Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 13/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Muhammad Annur Muhammad

  1. An kama wanda ake zargi da fillewa wani magajin gari kai a Mexico

    Jami'ai a ƙasar Mexico sun kama wani mutum da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa magajin garin Chilpancingo a watan jiya.

    Kisan Alejandro Arcos, wanda aka tsinci gawarsa kwanaki kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin magajin gari, ya haifar da kaɗuwa da bacin rai a jihar Guerrero mai fama da tashin hankali.

    A ranar Talata, ƴan sanda sun damƙe Germán Reyes, wanda shi ne babban jami'in tsaro a Chilpancingo, bisa zarginsa da hannu a kisan.

    Germán Reyes dai ya musanta cewa yana da hannu a wannan aika-aika kuma ya ce ana amfani da shi ne a matsayin wanda ake son a yi misali da shi.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun daɗe suna yin gargadin cewa wasu kungiyoyi masu aikata miyagun laifuka na kutsawa jami’an tsaro na cikin gida a Mexico, ta hanyar cin hanci da rashawa da kuma yin barazana ga rayukansu.

    Kisan gillar da aka yi wa magajin garin Arcos a cikin mako guda da hawansa mulki a ranar 1 ga watan Oktoba, da kama Reyes da aka yi a ranar Talata mutane da yawa a Chilpancingo na ganin ƙarin shaida ne na ƙoƙarin da kungiyoyi masu aikata manyan laifuka ke yi na kara ƙarfi a birnin da hukumominta.

  2. Eritrea ta soki yadda ƙasashen waje ke katsalandan a yaƙin Sudan

    Shugaban Eritrea Isaias Afwerki ya yi ƙira da a kawo kawo ƙarshen tsoma bakin da ƙasashen waje ke yi kan rikicin Sudan, kamar yadda ministan watsa labarai Yemane Gebremeskel ya wallafa a shafinsa na X.

    Shugaba Isaias ya yi wannan kira ne a jiya lokacin da yake tattaunawa da wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman a Sudan Ramtane Lamamra.

    "Shugaban ya yi bayani a buɗe cewa Eritrea ta yi amannar za a kawo ƙarshen rikicin Sudan ne idan ɓangarorin da suke yaƙin suka amince da hakan, amma ba ta hanyar katsalandan ɗin ƙasashen waje ba da hakan ke haifar da koma baya a yunkurin samar da zaman lafiya a ƙasar," in ji Yemane.

    Eritrea ta daɗe tana sukar "tsangwama daga waje" a yaƙin basasar Sudan da ya ɓarke a watan Afrilun 2023.

    An zargi Hadaddiyar daular larabawa da Masar da Iran da Rasha da samar da makamai ga ɓangarorin da ke hamayya da juna.

  3. An kashe wasu majinyata a Haiti - MSF

    Kungiyar agajin likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce aƙalla majinyata biyu ne aka kashe a Haiti bayan ƴan sanda da ƴan sai-kai sun kai hari kan motar ɗaukar marasa lafiya a babban birnin Port-au-Prince.

    Ƙungiyar ta ce ma’aikatanta sun yi jigilar majinyata uku da suka samu raunukan harbin bindiga zuwa asibitin MSF a ranar Litinin ɗin da ta gabata lokacin da hukumomi suka tsayar da su tare da tilasta musu zuwa asibitin gwamnati.

    Lokacin da suka isa, jami’ai da “’yan kungiyar kare kai” ne suka far wa motar, inda suka sare tayoyinta tare da fitar da mutanen da ke cikin motar ta hanyar banka musu hayaki mai sa hawaye.

    Sa'an nan kuma an ɗauke majinyatan da suka jikkata daga harabar asibitin inda "aka kashe a kalla biyu daga cikinsu", in ji ƙungiyar likitocin.

