Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/08/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/08/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Peter Obi ba zai iya cin arewa a 2027 ba saboda kafuwar Tinubu a yankin'

    Ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo ya ce ɗaya daga cikin jagororin sabuwar haɗakar ADC, Peter Obi ba zai iya cin yankin arewacin Najeriya a zaɓen 2027, sakamakon yadda Shugaba Tinubu ya kafu a yankin.

    Yayin wata hira da gidan talbijin na Channels, Keyamo ya ce Shugaba Tinubu da jam'iyyarsa ta APC, sun samu kafuwa da tsari a yankin arewacin Najeriya.

    Ministan jiragen saman ya kuma ce da wahala haɗakar ADC ta iya yin wani tasiri a fagen siyasar ƙasar.

    ''Babu inda za su je, indai don batun samun magoya baya ne'', in ji Keyamo.

    “Wannan haɗakar da suke kira ADC, abin da take yi shi ne ƙoƙarin haɗa Atiku da Obi a 2027, domin zartar adadin ƙuri'a miliyan takwas da muka samu a 2023'', in ji shi.

    “Idan ka tsayar da Obi takara, a yanzu ba zai iya cin arewa ba, saboda yadda muka kafu. Muna da gwamnoni da jagoranci kai ƙarfi a yankin'', in ji ministan.

    A zaɓen 2023 da Tinubu ya yi nasara ne da ƙuri'a sama da miliyan takwas, yayin da Atiku da ya zo na biyu ya samu ƙuri'a kusan miliyan bakwai, sai Peter Obi da ya zo na uku ya samu ƙuri'a sama da miliyan shida.

  2. Ƴan matan Najeriya sun lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka

    Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka.

    Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi.

    Ƴan wasan Najeriyar sun kankane gasar ƙwallon kwandon Afirka, inda suka yi nasara sau 29 a jere a duka wasan da suka buga ba tare da rashin nasara ba tun 2015.

    Nasarar D’Tigress na zuwa ne kimanin mako guda bayan da tawagar Super Falcons ta ƴan wasan ƙwallon kafar matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon ƙafar matan Afirka, karo na 10 a tarihi.

  3. 'Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa a wurin rabon abinci a Gaza'

    Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin Isra'ila sun sake buɗe wuta kan Falasɗinawa da ke cikin tsananin buƙatar agaji a kusa da inda ake rabon kayan tallafi a cibiyoyi biyu, a jiya Lahadi.

    Asibitoci a Gaza sun ce aƙalla Falasdinawa 27 aka kashe.

    Rahotanni na cewa sojojin sun buɗe wa mutane wuta bayan isa gab da ɗaya daga cikin cibiyoyin rabon agajin na gidauniyar da Amurka da Isra'ila ke mara wa baya a Rafah.

    Sanan sauran kuma an kashe su ne a sansanin da ke tsakiyar Gaza.

    Har yanzu sojojin Isra'ila ba su yi martani ba kan wannan rahoton.

    Hamas ta ce ƙungiyar agaji ta Red Cross kaɗai za ta iya miƙa wa 'yan Isra'ilar da take riƙe dasu a Gaza idan har aka cimma daidaituwar ba da dama a shigar da kayan agaji a duk sassan zirrin.

  4. Ambaliya ta cinye gidaje da gonaki a jihohin Najeriya uku

    Ambaliya ta cinye gonaki da gidaje da makarantu da wuraren ibada a jihohin Bauchi da Filato da kuma jihar Neja, lamarin da ya tilasta wa ɗaruruwan mutane barin gidajensu.

    Mazauna yankunan da lamarin ya faru sun ce ruwan saman da aka samu kamar da bakin ƙwarya haɗe da iska a wayewar garin ranar Lahadi, ya kayar da bishiyoyi tare da tsige turakun lantarki da ɗaye kwanukan rufi lamarin da ya sa gine-gine da dama suka faɗi.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa fiye da gine-gine 50 ne suka rushe sakamakon ambaliyar a garin Menkaat na ƙaramar hukumar Shendam a jihar filato.

    Can a ƙaramar hukumar Dass ta jihar Bauchi fiye da magidanta 40 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar da ta lalata gonaki masu yawa a cewar Jaridar.

    Haka a jihar Neja kusan garuruwa 18 ne suka fuskanci ambaliyar a ƙaramar hukumar Lapai ta jihar Neja, inda ruwa ya cinye gonaki masu yawa.

    Lamarin na zuwa ne dai a daidai lokacin da hukumar hasashen yanayi ta ƙasar, (Nimet) ke gargaɗin samun ruwan sama haɗe da tsawa da yiwuwar samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar.

  5. MDD ta ce mazauna El Fasher na cikin tsananin yunwa

    Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce iyalan da ke maƙalle a birnin El Fasher da ke Sudan sama da shekara guda na cikin tsananin Yunwa.

    WFP ya kuma yi gargaɗin cewa babu alamar kawo ƙarshen mamayar dakarun RSF.

    Mayaƙan RSF na ta kokarin ganin sun ƙwace illahirin birnin da ke arewacin Darfur daga Sojojin Sudan da ke iko da birnin.

    Tun cikin watan Afrilu ne mayaƙan na RSF suka yiwa birnin Kawanya, tare da datse hanyoyin kai abinci da sauran kayan tallafi ga dubban mutanen da ke maƙale ke buƙata.

    WFP ya ce iyalai da dama sun koma cin abincin dabobbi da abinci da ya lalace domin su rayu.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, mande tushen aiki ko da nasara na tsoranki, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Sannunmu da sake haɗuwa da ku a wannan shafi domin kawo muku yadda duniya ta wayi gari.

    Kada ku manta ta shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.