Amnesty ta buƙaci kotun ICC ta daina jinkiri wajen binciken laifuka a yaƙi da Boko Haram
Ƙungiyar Amnesty International ta kai kokenta ga alƙalan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC a madadin waɗanda aka yi zalinta domin daƙile yadda masu shigar da ƙara na kotun ke jan ƙafa wajen neman haƙƙin waɗanda aka yi wa laifi a Najeriya.
A watan Disamban 2020 ne masu gabatar da ƙara na International Criminal Court (ICC) suka ce dukkan sharuɗa sun cika domin fara binciken laifukan da aka aikata a lokacin yaƙin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya tun daga 2010.
Cikin laifukan har da waɗanda mayaƙan masu iƙirarin jihadi suka aikata, da kuma wanda ake zargin dakarun sojin Najeriya da aikatawa.
Amnesty ta ce ya kamata ne a ce an kai buƙatar hakan ga alƙalai masu sauraren korafe-ƙorafe, idan sun amince sai a fara bincike.
"Amma shekara huɗu ke nan har yanzu ofishin mai gabatar da ƙara a ICC bai gabatar da buƙatar ba," in ji Amnesty.
A cewar shugaban Amnesty a Najeriya, Isa Sanusi: "Waɗanda aka zalinta a Najeriya sun cancanci adalci kamar sauran waɗanda aka zalinta a wasu wuraren. Sun daɗe suna jira a yi musu adalci, bai kamata kotun ICC ta manta da Najeriya ba."