    Bayanin daga MSF bai tabbatar da halin da ɗaya majinyacin ke ciki ba. Sai dai ƙungiyar ta ce jami’an tsaro da ƴan kungiyar kare kai sun ci zarafin ma’aikatan motar ɗaukar marasa lafiyar.

    Tun bayan kisan da aka yiwa shugaba Jovenel Moïse a shekarar 2021, gungun ƴan daba sun karɓe iko a yankuna da dama na Haiti, lamarin da ya haifar da ƙaruwar tashe-tashen hankula a kan tituna a ƙasar mafi talauci a nahiyar Amurka.

  4. Rasha ta aike da dakarunta Equatorial Guinea

    Rahotanni sun ce ƙasar Rasha ta aike da dakaru kusan 200 zuwa ƙasar Equatorial Guinea domin kare fadar shugaban kasar, yayin da take ci gaba da faɗaɗa tasirinta a nahiyar Afirka.

    Kafofin yaɗa labarai sun ce sojojin Rasha na horar da manyan masu gadi a manyan biranen ƙasar guda biyu - babban birnin ƙasar Malabo da Bata.

    Rahotannin sojojin Rasha da aka tura ƙasar sun fara bayyana ne a cikin watan Agusta.

    Ƙasar Rasha da ke neman ƙarin ƙarfin faɗa a ji a nahiyar Afirka, a shekarun baya-bayan nan dai ta tura dubban sojojin haya zuwa ƙasashen yammaci da tsakiyar Afirka domin kare gwamnatocin soji da kuma taimaka musu wajen yaki da masu tada ƙayar baya.

    Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto majiyoyi na cewa daga cikin ƴan ƙasar Rasha 100 zuwa 200 ne aka kiyasta sun isa ƙasar a cikin watanni biyun da suka gabata.

    Ya ce akwai yiyuwar wasu su kasance cikin rundunar Africa Corps, rundunar sojojin da aka fi sani da Wagner kafin a canza sunanta kuma a hukumance ta koma ƙarƙashin ikon sojojin Rasha.

    Ƙaramar ƙasar mai yawan al'umma miliyan 1.7 tana ƙarƙashin jagorancin shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, shugaban da ya fi daɗewa kan karagar mulki a duniya, wanda ya ke mulki tun shekarar 1979.

  5. An damke shugaban hukumar ƙwallon kafa ta Afirka ta kudu bisa zargin Almundahana

    An bayar da belin shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta Kudu (SAFA), Danny Jordaan, bisa zarginsa da amfani da kuɗaɗen hukumar don biyan bukatun kansa.

    Sashen binciken manyan laifuka na ƙasar, Hawks, yana duba zargin zamba da almundahana a SAFA tsakanin 2014 zuwa 2018 wanda ya kai $ 72,000.

    Ana zargin Jordaan da hayar wani kamfani mai zaman kansa don kare lafiyarsa da kuma kamfanin hulɗa da jama'a ba tare da izini daga hukumar SAFA ba.

    Jordaan mai shekaru 73, wanda ya kasance jigo wajen kawo gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 2010 zuwa Afrika ta Kudu, ya kasance shugaban SAFA tun shekarar 2013,

    An kama shi ne a ranar Laraba kuma ya bayyana a gaban kotun Majistare ta Palm Ridge da ke birnin Johannesburg.

    An dai bayar da belin waɗanda ake tuhuma da suka haɗa da babban jami'in kuɗi na SAFA Gronie Hluyo da ɗan kasuwa Trevor Neethling, waɗanda suka bayyana a kotu tare da Jordaan.

    Masu sukar Jordaan dai sun dade suna kira gare shi da ya yi murabus, inda suke nuni da gazawar tawagar ƙwallon ƙafa ta maza na samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya tun shekara ta 2010 da kuma tabarbarewar ababen more rayuwa na kwallon kafa a ƙasar.

  6. Za mu kawo ƙarshen mayaƙan Lakurawa – Ribadu

    Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da kawo ƙarshen ƙungiyar 'yan ta’adda da ake kira ‘Lukarawa’ a shiyyar Arewa maso yammacin nan ba da jimawa ba.

