Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 04/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Amurka ta yi fatali da ƙudirin MDD na tsagaita wuta a Gaza

    Amurka ta hau kujerar na-ƙi game ƙudirin da aka gabatar a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta a yaƙin Gaza ta dindindin ba tare da sharaɗi ba.

    Sauran mambobin kwamitin 14 sun amince da buƙatar ƙudirin, wanda kuma ya buƙaci sakin duka Isra'ilawa da ake garkuwa da su tare da ɗage taƙaita shigar da agaji zuwa Gaza.

    Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniyar, Dorothy Camille Shea, ta ce ƙudirin ya gaza shafar kowane ɓangare saboda bai yi kira ga Hamas ta ajiye makamanta tare da ficewa daga Zirin Gaza ba.

  2. Azabar da Falasɗinawa ke ciki ta fi ta jahannama - Shugabar ICRC

    Shugabar ƙungiyar agaji ta Red Cross, wato ICRC ta bayyana cewa halin da ake ciki a Gaza ya zarta azabar jahannama.

    A hirarta da BBC, a shalkwatar ƙungiyar da ke birnin Geneva, Mirjana Spoljaric ta ce matsalar ''jin ƙai na ƙara ta'azzara'', yayin da take ganin masifun yaƙin Gaza.

    BBC ta tambayi Ms Spoljaric game da kalaman da ta yi cikin watan Afrilu cewa Gaza ce ''jahannamar duniya'', ko a yanzu ta sauya matsayarta?

    "Ai lamarin ya ma zarta hakan… Bai kamata mu zura ido muna ci gaba da ganin abin da ke faruwa ba. Lamarin ya wuce hankali da shari'a da tunanin ɗan'adam, la'akari da girman yadda aka ruguza yankin da yawan wahalar da aka jefa mutane''.

    "Abu mafi muhimmanci shi ne, ganin yadda aka hana wa mutane kimarsu ta ɗan'adamtaka. Abin yana tayar da hankalinmu.''

    Ta ƙara da cewa dole ne ƙasashe su yi duk mai yiwuwa domin kawo ƙarshen yaƙin, da ƙarshen wahalar da Falasɗinawa ke ciki da kuma sakin Isra'ilawan da ake garkuwa da su.

    ICRC ƙungiyar agaji ce ta duniya da ta kwashe kusan shekara 150 tana aikin kawar da wahalhalun da yaƙi ya samar a faɗin duniya.

  3. Putin ya ce Rasha za ta ɗauki fansa kan Ukraine - Trump

    Donald Trump ya ce Shugaba Putin na Rasha ya faɗa masa ta waya cewa Moscow za ta ɗauki fansa bayan harin Ukraine kan jiragen yaƙinta a ƙarshen mako.

    Wani jami'in ƙungiyar tsaro ta NATO da ba a ambaci sunansa ba, ya ce jiragen yaƙin Rasha fiye da 40 aka lalata a lokacin harin.

    Shugaban na Amurka ya bayyana tattaunawar wayar da ya yi da Putin a matsayin ''kyakkyawar hira'', to amma ya ce ba za ta kai ga tsagaita wuta a nan kusa ba.

    Ya ce ya faɗa wa Putin cewa Ukraine ba ta ba shi shawarar kai harin ba.

    Fadar gwamnatin Rasha ta ce Shugaba Putin ya kuma zanta da Fafaroma Leo, inda ya jaddadama ƙudirinsa na cimma tsagaita wuta ta hanyar lalama.

    Rahotonnin sun ce Mista Putinya shaida wa sabon fafaroman cewa Ukraine ce ke rura wutar yaƙin ta hanyar kai hari cibiyoyin fararen hula.

  4. MDD za ta kaɗa ƙuri'ar buƙatar tsagaita wuta a Gaza nan take

    Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kaɗa ƙuri'a kan wani daftarin buƙata da ke neman tsagaita wuta na dindindin nan take a Gaza, ba tare da gindaya wasu sharuɗɗa ba.

    Daftarin da aka cimma matsaya a kai - wanda ƙasashe 10 na kwamitin sulhu na majalisar ya samar - na kuma buƙatar a saki dukkanin mutanen da ake garkuwa da su a Gaza, sannan kuma a ɗage duk wani takunkumin shigar da kayan tallafi zuwa yankin da aka ƙaƙaba.

    Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa ana sa ran Amurka, wadda ɗaya ce daga cikin ƙasashe biyar masu kujeran dindindin a kwamitin - za ta hau kujerar na-ƙi kan shawarar.

  5. Ban taɓa zuwa wurin boka don neman a sake zaɓe na gwamna ba - Soludo

    Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya tuntuɓi wani boka domin buƙatar sake zaɓarsa matsayin gwamnan jihar a wa'adi na biyu.

    Ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar da muke ciki ne hukumar zaɓen Najeriya ta saka domin gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

    A cinin ƴan kwanakin nan ne wani bidiyo ya karaɗe shafukan sada zumunta da ke iƙirrarin cewa gwamnan ya tuntuɓi wani boka domin neman ''sa'ar'' sake zaɓarsa.

    To sai dai cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Christian Aburime, ya fitar, gwamnan ya bayayna zargin a matsayin ''tsagwaron ƙarya''.

    Sanarwar ta ce bidiyon da ake yaɗawar an ɗauke shi ne a lokacin wani taro da jami'an gwamnati suka yi da masu wallafa abubuwa a shafukan sada zumunta na jihar.

  6. Mutanen da suka yi tafiyar wata bakwai kan doki domin zuwa aikin Hajji

    Wasu matasa uku sun yi tafiyar watanni kan doki zuwa Makkah domin aikin Hajji.

    Sun yi tafiyar dubban kilomitoci kan sirdi domin bin wata daɗaɗɗiyar hanyar ƙasa da Musulman Andalus suka riƙa amfani da ita shekaru 500 da suka gabata domin zuwa aikin Hajji.

    Mutanen sun yi tafiyar sama da wata bakwai kafin isa ƙasar Saudiyya.

  7. Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu a Legas

    Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu a gidanke da ke birnin Legas.

    Cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ya kai ziyarar ne tare da ƴan'uwansa, babban yayaransa Adedeji Adeleke, da kuma ɗandan'uwansa, fitaccen mawaƙin nan David Adeleke da aka fi sani da Davido, gabanin bukukuwan babbar sallah.

    Kodayake babu cikakken bayani kan abin da tattaunawar tasu ta ƙunsa, ganawar na zuwa ne kwanaki bayan Davido ya gana da Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a wani abu da ake ganin tattaunawa ce tsakanin dangin Adeleke da fadar shugaban ƙasar.

    A cikin watan da ya gabata ne hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta saka ranar 20 ga watan Yulin 2026 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun.

    Ana ganin Gwamna Adeleke - wanda ɗan jam'iyyar PDP ne - zai tsaya takara a zaɓn domin neman wa'adin mulkinsa na biyu, bayan da aka zaɓe shi a karon farko a 2022.

  8. An kwashe mutum 20,000 daga gidajensu don kwance bam ɗin Yaƙin Duniya na Biyu

    Birnin Cologne na Jamus ya kwashe mutum 20,500 da gidajensu daga wani yanki saboda a samu damar kwance bamabamai uku da aka ɗana yayin Yaƙin Duniya na Biyu.

    An gano bamabaman ne da Amurka ta harba a ranar Litinin a wani fili da ke unguwar Deutz, a cewar unguwar cikin wata sanarwa.

    Har yanzu bamabaman da ba su tashi ba barazana ce kuma birnin ya killace yankin da ya kai faɗin mita 1,000.

    Gidaje da shaguna da otel-otel da makarantu, duka an umarce su da su rufe, har ma da wani babban asibiti da babbar tashar jirgin ƙasa.

    "Idan mutum ya yi gardama za mu kore shi daga gidansa da ƙarfi idan ta kama bisa taimakon 'yansanda," a cewar hukumomin yankin.

  9. An haramta wa kafafen yaɗa labarai ɗaukan labarin Joseph Kabila

    Gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo ta hana kafafen yada labarai ɗaukan rahoto game da tsohon shugaban ƙasar, Joseph Kabila da jam'iyarsa.

    Gwamnatin Kinshasa ta ce za ta tuhumi Mista Kabila da cin amanar ƙasa bayan zargin sa da alaƙa da ƴan tawayen M23 da Rwanda ke goya wa baya.

