai linzami da Iran ta yi a farkon wannan watan.

    Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce hare-haren Isra'ilar basu kai yadda aka yi ta zuzutawa ba.

  17. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da hantsin Lahadi.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.