    Ribadu ya bayyana haka ne a lokacin da ya wakilci shugaban kasa Tinubu a wajen bikin buɗe babban taron kwastam na shekarar 2024, ranar Laraba, a Abuja.

    “Za mu fatattaki waɗanda ake kira Lukarawa daga kasarmu. Za mu kunyata masu sukar mu kuma zamu rufe bakunansu.

    "Boko Haram da suka addabi kasarmu a baya, yanzu tserewa suke yi. Yanzu haka mambobinta suna tafiya zuwa wasu ƙasashe makwabta saboda ba su da damar yin ta’addancinsu a Najeriya” inji shi.

    Ya kuma bayyana cewa, alamun na ƙara nuna cewa al’amura na cigaba da inganta ta fuskar tattalin arziki a ƙasar nan wanda kowa zai iya gani, inda ya ba da misali da yadda ake hako danyen mai a yankin Neja-Delta da kuma sauye-sauyen kasafin kudi da babban bankin Najeriya (CBN) ke yi a cikin irin wannan kokari.

    “Haƙar danyen mai ya kai ganga miliyan 1.8 a kowacce rana. sannan kuma an tsaftace babban bankin kasa, babu wanda ke ɗaukar kobo daga babban bankin.

    "Mun yi alƙawarin cewa za mu gyara kasar nan, kuma za mu yi hakan domin Shugaba Tinubu bai taɓa zama mutum mai gazawa ba,” inji Ribadu.

  7. Manomanmu sun yi asarar sama da naira miliyan 100 - Honarabil Birnin Gwari

    Dan majalisar tarayya mai wakiltar Birnin Gwari da Giwa Bashir Zubairu Birnin Gwari ya ce manoman yankin da yake wakilta sun yi asarar amfanin gonar da suka kai sama da naira miliyan biyo bayan harin da 'yan bindiga suka kai musu kan gonakinsu.

    A wata tattaunawa da ya yi da BBC Honarabil Bashir Zubairu ya ce a ranar Lahadi aka kai harin kan gonakin manoman da suka noma masara a garin Kwaga da Unguwar Zoko da ke birnin Gwari.

    Yace an ta yin sulhu da 'yan bindigar amma abin takaici sulhun baya karƙo, kuma gwamnati ta gaza shawo kan matsalar.

    Ya ce "akwai mutanen da suke yi mana zagon ƙasa kuma lokaci zai yi da za mu ambaci sunayensu.

    "Idan lokaci ya yi da mutanenmu ya kamata su ɗauki makamai domin kare kansu to za su yi hakan," in ji ɗan majalisan wanda ya bayyana hakan cikin fushi.

    Ya ƙara da cewa 'yan bindigar sun ce sun kawo harin ne saboda an kwace wa mutanensu bindiga da babura, kuma ba za su daina ba har sai an biya su kayan.

    "Mu waɗanda aka yi wa asara wa ya biya su, ko su ba mutane ba ne?

  8. Somaliland na gudanar da zaɓuka duk da rikicin da ya kanannaɗe yankin

    Ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a a jamhuriyar Somaliland wadda ke jin gashin kanta, inda kimanin masu kaɗa ƙuri'a miliyan 1.2 ne suka cancanci zaɓar shugaban ƙasa. ‘

    Ƴan takara uku ne ke fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa – shugaban ƙasa mai ci Muse Bihi Abdi na jam’iyyar Kulmiye da Abdirahman Mohamed Abdullahi wanda aka fi sani da Cirro na jam’iyyar Wadani da kuma Feisal Ali Waraabe na jam’iyyar UCID.

    Hukumar zaɓen ta ce akwai rumfunan zaɓe 2,637, waɗanda aka buɗe da sanyin safiyar ranara Laraba.