    Ba a daɗe da janye masa kariya daga fuskantar hukunci ba. Shugaban Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ya shaida wa ƴan jarida cewa za a dakatar da su idan suka karya ka'ida.

    Hanin ba zai yi tasiri a yankin da ke ƙarkashin ikon ƴan tawaye a gabashin Congo ba, inda Mista Kabila ke zaune a yanzu, kafafen yada labarai za su ci gaba da yada manufofinsa da izinin ƙungiyar M23 wadda Rwanda ke goyon baya.

    A makon da ya gabata ne Mista Kabila ya sauka a birnin Goma wanda ke ƙarƙashin ikon ƴan tawayen M23, bayan shekaru biyu ya na gudun hijira.

    A baya Kabila ya musanta alaƙa da ƙungiyar M23.

  10. Tinubu ya bai wa mutanen Mokwa tallafin naira biliyan biyu da shinkafa tirela 20

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince da bai wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Neja gudumawar kuɗi naira biliyan biyu da kuma tirela 20 na shinkafa.

    Shettima ya sanar da hakan ne a garin Mokwa, lokacin ziyarar da ya kai bayan ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita garin wadda ta lalata dukiya da kadarori da kuma sanadiyyar salwantar ɗaruruwan rayuka.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya ce za a magance duk wasu matsaloli da ke addabar al'ummar.

    Inda ya ce shugaban ƙasar ya bayar da umarnin gyara gadojin da ambaliyar ta lalata ba tare da ɓata lokaci ba.

    Hukumomi sun tabbatar da mutuwar sama da mutum 200 a ambaliyar ta ƙaramar hukumar Makwa da ke jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya.

    Haka nan akwai sama da mutum 500 da ba a san inda suke ba, wani abu da ake fargabar zai ƙara yawan mutanen da suka rasa rayukansu.

  11. Alhazan Najeriya sun isa tantunansu a Mina domin fara aikin Hajji

  12. BBC ta musanta zargin da gwamnatin Amurka ta yi mata kan labarin yaƙin Gaza

    Kafar yaɗa labarai ta BBC ta yi watsi da sukar da fadar gwamnatin Amurka ta yi mata, tana mai musanta cewa ta goge wani labari da ta wallafa game da yaƙin Isra'ila a Gaza.

    Yayin taron manema labarai na ranar Talata, mai magana da yawun Shugaba Donald Trump Karoline Leavit ta zargi BBC da "amfani da kalaman Hamas" yayin ba da rahoto kan adadin mutanen da aka kashe a kusa da wani wurin karɓar abincin tallafi ranar Lahadi.

    Sannan ta yi iƙirari na kuskure cewa BBC ta goge wani labari.

    "Iƙirarin cewa BBC ta goge wani labari bayan kallon wani bidiyo ba gaskiya ba ne kwatakwata. Ba mu goge wani labari ba kuma muna nan kan bakarmu," a cewar BBC cikin wata sanarwa.

    Karoline Leavitt ta soki BBC game da sauya adadin mutanen da aka kashe a kan labarin. Amma BBC ta ce an yi sauya kan labarin ne a duka tsawon ranar da sabbin alƙaluma "wanda da ma haka ake yi a kowane labari da yake tsaka da faruwa".

  13. Isra'ila ta kai hare-hare cikin Syria

    Sojojin Isra'ila sun yi amfani da jiragen yaƙi da makaman atilare wajen kai hare-hare a kudancin Syria, wanda suke cewa martani ne kan wasu makamai biyu da aka harba musu daga yankin Syria da suke da iyaka.

    Isra'ila ta ce ta kai hare-haren ne kan rumbun makaman gwamnatin Syria.

    Kafar yada labaran Syria na cewa sun tafka asara har da rasa rai a yankin Daraa. Ma'aikatar harkokin waje da ke Damascus ta ce babu sahihan bayanai kan wadanda suka kai hari a yankin Tuddan Golan.

    Ministan tsaron Isra'ila ya ce sun ɗora wa shugaban Syria Ahmed al-Sharaa alhakin abin da ya faru.

