Likitoci a Khartoum sun yi gargaɗin ɓarkewar kwalara a ɗaukacin birnin
Likitoci a Khartoum babban birnin Sudan sun yi gargaɗin ɓarkewar cutar kwalara a birnin baki-ɗaya.
Ƙarancin wutar lantarki da hare-haren da sojoji ke kai wa ya kawo cikas ga samar da ruwa, kuma mazauna yankin na shan gurɓataccen ruwa.
Lamarin ya kara kamari cikin gaggawa tun bayan da mayakn RSF suka fara kai hari kan tashoshin lantarki da wuraren adana man fetur makonni uku da suka gabata.
Ma'aikatar lafiva ta ƙasar ta sanar da mutuwar mutane sama da 50, yayin da cutar ta ƙara bazuwa sakamakon ƙarancin ayyukan jinya a birnin Khartoum.
Ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa-kai na RSF a yammacin kasar.
Dubban mutane ne suka rasa matsugunansu a yankunan Darfur da Kordofan.