Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 13/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Muhammad Annur Muhammad

  1. An bayyana jagoran 'yan hamayya na Mauritius a matsayin Firaminista bayan gagarumar nasara a zaɓe

    Shugaban Mauritius, Prithvirajsing Roopun ya bayyana sunan babban jagoran 'yan hamayya na ƙasar Navin Ramgoolam, a matsayin sabon firaministan ƙasar, bayan da jam'iyyarsa ta samu gagarumar nasara a zaɓen majalisar dokoki.

    Kafar yaɗa labarai mai zaman kanta ta Defi Media da ke ƙasar ita ce ta ruwaito labarin a jiya Talata.

    Haɗakar jam'iyyun hamayya ta ci kujeru 60 na majalisar dokoki, inda wannan nasara ta zama mai tarihi a siyasar ƙasar.

    Sabuwar gwamnati da za a kafa ta yi alƙawarin yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima, tare da gudanar da zaɓen hukumomin ƙauyuka da birane duk bayan shekara biyar.

    Tsohon Firaminista na baya-bayan nan Pravind Jugnauth, ya amince da shan kaye a zaɓen wuri da aka yi ranar 11 ga watan nan na Nuwamba, ya kuma sauƙa bayan shekara bakwai a kan mulki.

    A shekara ta 2017 ya gaji mahaifinsa a matsayin firaminista.

    Ramgoolam, mai shekara 77, zai kasance firaminista a karo na uku, kasancewar ya riƙe muƙamin a baya daga shekarar 1995 zuwa 2000, sannan kuma ya sake hawa tsakanin 2005 da 2014.

    Ya fito ne daga gidan iyalan ɗaya daga gidajen da suka mamaye siyasar ƙasar ta Mauritius, tun da ta samu 'yanci a 1968.

  2. Chadi ta haramta wa wasu jiga-jigan jam'iyya mai mulki takarar zaɓen majalisa

    Hukumar zaɓe ta ƙasar Chadi ta (ANGE), ta haramta wa wasu manyan 'yan jam'iyya mai mulkin ƙasar (MPS) tsayawa takarar zaɓen majalisar dokoki da za a yi ranar 29 ga watan Disamba mai kamawa.

    Rahotanni sun ce, hukuncin hana jiga-jigan uku na jam'iyyar mai mulki - Mahamat Zene Bada, da Ibrahim Wang Laouna Foullah, da kuma Mariam Djimet Ibet ya zo da mamaki.

    Foullah da Djimet tsofaffin magadan garin babban birnin ƙasar ne, N'Djamena.

    Hukumar zaɓen ta ce an ƙi amincewa da buƙatar manyan jami'an ne su uku saboda bambance-bambance a sunayensu da kuma ɓarnata kuɗaɗen gwamnati da suka yi.

    Haka ita ma jam'iyyar, PSF, ta yi watsi da waɗanda ta kira haramtattun 'yantakara da aka bayar da sunayensu a ƙarƙashinta.

    Manyan jam'iyyun hamayya na ƙasar ta Chadi sun ƙaurace wa zaɓen majalisar dokokin da kuma na birane da za a yi bayan da gwamnati ta gaza cimma wasu buƙatunsu.

  3. Gwamnatin Abia za ta riƙa gurfanar da iyayen da suka ƙi sa ƴaƴansu a makaranta a kotu

    Gwamnatin jihar Abia ta ce duk wani uba da ya ƙi sa ɗansa a makaranta za ta gurfanar da shi gaban shari'a daga ranar 1 ga watan Janairu na sabuwar shekara mai kamawa, 2025.

    Kwamishinan yaɗa labarai, na jihar Okey Kanu ne ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa ta jihar a babban birnin jihar Umuahia, jiya Talata.

    Mista Kanu ya ce, bisa tanadin dokar inganta rayuwar yara ta 2006, yanzu laifi ne ga iyaye su ki tura 'ya'yansu makaranta a jihar.

    Ya ƙara da cewa :“Ilimi kyauta ne a jihar Abia har zuwa matakin ƙaramar sakandire. Babu dalilin da zai sa iyaye su ƙi sa 'ya'yansu a makaranta.”

  4. Ƴan Najeriya sama da miliyan 28 ba sa mu'amulla da bankuna - CBN

    Babban Bankin Najeriya ya ce akwai 'yan ƙasar sama da miliyan 28 da ba su da hanyoyin mu'amulla da banki - yawancinsu kuma suna yankuna ne na karkara.

    Mataimakin gwamman bankin mai kula da fannin hada-hadar kuɗi, Philip Ikeazor, wanda ya bayyana haka jiya Talata, ya ce, bankin da sauran masu ruwa da tsaki suna aiki tuƙuru domin rage wannanan matsala ta yadda za a samar da hanyoyin mu'amulla da bankuna da jama'a.

    Ya ce, alƙaluma sun nuna waɗanda ke cikin wannan rukuni na waɗanda ba su da hanyar samun bankuna yawanci mata ne da matasa da al'ummomin karkara da masu 'yan ƙanana da ƙanana da kuma matsakaitan sana'o'i.

    Mista Ikeazor, wanda ke magana a Lagos a wajen taron ƙasa da ƙasa na wannan shekara kan mu'amullar jama'a da bankuna ya ce, matakan da bankin yake ɗauka ne ma ya sa aka samu raguwar mutanen da ba sa mu'amulla da bankunan daga kashi 46.3 a 2010, zuwa kashi 26 cikin ɗari a wannan shekara - wanda shi ne sama da mutum miliyan 28.

  5. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 23 a Lebanon

    Aƙalla mutum 23 ne aka kashe a wasu hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai kan wasu gine-gine biyu a tsakiyar Lebanon, wajen da aka ruwaito cewa iyalai waɗanda aka ɗaiɗaita na rayuwa a ciki, a cewar ma'aikatar lafiya a Lebanon.

    Mutum 15, yawanci mata da ƙananan yara aka kashe a garin Joun sannan aka kuma kashe wasu takwas a kusa da Baalchmay.

    Dukkan ƙauyukan suna a wani tsauni ne da kuma wajen yankunan da Hezbollah ke da karfi.

    Sojojin Isra'ila sun ce suna duba batun hare-haren, waɗanda ke zuwa a daidai lokacin da suka ce harin ya faɗa kan shingayen Hezbollah da ke wajen kudancin birnin Beirut.

  6. MDD ta soki Isra'ila kan aikata laifukan yaƙi a Gaza

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake fitar da kakkausar suka kan matakan da Isra'ila ke ɗauka a zirin Gaza, inda ɗaya daga cikin shugabannin hukumominta ya ce Isra'ilar ta na aikata munanan laifukan yaƙi.

    Sa'o'i kaɗan gabannin wa'adin da Amurka ta ginɗaya na ba da damar kai kayan agaji, sai ma'aikatar cikin gida a Amurka ta fito ta ce Isra'ila ba ta take wata doka ta Amurkar ba, kuma ana samun ci gaba kan shirin kai agajin.

    Joyce Msuya da wasu jami'an uku sun shaida wa kwamitin tsaro na MDD yadda rayuwa ta ke a Gaza a kowacce rana, Falasɗinawa Mata da maza, yara da manya har tsofaffi na fama da matsananciyar yunwa.

    Shi ma wani jami'an MDD ya ce jami'an sra'ila na amfani da yunwa a matsayin makamin yaki a Gaza.

  7. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Laraba - ta bawa ranar samu.

    Ku kasance da mu a wannan shafi na labarai kai-tsaye domin sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.