Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye. Sai Allah ya kai mu gobe Lahadi.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammmed nake cewa mu kwana lafiya
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/05/2025
Ahmad Bawage
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye. Sai Allah ya kai mu gobe Lahadi.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammmed nake cewa mu kwana lafiya
Jami'ai a Ukraine sun ce an azabtar da kashi 95 cikin fursunonin ƙasar da suka yi musaya da Rasha a baya-bayan nan a lokacin da ake tsare da su a gidajen kason ƙasar.
Sun kuma ce an azabtar da su da yunwa da rashin kula da lafiyarsu, sannan an kuma cusa musu ra'ayi na daban domin juya musu tunani.
Shugaba Zalensky ya ce duk da hakan, Rasha ta ci gaba da kai munanan hare-hare Ukraine, hakan alama ce ta ba ta shirya kawo ƙarshen yaƙin ba.
Mr Zalensky ya ce lokaci ya yi da za a matsa wa Rasha lamba a cimma abubuwan da ake buƙata, kuma hakan na nufin a kawo ƙarshen yaƙin nan.
Kawo yanzu ɓagaren Ukraine da Rasha sun yi musayar fursunoni sama da 300 daga kowanne ɓangare, a rana ta biyu da fara hakan.
Wakilan gwamnatin Syria sun kai ziyara a karon farko, sansanin al-Hol da ake tsare da dubban Ƙurdawa.
Cikin waɗanda ake tsare da su har da ɗaruruwan mata da ƴaƴan waɗanda ake zargin masu ikirarin jihadi ne.
Dakarun Ƙurdawa ne dai ke gadin sansanin tun bayan kawo ƙarshen yaƙin basasar da aka yi shekara biyar da suka gabata.
A watan Fabrairu, gwamnatin Ƙurdawa ta sanar da aniyarta ta rufe dukkan sansanonin da ƴan Syria da Iraqi ke ciki, a ƙarshen wannan shekarar.
An kafa wani kwamiti da ya haɗa wakilan gwamnatin Syria da Amurka da ta Ƙurdawa domin sanya ido kan yadda za a gudanar da aikin.
Hukumar Bayar da Bashin Karatu ta Najeriya Nelfund ta ce ta ba ɗaliban Najeriya rancen kuɗi naira biliyan 56.55 domin biyan kuɗin makaranta da alawus ɗin kashewa na yau da kullum.
Hukumar ta bayyana haka ne domin bayyana nasarorin da ta samu a cikin shekara ɗaya da fara aiki tun bayan ƙirƙirar shirin.
A wata sanarwa da daraktan sadarwa na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi ta fitar, ya ce sama da ɗalibai 600,000 ne suke nami rancen, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
"Bayan tantancewa, mun amince tare da ba ɗalibai 550,000 rancen, inda muka ba su kuɗi naira biliyan 56.85 a cikin shekara guda."
"Tsarin bayar da rancen ya taimaka wajen sauƙaƙa wa ɗaliban Najeriya da iyaye," in ji ta.
Ministan yaɗa labaran Najeriya Mohammed Idris ya gargaɗi ƴan ƙasar kan amfani da ƙirƙirarrun bidiyo domin nuna shugabannin ƙasar a wani yanayi mara kyau domin ɓata musu suna.
Jaridar The Nation mai zaman kanta ta ruwaito ministan yana cewa, "mun ga yadda ake amfani da ƙirƙirarriyar basira ta hanyoyin da suka dace, da hanyoyin da ba su dace ba. Zai iya yiwuwa kana zaune a nan kawai sai wani ya yanko kanka ya ɗaura a wani jikin domin ɓata maka suna."
"Muna ganin yadda ake juya maganar shugaban ƙasa, inda zai faɗa abu daban, amma sai a canja abin da ya faɗa. Ko kuma minista ya faɗa wani abu, sai a juya masa magana," in ji shi.
Ya ƙara da cewa suna duba lamarin sosai a matakin gwamnati, "musamman yadda za mu tsaftace kafofin sadarwa ba tare da tauye haƙƙin furta albarkacin baki ba."
Mahaifiyata ta kasance ta saka min doka ta cire takalmi yayin shiga cikin gida. Ba ta la'akari da ko ma waye zai ziyarce gidanmu ba, ko da a ce baƙo ne ko makwabci, dole ne sai sun cire takalmi kafin shiga cikin gida.