  14. Ambaliyar Neja: An gano gawar mutum bakwai

    Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar mutum bakwai da ambaliyar ruwa ta binne ƙarƙashin ɓaraguzai a jihar Neja, kamar yadda hukumar agaji ta jihar Nsema ta bayyana.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban hukumar Abdullahi Baba Arah na cewa hakan ya sa adadin waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu ya zama 160 a ranar Talata. Sai dai alƙaluman sun sha bamban da waɗanda gwamnatin jiha da na ƙaramar hukumar suka bayar na mutum 200.

    Abdullahi ya ce mutanen gari ne suka taimaka wajen aikin ceton, inda aka zaƙulo gawa huɗu ranar Litinin, da kuma uku ranar Talata.

    A jiya Talata kwamashinan agaji na jihar, Ahmad Sulaiman, ya ce sama da mutum 200 ne suka mutu, sannan ana neman wasu da dama.

    Wani jami'in ƙaramar hukumar Mokwa ya faɗa wa BBC cewa mutanen da suka mutu sun kai 230 sannan ana neman sama da 400 da suka ɓace.

  15. Isra'ila ta kashe Falasɗinawa takwas a hari kan makaranta, in ji likitoci

    Aƙalla Falasɗinawa takwas aka kashe tare da raunata wasu da dama sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan wata makaranta a yankin Khan Younis da ke kudancin Zirin Gaza, a cewar likitoci da kuma shaidu.

    Shaidun da suka ga lamarin sun ce wani jirgin Isra'ila maras matuƙi ne ya hari tanti biyu da ke ɗauke da gwamman Falasɗinawa, ciki har da mata da ƙananan yara waɗanda ke neman mafaka.

    Wani ma'aikacin lafiya a hukumar tsaron fararen hula ta Hamas ya turo saƙo ta dandalin WhatsApp cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar mutum takwas zuwa yanzu, cikinsu akwai yara biyu.

    Kazalika sun kai sama da mutum 20 asibiti, inda wasu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.

    'Yanjarida sun ce a kwanan nan ne ɗaruruwan 'yan gudun hijira suka isa makarantar daga yankin al-Amal da ke Khan Younis ɗin bayan rundunar sojin Isra'ila ta umarce su da su fice daga wurin.

    BBC ta nemi jin ta bakin rundunar sojin ta Isra'ila IDF game da batun.

  16. Kifewar kwale-kwale ta kashe mutum biyar a jihar Sokoto

    Mutum bakwai ne suka rasu sakamakon kifewar kwalekwale a yankin ƙaramar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto a arewacin Najeriya.

    Lamarin ya faru ne a lokacin da matafiyan suka fito daga Gidan Hussaini zuwa ƙauyen Gwargawu a ranar Litinin da misalin ƙarfe 9:30 na safiya, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta ƙasa Nema ta bayyana.

    Nema ta ce bayanai sun nuna iska mai ƙarfi ce ta haddasa kifewar jirgin ruwan.

    A watan Oktoban 2024 ma wani jirgi ya kife da kusan mutum 300 a yankin Mokwa na jihar Neja da ke tsakiyar Najeriyar. Kafin haka, mutum 24 ne suka mutu a kifewar wani jirgin a watan Satumban 2023 a jihar.

  17. An dakatar da raba kayan tallafi a Gaza saboda kashe Falasɗinawa

    An dakatar da ayyukan gidauniyar rabon tallafin nan da Amurka da Isra'ila ke goyon-baya a Gaza na wuni guda a yau Laraba sakamakon yadda ake ta kashe Falasɗinawa yayin karɓar tallafin.

    Rundunar sojin Isra'ila ta yi gargadin cewa hanyoyin isa sansanonin rabon kayan abinci wurare ne da aka ayyana a matsayin filin daga.

    Ƙungiyar da ke yawan fuskantar suka ta ce sai zuwa gobe Alhamis za ta dawo da ayyukanta sabdoda ta samu damar inganta ayyukanta.

    Gwamman Falasdinawa aka dinga kashewa a lokacin da suka yi kokarin karɓar abinci tun daga ranar Lahadi.

    Wani jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya ce ya zama tilas a yi bincike da babu son zuciya domin hukunta masu laifi.

  18. Maraba

    Barkanmu da hantsin Laraba.

    Za mu kawo rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Ku biyo ni Umar Mikail domin sanin halin da duniyar ke ciki bisa kulawar Usman Minjibir.