    Masu kaɗa ƙuri'a kuma za su zaɓi uku daga cikin sabbin ƙungiyoyin siyasa bakwai da za su zama jam'iyyun ƙasa a hukumance.

    A shekarar 1991 Somaliland ta ayyana ƴancin kai daga Somalia, amma ba a amince da ita a duniya ba.

    Tun da farko dai an shirya gudanar da zaɓen ne a shekarar 2022 amma aka ɗage saboda matsalolin gudanarwa da suka jiɓanci da kuɗi.

    Ana gudanar da zaɓen ne yayin da rikicin diflomasiyya da na soji suka yi wa yankin dabaibayi, wanda ya samo asali ne bayan da Somaliland ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ƙasar Habasha, inda ta ba ta hayar wani yanki mai nisan kilomita 20 a gaɓar tekun Aden don ta yi lamfani da shi don ayyukan soji da kuma gudanar da kasuwanci. inda ita kuma a na ta ɓangaren, an ce Habasha za ta amince da Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

  9. Za mu riƙa sayen mai daga Ɗangote kan naira 990 - IPMAN

    Ƙungiyar dillalan man fetur ta IPMAN a Najeriya, ta yi ƙarin bayanin dagane da matsayar da suka cimma da matatar mai ta Ɗangote kan farashin da za su ringa siyen man fetur daga wajensa.

    Kungiyar ta ce kamfanin Ɗangoten ya amince da siyar musu da man fetur ɗin kan Naira 990, yayin da kuma masu deport, su kuma zai ringa yasar musu da shi kan naira 940.

    To ko wannan na iya tasiri wajen samun saukin man fetur a Najeriya, ga tattaunawar Khalifa Shehu Dokaji da Abubakar Mai Gandi Sheetima, shugaban ƙungiyar dillalan ta kasa.

  10. Majalisar wakilan Najeriya na binciken NAHCON kan naira biliyan 90

    Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) da hukumar allhazai ta birninn tarayya, Abuja, ya nuna rashin jin ɗaɗinsa kan rashin daidaiton kuɗaɗen tallafin Naira biliyan 90 da aka bai wa alhazan Najeriya a lokacin aikin Hajjin 2024.

    Shugaban kwamitin, dan majalisar wakilai Sada Soli ya koka kan yadda hukumar ta tafiyar da tallafin na aikin ibada, inda ya yi zargin cewa wasu ayyuka da ta gudanar ba su taimaki kowa ba sai jami’an hukumar.

    A yayin sauraron batun, Sada Soli ya dage cewa shugaban hukumar NAHCON, Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana da kansa don amsa tambayoyin, aikin da tun farko ya mika wa kwamishinan Ayyuka, Prince Olarewaju Elegushi.

    Soli ya ƙalubalanci manufofin hukumar game da rabon tallafin, inda ya nuna cewa yayin da wasu alhazai ke samun cikakken tallafi ko wani ɓangare, wasu kuma ba su samu komai ba.

    "Yaya za ku bayar da cikakken tallafi, ko rabin tallafi, wasu kuma ba su sami komai ba -bayan dukansu ƴan Najeriya ne?" Soli ya tambaya.

    Kwamishinan ya yi bayanin cewa an cire wasu maniyyatan daga tallafin saboda rashin yin rijista a kan lokaci, amma Soli ya ci gaba da cewa ya kamata a yi adalci ga dukkan alhazan Najeriya.

    Ya ce aikin kwamitin shi ne tabbatar da ayyukan Hajjin da za a yi a nan gaba sun kasance cikin tsari da kuma aminci. “Muna magana ne g da yawun talakawan Najeriya da za su ajiye kudi na tsawon shekaru biyar, sai dai su fuskanci matsaloli saboda gazawar gudanarwa. Ya kamata ku yi abin da ya dace,” inji shi.

    Wani mamban kwamitin Mohammed Umar Bio, ya soki yadda hukumar ke tafiyar da aikin hajjin 2024, inda ya yi nuni da irin tallafin da gwamnati ke bayarwa da ya kai N90bn.