Lokacin da nake ƙarama, na yi tunanin mahaifiyata na da tsauri. Amma lokacin da na fara fahimtar kaina na fara girma, shine na gane cewa ba tsafta kaɗai take yi wa haka ba, harda ma saboda lura da lafiyarmu.
Tsafta tabbas tana da mahimmanci. Amma idan ana maganar takalma, abin da yake haɗari shine datti wanda ba za a iya ganinsa ba wanda ke taruwa a ƙasan takalmanku.
Jam'iyyar hamayya a ƙasar Kamaru ta Opposition Cameroonian National Reconciliation Party (PCRN) ta sanar da jagoransu, Cabral Libii a matsayin ɗantakararta na shugaban ƙasa.
Za a gudanar da zaɓen ne a watan Oktoba mai zuwa kamar yadda kafar RFI ta ruwaito.
Libii ne ya sanar da hakan a ranar 23 ga watan Mayu bayan babban taron jam'iyyar da aka yi a garin Nkolafamba da ke birnin Yaounde.
Ya ce shugabannin jam'iyyar PCRN ɗin ne suka amince ya tsaya takara, bayan tantance sauran waɗanda suka nuna sha'awarar tsayawa takarar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan jam'iyyun hamayya a ƙasar suke kira da a haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tunkarar Shugaba Paul Biya mai shekara 92 a babban zaɓen mai zuwa.
Tuni an lashe kofuna a wasu gasar Turai a bana, an fayyace waɗanda suka yi ban kwana da wasannin kakar nan, an samu wasu da za su buga Champions League a badi.
Kenan abin da ya rage shi ne wanda zai lashe ƙyautar takalmin zinare a matakin wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a kakar nan.
Lokiacin da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ke kan ganiya suke taka leda a Turai, sun karɓi ƙyautar a karo da yawa, haka kuma Thierry Henry da Luis Suarez da kuma Robert Lewandowski duk sun lashe ƙyautar.
Ƙungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta cika yarjejeniyar da suka shiga a shekarar 2009 ko ta tsunduma yajin aiki.
Shugaban ASUU, Chris Piwuna ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma'a a Abuja.
Ya nanata buƙatar da ke akwai na gwamnatin ta cika yarjejeniyar da alƙawuran da ta ɗauka domin magance matsalolin da jami'o'in ƙasar ke fuskanta.
Piwuna ya ce har yanzu akwai wasu muhimman batutuwa guda tara da ba a daddale su ba a yarjejeniyar da suka shiga.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa daga cikin abubuwan da suka rage akwai albashin malaman da ba a biya ba lokacin da suke yajin aiki na shekarar 2022 da wasu alawus ɗinsu da ake riƙe saboda IPPIS da sauransu.
Ya ce duk da alƙawarin da gwamnati ta yi na zuba naira biliyan 150 domin gudanar da jami'o'in ƙasar da inganta alawus na malaman, har yanzu ba su gani a ƙasa ba.
Ƙasar Masar ta kwashe ƴan ƙasarta 71 daga Tripoli, babban birnin ƙasar Libya bayan rikici tsakanin ɓangarorin ƴanbindiga biyu ya fara ƙamari a birnin.
Wannan na zuwa ne bayan ƙasashen Italiya da Spain da Turkiyya da Pakistan sun kwashe nasu mutanen daga birnin na Tripoli.
Wannan rikicin ya faro ne bayan kashe wani jagoran ƴantawayen, Abdulghani Kiki mako biyu da suka gabata.
Firaministan ƙasar Abdul Hamis al-Deiba ya ce ba zai fara tattauna batun shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da ƴantawayen ba, har sai sun fice dafa Tripoli.
Tun bayan hamɓarar da mulkin Muammar Gaddafi a shekarar 2011 ne dai ƙasar take a rabe, kuma take cikin rikice-rikice.
Yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da faɗaɗa farmaki a Gaza, an ruwaito kashe ƴaƴan wata likita guda tara wadda ke aiki a asibitin Khan Younis, a wani hari da Isra'ila ta kai.
Hotunan bidiyo da aka wallafa sun nuna lokacin da ake fitar da gawawwaki da suka ƙone daga cikin ɓaraguzai.
BBC ta nemi jin martani daga sojojin Isra'ila.
