Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe Litinin, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/09/2025.
Umar Mikail
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye.
Sai kuma gobe Litinin, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya.
Mu kwana lafiya.
Dubban masu zanga-zanga sun yi tattaki a Brazil, na nuna kin yarda da wani yunkuri na bayar da kariya ga 'yan majalisar dokoki daga gurfana a gaban shari'a, da kuma yafe wa wadanda suka yi yunkurin juyin mulki a kasar.
Jama'a sun harzuka bayan da majalisar wakilan kasar ta amince da kundin dokar kariyar, da ke bukatar a kada kuri'a cikin sirri ta amincewa da dokar ta hana tuhuma ko kama 'yan majalisa.
Haka kuma majalisar dokokin ta hanzarta amincewa da wani kudurin na yafiya ga wadanda kotu ta kama da laifin hari kan gine-ginen gwamnati - da a iya cewa a takaice, har da tsohon shugaban kasar Jair Bolsonaro, wanda kotu ta yanke wa hukunci a watan nan saboda hannunsa a yunkurin juyin mulkin.
Dukkanin kudurin dokar biyu na fuskantar tirjiya daga majalisar dattawan kasar ta Brazil, kuma Shugaba Lula da Silva ya lashi takobin hawa kujerar-naki a kan kudurin yafiyar.
Dubban masu makoki ne a Amurka suka cika wani filin wasa a Arizona domin halartar taron addu'a ga mai rajin kishin addinin Kirista kuma mai ra'ayin rikau, da aka harbe Charlie Kirk.
Shugaba Trump da matar marigayin - Erika za su gabatar da jawabi. Kafin ya bar fadarsa ta White House, Mista Trump, ya ce taron zai yi alfahari da 'rayuwar babban mutum'.
An harbe Kirk ne a lokacin da yake jawabi ga dalibai a jami'a a jihar Yutah a farkon watan nan.
Kisan ya janyo zazzafar muhawara a kan 'yancin fadin albarkacin baki a Amurka. An tuhumi Tyler Robinson wani matashi mai shekara 22 da kisan.
An kammala kada kuria a zaben amincewa ko watsi da daftarin sabon kundin tsarin mulki a Guinea.
Idan har aka amince da shi, zai bayar da dama a gudanar da zabe nan gaba a shekarar nan, tare da share hanya ga shugaban mulkin sojin kasar Janar Mamady Doumbouya, ya tsaya takara.
Wakilin BBC ya ce, Janar Damboya wanda ya yi juyin mulki shekara hudu da ta wuce, bai ce ko zai tsaya takara a zabe a gaba ba.
Amma ana zarginsa da rufe bakin masu suka, da takurawa 'yan jarida da kuma danne 'yan hamayya.
Daman 'yan hamayyan sun kaurace wa zaben na rafaranda, da cewa tuni an riga an tsara yadda sakamakonsa zai kasance. An baza dubban sojoji da jami'an tsaro a fadin kasar ta yankin Afirka ta Yamma.
Gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Nepal ta naɗa kwamiti mai mutum uku domin binciken tashin-tashinan da aka samu a ƙasar a sanadiyar zanga-zangar adawa da gwamnati da yaƙi da cin hanci da rashawa da aka yi a ƙasar a watan jiya.
Gwamnatin ta naɗa kwamitin ne a ƙarƙashin tsohon alƙalin kotun ƙolin ƙasar, Gauri Bahadur Karki.
Aƙalla mutum 70 ne suka rasu a zanga-zangar, wadda dubban ƴan ƙasar suka gudanar, lamarin da ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin K P Sharm Oli.
Masu zanga-zangar sun ƙone wasu ofisoshi da hukumomin gwamnatin ƙasar, ciki har da kotun ƙolin ƙasar.
Gwamnatin ta buƙaci kwamitin ya bincika tare da gabatar da rahotonsa cikin wata uku.
Matasan da suka yi zanga-zangar ne suka miƙa sunan tsohuwar alƙaliyar kotun ƙolin ƙasar Sushila Karki domin ta maye gurbin firaministan ƙasar da suka kifar.
A cewar masana ilimin halayyar dan'adam, yadda mutum ke tunani ko jin abu ko kuma yadda yake yin abubuwa, shi ke nuna ko wanene shi.
Shin kai mutum ne da ke yi wa abubuwan da ke faruwa a rayuwa mummunan kallo ko kuwa wanda ke da kyakkyawan fata ga rayuwa?
Shin kana jin haushi idan wani ya zo ya sha gabanka a lokacin da kake tuƙa mota, ko kuwa kai mai bayar da uzuri ne — kila ko yana sauri ne za shi asibiti?