    "Duk da maƙudan kuɗaɗen da aka kashe, aikin NAHCON a wannan shekarar bai wadatar ba," in ji Bio,

  11. Yadda Trump ya isa fadar White House domin ganawa da Biden

    Donald Trump ya isa fadar White House don ganawarsa da Shugaba Biden.

    Shugabannin biyu za su tattauna a asirce a cikin ofishin shugaban ƙasa kan batun miƙa mulki da sauran batutuwa.

  12. An ƙi ba da belin shugabannin 'yan adawa a Mali

    Kotun ɗaukaka ƙara a Mali ta yi watsi da buƙatar neman beli daga shugabannin 'yan adawa 11 da aka kama a wata Yuni game da bijirewa haramcin da aka sanya wa jam'iyyun siyasa, kamar yadda gidan radiyon Faransa ya rawaito.

    Lauyoyin waɗanda ake tsare da su sun bayyana hukuncin a matsayin rashin adalci da kuma wani salon jan ƙafa ga abin da ba zai zama barazana ba ga al'umma.

    "An san inda suke zama kuma za a gindaya wasu sharuɗa kafin a ba da belin su. Ta ya ya za su ba d hujja kan ci gaba da riƙe su? Kwai wani salo ne na tsawaita azabtar da su da ake yi," kamar yadda lauya Ibrahim Marouf Sackoya bayyana.

    Waɗanda ake tsaren da su mambobi ne mambobin yarjejejniyar 31 ga watan Maris 2024 ne, da ke gamayyar ƙungiyoyin siyasa da suka riƙa kiran sjojin riƙon kwarya su mayar da mulki hannun farar hula ta hanyar zaɓe, bayan ƙarewar wa'adin da suka ɗauka na sauka daga iko. Cikinsu har da Yaya Sangare da Amadou Maiga.

    A watan Afrilun ne sojojin da suke mulki suka kafa wata dokar soji da ta dakatar da jam'iyyun siyasa har sai baba ta gani domin bin doka da oda.

  13. Trump zai gana da Shugaba Biden a Fadar Gwamnatin Amurka

    A yau ne shugaban Amurka mai barin-gado Joe Biden zai karɓi baƙuncin wanda zai gaje shi, Donald Trump a Fadar White House.

    Wannan wani mataki ne na girmama al'ada tsakanin shugabanni masu barin gado da masu jiran gado, wanda Mista Trump bai amince da Mista Biden ba lokacin da ya kayar da shi a zaɓen 2020.

    Wannan ne karon farko da shugabannin biyu za su yi tozali bayan zazzafar muhawarar da suka tafka a watan Yuni.

    Duk da cewar Biden ya bayyana Trump a matsayin barazana ga dimukuraɗiyyar Amurka, ya sha alwashin alwashin miƙa mulki cikin sauƙi da girmamawa.

    Mista Trump ya sanar da sababbin nade-naden gwamnatinsa da suka haɗa da attajiri Elon Musk wanda ya bayar da gudummawa yayin yaƙin neman zaɓen Trump.

  14. Shugaba Biden zai ƙara goyon bayan Ukraine a ragowar kwanakinsa - Blinken

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya ce Shugaba Biden na da niyyar amfani da sauran kwanakin da suka rage a wa'adin mulkinsa wajen inganta ƙawancen NATO da kuma goyon bayan Ukraine.

    Wasu shugabannin ƙasashen Yamma sun damu ƙwarai da makomar NATO sakamakon sake zaɓen Donald Trump.

    Mista Blinken ya ce, Shugaba Biden ya yi niyyar daidai ƙawancen wanda ke da muhimmanci ga tsaron Amurka da ƙasashen Turai.

    A wannan rana ce kuma aka buɗe sabon sansanin sojin saman Amurka a arewacin Poland kusa da gabar kogin Baltic.