Jami'an agaji da na lafiya sun ce gomman Falasɗinawa ne aka kashe a wasu hare-hare da Isra'ilar ta kai cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Hukumomin Isra'ila sun ce an aika motocin agaji 83 zuwa Gaza ranar Juma'a, sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce adadin agaji da aka bari zuwa yankin ya yi kaɗan, ba zai kuma wadatar ba.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na wata tattaunawa da shugaban Syria Ahmed al-Sharaa a birnin Istanbul, kwanaki kaɗan bayan da Amurka da Tarayyar Turai suka sanar da cewa za su ɗage takunkuman da suka kakaba wa ƙasar lokacin mulkin Assad.
Shugabannin biyu za su tattauna kan yiwuwar kulla alaƙar tsaro, ciki har da batun horas da sabbin sojojin Syria da Turkiyya za ta yi da kuma kirkiro da sansanonin sojin saman Turkiyya a Syria.
Turkiyya na son daƙile barazana daga ƙungiyoyin mayaƙa na Kurdawa da ke Syria da kuma nuna kanta a matsayin mai taka rawa wajen sake gina Syria bayan yaƙi.
Isra'ila na nuna damuwa kan goyon bayan da Turkiyya ke bai wa gwamnatin Sunni da ke da cibiya a Damascus.
Kamfanin kula da albarkatun man fetur na Najeriya NNPCL, ya sanar da cewa za a rufe matatar mai ta Fatakwal domin yin wasu gyare-gyare.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da NNPCL ya fitar a shafinsa na X, inda ya ce za a fara aikin daga yau Asabar, 24 ga Mayun 2025.
"Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA, don tabbatar da cewa aikin gyare-gyaren ya tafi yadda ake so da kuma bisa gaskiya," in ji NNPCL.
Kamfanin ya ce a shirye yake a kowane lokaci wajen samar da isasshen makamashi a Najeriya.
lyalan mutanen da suka mutu a haɗuran da jiragen Boeing 737 Max suka yi a Indonesia da Habasha sun yi Alla-wadai da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kamfanin ƙera jiragen da ma'aikatar sharia ta Amurka.
Yarjejeniyar za ta sa Boeing ya biya sama da dala biliyan ɗaya a matsayin tara da diyya, da kuma kaucewa tuhumar da ake yi masa ta yaudarar mahukunta game da amincin tsarin kula da jiragensa.
Lauyan da ke wakiltar yawancin iyalan mutane 346 da suka mutu yayin haɗurran kamfanin, ya kira yarjejeniyar a matsayin wadda ba a taɓa gain irinta ba wajen rashin adalci.
Aƙalla mutum 14 ne suka jikkata bayan da Rasha ta ka harin makami mai linzami kan birnin Kyiv, a cewar hukumomi.
Rasha ta kaddamar da harin jirage marasa matuki 250 da kuma na makaman linzami 14 a birnin Kyiv, a cewar sojojin saman Ukraine, abin da ya janyo ɓarkewar gobara a gine-gine da dama.
Wannan na ɗaya daga cikin hari mafi muni da aka kai birnin tun soma yaƙin.
Sojojin saman ƙasar sun ce sun kakkɓe makaman linzami shida da kuma na jirage marasa matuki 245.
"Duk wani hari da aka kai, yana ƙara nuna cewa Mosocow ba ta son kawo karshen yaƙi," kamar yadda shugaba Zelensky ya wallafa a shafinsa na X.
Harin ya zo ne a daidai lokacin da Rasha da Ukraine ke musayar fursunoni wanda aka amince da shi bayan tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu a Turkiyya.
Ɗan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na kakar bana.
Wannan ne karo na biyu da Salah ya lashe kyautar, wanda ake yi bayan haɗa kuri'un jama'a da na masana harkar kwallon kafa - ɗan wasan ya taɓa lashe kyautar a kakar 2017-2018.
Salah wanda ya jagoranci ƙungiyarsa wajen lashe gasar Premier, ya doke abokan takararsa da suka haɗa da Virgil van Dijk da Ryan Gravenberch da kuma Declan Rice.
Sauran waɗanda ya doke a lashe kyautar sun kunshi Alexander Isak da Bryan Mbeumo da kuma Chris Wood.
Wannan ne karo na farko tun kakar 2018-2019 da ɗan wasan Manchester City bai lashe kyautar ba.
Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Masar ya zura kwallaye 28 da kuma bayar da 18 aka ci a wannan kakar da ke daf da karewa.
Gwamnatin tarayya ta ce za yi wa ƴan Najeriya gwanjon rukunin gidaje da ta ƙwace a Abuja a hannun tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele.