Kana jira sai dab da lokaci ya kusan cika kafin ka yi abin da ke gabanka, ko kuwa kana shiryawa tun da wurwuri.
Rahotanni daga China na cewa wata kotu a birnin Shangai ta sake ɗaure wata fitacciyar ƴar jarida kuma ƴar gwagwarmaya na tsawon shekara huɗu a gidan yari.
Tun a shekarar 2020 ne aka tsare Zhang Zhan, inda aka ɗaure ta na shekara huɗu bayan ta yi rahoto kan hargitsin da aka samu a birni Wuhan a lokacin da ake tsaka da annobar cutar Covid-19.
An sake kama ta ne a shekarar 2024 bisa zarginta da tayar da husuma da tayar da hankalin jama'a a ƙasar - tuhumar da ake amfani da ita a ƙasar China wajen yaƙi da ƴan gwagwarmaya.
Ƙungiyar kare haƙƙin ƴanjarida ta Reporters Without Borders ta ce an sake ɗaure Zhang Zhan ne bayan wata sabuwar shari'ar a ranar Juma'a a Shangai, inda za ta sake zaman gidan kaso na shekara huɗu.
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce jami'anta sun kashe mayaƙa sama da 25 a wasu hare-hare da suka kai a yankin Bula na jihar Yobe da Banki na jihar Borno.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Ehimen Ejodame ya fitar a ranar Asabar.
A cewarsa, sojojin na Najeriya sun kai farmakin ne haɗin gwiwa a ranar 18 ga watan Satumba bayan samun bayanan sirri.
Ya ce hakan ya sa suka yi amfani da fasahar zamani wajen ganowa da tattara bayanan zirga-zirgar mayaƙan, sannan suka far musu.
"Sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe aƙalla ƴanta'adda guda 25 a wani farmakin haɗin gwiwa a yankin Bula na jihar Yobe da yankin Banki na jihar Borno a ranar 18 ga Satumba," in ji shi.
Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta bayyana amincewa da ƙasar Falasɗinu a matsayin "saka wa ƙungiyar Hamas - wadda ke samun ƙwarin gwiwa daga Musulman Birtaniya".
Cikin wani saƙo a dandalin X, ma'aikatar ta soki matakin na Birtaniya da Canada da Australia da suka sanar a yau Lahadi.
"Shugabannin Hamas sun sha bayyanawa cewa wannan amincewar sakamako ne kai-tsaye na harin ranar 7 ga watan Oktoba," in ji sanarwar.
A yanzu, fiye da kasashe 150 cikin 193 mambobin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ne suka amince da kasar Falasdinawa a matsayin mai 'yanci.
Ciki har da mambobin kungiyar ƙasashe Larabawa a MD, da kungiyar hadin kan kasashen Musulmi, da kuma kungiyar yan ba-ruwanmu wadanda ba su nuna matsayarsu ba.
Wasu kasashen Turai na daga cikinsu - kamar Sifaniya da Ireland da Norway waɗanda suka amince da Falasdinu a matsayin kasa a Mayun 2024. Gabanin haka, kasashen Turai kalilan ne suka yi haka - galibinsu a 1988.
Sai dai babbar mai mara wa Isra'ila baya wato Amurka ba ta amince ba, har ma tana sukar masu yin hakan tare da kiran su da su dakata.
Ita ma ƙasar Australia ta sanar da amincewa da ƙasar Falasɗinawa, inda ta bi sawun Birtaniya da Canada.
Kafin yanzu, ƙasashen Canada da Ausrtralia sun bayyaa a baya cewa sai a taron Majalisar Ɗinkin Duniya za su bayyana amincewa da ƙasar ta Falasɗinu, wanda za a fara a gobe Litinin.
Firaministan Canada Mark Carney ya ce daga yau (Lahadi) "Canada ta amince da ƙasar Falasɗinu" a hukumance.
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalin X, Mista Carney ya ce:
"Canada ta amince da ƙasar Falasɗinu kuma muna miƙo tayinmu na taimakawa wajen samar da zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila."
Birtaniya ta sanar da amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yanci.
"A yau, domin dawo da shirin samar da zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila, da kuma samar da ƙasa biyu, Birtaniya ta amince da ƙasar Falasɗinu a hukumance," a cewar Firaministan Birtaniya Keir Stermer cikin wani jawabi.
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya kama hanyar zuwa Amurka domin jagorantar tawagar ƙasar a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) karo na 8.
Za a yi taron daga gobe Litinin zuwa Lahadi 28 ga watan Satumba, inda Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a madadin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
Wannan ne karo na biyu a jere da Shettima ke jagorantar tawagar Najeriya zuwa taron - bayan ya yi hakan a watan Satumban 2024.