    Rasha ta bayyana cewar ta dauki matakan kariya bayan ta bayyana sansanin a matsayin yunƙurin rage ƙarfin sojinta.

  15. Amurka ta ce tun da Isra'ila ta cika burinta a Gaza sai a kawo ƙarshen yaƙin

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce tun da Isra'ila ta cika burinta, a Gaza ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin.

    Blinken ya bayyana hakan ne a lokacin da ya nemi a ƙara lokacin tsagaita wuta a Gaza don kayan agaji su isa ga mutanen da suke buƙata.

    Ya yi wannan jawabi ne lokacin da Amurka ta ce za ta ci gaba da aika wa Isra'ila da taimakon soji.

    Gwamnatin Biden ta gamsu da cewar Isra'ila ba vta hana shigar da kayan agaji, don haka ba a karya dokar Amurka ba.

    To amma ƙungiyoyin agaji sun bayyana cewar Isra'ila ta yi watsi da wasu daga cikin umarnin da Amurka ta ba ta.

    Mista Blinken ya ce: ''Mun fara ganin yadda aka fara aiki da umarnin da muka bayar, za a ɗauki lokaci kafin a fara ganin tasirinsu.''

  16. Kotun Ƙolin India ta hana rushe gidajen waɗanda ake zargi da laifi

    Kotun Ƙolin Indiya ta hana rushe gidajen waɗanda aka zarga da aikata laifuka.

    Ƴan fafutuka sun bayyana cewar gidajen mabiya addinin Islama ake rushewa.

    A baya-bayan nan rusau ya zama ruwan dare a jihohin da mabiya addinin Hindu ƴan jam'iyyar BJP suke shugabanci.

    Kotun ta zartar da cewa jami'ai ba su da damar rusa gidaje ko shaguna saboda an zargi mutum da laifi.

    Masu suka sun ce rusa gidaje na haifar da rikicin addini ko tarzoma, batun da gwamnati ta ƙaryata

  17. Tashin hankali ya kankane yaƙin neman zaɓen majalisar dokokin Senegal

    Firaministan Senegal Ousmane Sonko ya janye barazanarsa ta mayar da kakkausan martani, tare da neman a zauna lafiya bayan da magoya bayan 'yam hamayya suka kai wa magoya bayansa hari yayin da ake tunkarar zaɓen majalisar dokokin ƙasar a ranar Asabar mai zuwa, 17 ga watannan na Nuwamba.

    A shekaran jiya Litinin ne, 11 ga wata Sonkoya zargi ministan cikin gida da sakaci su kuma hukumomin ƙasar da kin ɗaukar mataki bayan da aka kai hari kan tawagarsa a birnin Saint Louis na arewa maso tsakiyar ƙasar.

    A kan hakan ne ya yi kira ga magoya bayansa su ɗaura ɗamarar mayar da tsattsauran martani.

    Jagoran 'yan hamayya Barthelemy Dias ya ƙalubalanci firaministan da ya yi ramuwar ya ga abin da zai biyo baya da abin da ya fi wanda ya ga ni da farko.

    Ƴansanda sun ce an kama mutum 77 yawancinsu masu tsaron lafiyar 'yansiyasa, kuma an kama motoci bakwai a wani mataki da aka ɗauka na daƙile tashin hankalin na siyasa kafin zaɓen majalisar dokokin.

  18. Ƙungiyar RSF ta Sudan ta musanta sanya wa ƙauyawa guba

    Ƙungiyar mayaƙan RSF ta Sudan ta musanta tare da sukar sanarwar da wakilin musamman na Amurka a Sudan, Tom Perriello, ya fitar a kan cewa ƙungiyar ta sanya wa ɗaruruwan ƙauyawa guba a al-Hilaliya da ke jihar Gezira t tsakiyar ƙasar.

    A martanin da ta yi a shafinta na Telegram RSF, ta ce sanarwar ta jakadan na Amurka ta dogara ne ga 'yan taƙaitattun bayanai waɗanda kuma suka saɓa wa bayanan da jama'a farar hula daga yankin ke bayarwa.