Bayanin haka ya fito ne lokacin da ministan ma'aikatar gidaje da raya birane Ahmed Dangiwa da kuma shugaban hukumar EFCC Olanipekun Olukoyede, suka jagoranci wata tawaga zuwa rukunin gidajen da aka ƙwace, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
EFCC ce ta ƙwace gidajen waɗanda ke alaƙa da Emefiele a watan Disamban 2024, inda aka miƙa su ga ma'aikatar bayan umarni da shugaba Tinubu ya bayar.
Lokacin ziyarar gani da idon, Dangiwa ya sanar da cewa ma'aikatar za ta fara aikin duba ingancin gidajen.
Ya ce bayan kammala duba su, za a samar da wani shafi wanda ƴan Najeriya za su shiga su nemi damar saya.
Ministan ya ƙara nanata zimmar gwamnatin tarayya wajen yin komai bisa gaskiya da adalci, inda ya yi kira ga jami'an gwamnati da su guji shiga abubuwan da ba su dace ba.
A watan Afrilun 2025 ne, wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan Babban Bankin na neman a dawo masa da rukunin gidajen da gwamnati ta ƙwace.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya yi Alla-wadai da harin da ƴanbindiga suka kai kan al'ummomin Munga Lelau a karamar hukumar Karim Lamido na jihar, abin da ya janyo mutuwar mutane da ba a san adadinsu ba.
Ƴanbindigar sun kai harin ne a lokacin da mutane ke komawa gida daga gonakinsu.
Lamarin ya afku da yammacin ranar Juma'a, makonni kalilan bayan wasu da ake zargin ƴanbindiga sun kashe wasu manoma biyu a yankin Bandawa na jihar.
Gwamna Kefas ya ce ba za a lamunci kai irin waɗannan hare-hare ba, inda ya ce suna mayar da jihar baya maimakon ci gaba.
Ya gargaɗi masu kai harin da cewa za su ɗanɗani kuɗarsu.
Ya kuma ƙara nanata cewa yana duk mai yiwuwa domin tsare jihar daga hare-hare da ake kai wa.
Ya ƙara da cewa akwai buƙakatar haɗa-kai tsakanin al'umma da jami'an tsaro, musamman wajen bayar da bayanan da suka kamata.
Rundunar 'yan sandan a jihar Kaduna sun damke wata mata da ke kauyen Malari a yankin karamar hukumar Soba ta jihar, bisa zargin kisan wani jinjirin kishiyarta ɗan wata uku da haihuwa.
Al'amarin ya auku ne a makon da ya gabata a gidan da matar ke zaune tare da kishiyar tata, yayin da uwar jinjirin ta shiga bandaki, ta bar yaron shi kadai a waje. Tana dawowa sai ta tarar da jaririn nata a hannun uwar gidan.
Kakakin 'yansandan jihar DSP Mansir Hassan, ya shaida wa BBC lamarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Mayu:
''Bayan ta amshi yaron sai ta ga kumfa na fitowa daga bakin yaron da kuma yanayin nau'inshi yana canzawa. Wannan ya sa aka garzaya da yaron asibiti, inda kafin a garzaya da shi ma asibitin Allah ya amshi rayuwarshi.
Mai magana da yawun 'yansandan yya ce bayan sun samu wannan labari ne suka tura jami'ansu inda suka yi nasarar kama wannan mata Zaliha, wadda bayan bincike ta tabbatar musu da kanta cewa, ta ba wannan yaro maganin asid ya sha domin ta kashe shi saboda kishi.
DSP Hassan ya ce, ''Abin da ya tabbatar mana bayan bincike shi ne, akwai kanin shi mai gidan wanda ya sayo mata asid ɗin bayan ta gaya mishi cewa ita fa ba ta sha'awar ganin wannan yaron.
Gwamnatocin ƙasashen Turai sun yi gargaɗin cewa tattalin arzikin ɓangarori biyu a Tekun Atlantika na iya faɗawa cikin rashin tabbas matsawar shugaba Trump ya aiwatar da aniyarsa ta lafta harajin kashi 50 cikin 100 kan kayayyakin da EU ke shiga da su.
Wasu dai sun yi watsi da alwashin Trump din, suna mai bayyana shi da tada kura kawai, don yin razani da kuma samun nasara a teburin tattaunawa.
Wakilin BBC ya ce kwamishinan kasuwanci na EU, ya ce a shirye ƙungiyar take ta kare muradanta, da zuciya ɗaya ba wai barazana ba.