Jakadan Falasɗinawa a Birtaniya Husam Zomlot ya faɗa wa BBC cewa yunƙurin da ƙasashen Yamma ke yi na amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa "gyara laifukan baya" ne.
Zomlot ya kuma ce Hukumar Falasɗinawa na shirin gudanar da zaɓe nan gaba kaɗan. "Amma yanzu ba zai yiwu ba saboda shingayen ababen hawa, da ta'addancin 'yan kama-wuri-zauna a Gabar Yamma da Kogin Jordan," in ji shi.
Ya ƙara da cewa amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa "nuhimmin abu ne" kuma duk wanda yake ganin bai dace ba to "ba shi da tunanin ci gaba".
Ƙarin 'yan Najeriya 148 ne suka koma gida daga Sudan a ranar Alhamis da ta gabata, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta sanar Asabar.
Matafiyan sun sauka a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana ɗauke da maza manya 25, da mata manya 27, da yara maza 39, da yara mata 57.
Kamfanin Tarco ne ya yi jigilar mutanen, waɗanda aka kai su otel ɗin Chila domin tantancewa jim kaɗan bayan sun sauka.
"Ba a saka su cikin wani shiri ba, kuma an sallame su tare da ba su kudin mota ta hanyar ba su katin ATM jim kaɗan bayan kammala tantance su," in ji sanarawar da Nema ta fitar.
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ne zai jagoranci tawagar ƙasar zuwa taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) karo na 80 da za a yi a watan nan, a cewar fadar shugaban ƙasa.
Hakan na nufin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba zai je taron ba, kuma wannan ne karo na biyu a jere da Shettima ke jagorantar tawagar ta Najeriya zuwa taron.
Sai dai fadar ba ta faɗi takamaiman dalilin da ya sa Tinubu ba zai je taron ba, wanda shugabannin ƙasashen dunya ke halarta duk shekara a hedikwatar MDD da ke birnin New York na Amurka.
Wata sanarwa daga ofishin mataimakin shugaban ta ce Shettima zai bi sawun takwarorinsa na ƙasashen duniya wajen tafka muhawara a zauren daga ranar Talata zuwa Lahadi 28 ga watan Satumba.
Amma sai a ranar Laraba Shettima "zai gabatar da jawabin Najeriya a tsakanin ƙarfe 3:00 zuwa 9:00 agogon New York", in ji sanarwar.
"Bayan kammala taron UNGA, mataimakin shugaban zai wuce Frankfurt na ƙasar Jamus, inda zai gana da jami'an Bankin Deutche kafin ya dawo Najeriya."
Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar kashe mutum biyu a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta ƙasa ta bayyana.
National Emergency Management Agency (Nema) ta bayyana cikin wata sanarwa a yau Lahadi cewa jami'anta da suka ziyarci wuraren da ruwan ya auka wa sun yadda ruwa ya ɗaiɗaita dukiyoyi da amfanin gona.
Ta ce mutanen da suka mutu wani ɗan shekara 51 ne da kuma wani ƙaramin yaro, yayin da wasu yaran biyu suka raunuka.
"Ambaliyar ta shafe garuruwan Ghandi, da Mai Kujera, da Tsamiya waɗanda suke cikin ƙaramar hukumar Raban," in ji Nema.
"Bugu da ƙari, ta wnake amfanin gona mai yawa, abin da ya jawo fargabar ƙarancin abinci a yankunan da lamarin ya shafa."
A cewar sanarwar, waɗanda suka rasa matsuganansu na samun mafaka a filin wasa da kuma firamare na Rabah, yayin da wasu suka koma gidajen 'yan'uwa da abokan arziki.
Yau Lahadi ne Birtaniya za ta amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yancin kanta.
Wata biyu da suka gabata ne Firaministan Birtaniya Kier Stermer ya yi gargaɗin cewa Birtaniya za ta dauki wannan mataki idan har Isra'ila ba ta kawo karshen yakinta a Gaza ba.
Wakilin BBC ya ce a wani jawabi ta bidiyo da ake sa ran zai gabatar, ana sa ran firaministan zai ce "a'ummar duniya na da haƙƙin sauke wani nauyi da ya rataya a wuyansu domin karfafa fatan samar da zaman lafiya.
Sai dai Amurka da Isra'ila sun soki matakin, suna bayyana shi a matsayin saaka wa Hamas duk da harin da ta kai na ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Su ma kasashen Faransa da Portugal da Canada da Australia sun ce za su amince da kasar Falasdinun a cikin wannan mako.