    Sannan ƙungiyar ta danganta rashin lafiyar da ake fama da shi a yankin da ɓarkewar cutar kwalara, wadda ta ce ta shafi farar hula da ma mayaƙanta.

    Ƙungiyar ta ɗora alhaki a kan gwamnatin mulkin sojin ƙasar da hana shigar da kayan tallafi inda ta nemi wakilin na Amurka ya mayar da hankali wajen ganin an sauƙaƙa hanyoyin shigar da tallafi a yankunan da matsalar rashin lafiyar take.

    A ranar 11 ga watan nan na Nuwamba ne Perriello ya fitar da sanarwar a kan zargin mayaƙan RSF da sanya wa jama'a guba a jihar ta Gezira, inda ya bayyana hakan da cewa tsabar mugunta ce da ta saɓa wa hankali.

  19. Sojoji sun shirya yadda za a yi maganin mayaƙan Lakurawa - Badaru

    Hukumomin tsaron Najeriya sun ce sun kammala shirye-shiryen murƙushe 'yan ƙungiyar Lakurawa, masu iƙirarin jihadi da ke addabar jama'a a waɗansu jihohin arewa maso yammacin kasar.

    Hakan na zuwa ne bayan da 'yan ƙungiyar suka kai hari a makon daya wuce a jihar Kebbi inda suka hallaka mutum 15 tare da jikkata wasu da dama.

    Ministan tsaro na Najeriya, Muhammadu Badaru Abubakar ne ya bayyana ƙudurin rundunonin sojin ƙasar na tunkarar matsalar tsaron ta Lakurawa da ta kunno kai kwanannan, a hirarsa da BBC.

    Ministan ya ce manyan hafososhin tsaron Najeriya sun riga sun fitar da wani tsari na musamman da zai hana 'yan Lakurawan yin tasiri a arewacin kasar.

    Ya ƙara da cewa manyan hafsoshin rundunonin sojin ƙasa da na ruwa da na sama sun gana da hafsan hafsoshi, Janar Christopher Musa, inda suka yi masa bayani kan matakan da suka shirya ɗauka kan wannan ƙungiya.

    "Ni ma sun yi mani bayani kuma na gamsu da shirinsu. Idan Allah ya yarda za a samu nasara nan da ɗan lokaci ,'' in ji ministan.

  20. Trump ya naɗa Elon Musk shugaban ma'aikatar inganta aikin gwamnati

    Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, ya naɗa Elon Musk a matsayin shugaban sabuwar ma'aikatar inganta ayyukan gwamnati.

    Kwamatin yaƙin neman zaɓen Trump ya kuma sanar da Vivek Ramaswamy, mai zuba jari a harkokin fasaha, domin yin aiki tare da Musk a ma'aikatar ta Department of Government Efficiency (Doge).

    Sunanta ya yi kama da sunan kuɗin kirifto da Elon Musk ya fi so mai suna Dogecoin, kuma an ƙirƙire ta ne domin kawo ƙarshen wahalhalu a harkokin gwamnati.

    Mutanen biyu za su dinga bai wa fadar White House ƙarƙashin gwamnatin Trump shawara ne kan "yadda za a gudanar da manyan sauye-sauye," a cewar Trump.

    Tun da farko, Trump ya sanar da naɗa mai gabatar da shiri a tashar talabijin ta Fox, Pete Hegseth, domin ya zama sakataren tsaro, sannan ya John Ratcliffe shugaban hukumar leƙen asiri ta CIA.

    An daɗe ana sa ran Musk, wanda ya fi kowa kuɗi a duniya, zai shiga gwamnatin ta Trump bayan ya bai wa kwamatin yaƙin neman zaɓensa maƙudan kuɗaɗe.

    Ramaswamy ya nemi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Republican kafin daga baya ya janye kuma ya mara wa Trump baya.