Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Muktar Uba, Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Ronaldo ya sake zama kan gaba a jerin ƴanwasan da aka fi biya a duniya

    Cristiano Ronaldo ya sake zama kan gaba cikin jerin ƴanwasan da aka fi biya a duniya.

    Shekara uku a jere kenan ɗan wasan na Portugal na samaun wanann matsayi, da fitacciyar mujallar nan da ke ƙiyasin dukiya ta Fobes.

    Mujallar ta ce sau biyar Ronaldo yana samun matsayin a sana'arsa ta ƙwallon ƙafa, inda ta ƙiyasta kudin da aka biya ɗan wasan da kimanin dala miliyan 275.

    Adadi kudin da ɗan wasa ɗaya ne a tarihi ya taɓa zarta su, wato ɗan wasan dambe ne duniya, Floyd Mayweathe, wanda a 2015 a ysamu kimanin dala miliyan 300.

    A watan Disamban 2022, Ronaldo mai shekara 40 ya koma ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya a wani ciniki mai gwaɓin gaske.

    Mujallar ta ce ɗan wasan ya samu kuɗi sakamakon wasu tsarabe-tsarebe da yarjejeniyarsa ta ƙunsa da kuma wasu tallace-tallace da kuma yawan mabiya a shafukansa na sada zumunta, da a yanzu suka kai miliyan 939.

    Ƴanwasa 10 da aka bi biya a duniya a 2025

    • Cristiano Ronaldo, ƙwallon ƙafa dala miliyan 275
    • Stephen Curry, ƙwallon kwando, dala miliyan 156m
    • Tyson Fury, wasan dambe dala miliyan 146
    • Dak Prescott, ƙwallon ƙafa dala miliyan 137
    • Lionel Messi, ƙwallon ƙafa dala miliyan 135
    • LeBron James, ƙwallon kwando dala miliyan 133.8
    • Juan Soto, kwallon baseball dala miliyan 114
    • Karim Benzema, ƙwallon ƙafa dala miliyan 104
    • Shohei Ohtani, ƙwallon baseball dala miliyan 102.5
    • Kevin Durant, ƙwallon kwando dala miliyan 101.4
  2. Fiye da mutum 50 sun mutu bayan Isra'ila ta zafafa hare-hare a Gaza

    Aƙalla mutum 50 ne aka ruwaito sun mutu a Gaza sakamakon ci gaba da hare-haren jiragen saman Isra’ila da dare, in ji hukumar agajin gaggawa ta Hamas.

    Wannan na zuwa ne bayan mutuwar fiye da mutum 120 a yankin a jjiya, ranar Alhamis.

    Halin da ake ciki na jin kai a Gaza na ci gaba da taɓarɓarewa, yayin da Isra’ila ke ci gaba da hana shigar abinci da magunguna da sauran kayan agaji tun daga tsakiyar watan Maris.

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana damuwarsa kan yadda halin jin ƙai ke kara tsananta a Gaza. Ya ce gwamnatin Trump “na cikin damuwa” kan halin da ake ciki.

    Wannan ya sha banban da yadda yake mayar da martani a baya, inda sau da yawa yake kiran ƙungiyar Hamas da ta mika wuya maimakon bayyana damuwa game da rayukan fararen hula na Falasɗinu.

  3. Hauhawar farashi ya zarta kashi 30 cikin 100 a Abuja da wasu jihohi 10

    Duk da cewa hukumar ƙididdiga ta Najeriya - NBS ta fitar da rahoton saukar hauhawar farashin kaya a Najeriya, jihohi goma tare da babban birnin Tarayya, Abuja na ci gaba da fama da hauhawar farashi da ya haura kashi 30 cikin 100.

    Wannan na nuna alamar cewa matsin tattalin arziki na ci gaba da gallaza wa al'umma a wasu sassan ƙasar.

    Rahoton hauhawar farashi na wata-wata ya nuna cewa a watan Afrilun 2025 hauhawar farashi ya sauka zuwa kashi 23.71 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris da kuma kashi 33.69 cikin 100 a watan Afrilu na bara.

    Sai dai duk da saukar farashin a matakin ƙasa, jihohin Enugu da Kebbi da Neja da Benue da Ekiti da Nassarawa da Zamfara da Delta da Gombe da Sokoto da kuma Abuja har yanzu suna fuskantar hauhawar farashi kayayyaki.

    Jihar da ta fi fuskantar hauhawar farashi mafi muni ita ce Enugu inda ya kai kashi 36.0 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

    Na Kebbi da Niger ya kai kashi 35.1 da 34.8 cikin 100 bi da bi.

    Farashin abinci na ci gaba da ƙara tsananta rayuwar jama'a a waɗannan jihohi.

    A Jihar Benue, hauhawar farashin abinci ya kai kashi 51.8 cikin 100 idan aka kwatanta da bara, tare da ƙarin kashi 25.6 cikin 100 a cikin wata guda.

    Wannan na da nasaba da rashin tsaro da ke kawo cikas ga noman abinci in ji rahoton.

  4. Trump na son ganawa da Putin da zarar ya shirya hakan

    Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna sha’awarsa ta gana da shugaban Rasha Vladimir Putin da zarar ya shirya hakan don ci gaba da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.

    A yayin ranar ƙarshe ta ziyararsa a Gabas ta Tsakiya, a wani taron majalisar kasuwanci a Hadaddiyar Daular Larabawa, Trump ya ce, "lokaci ya yi da za mu fara aiwatar da tattaunawar zamann lafiyar nan kuma za mu samu nasara."

    Ya jaddada cewa ba za a samu ci gaba mai ma’ana a tattaunawar zaman lafiyan ba sai an yi ganawar fuska da fuska da Putin.

    Maganganun Trump na nuna fatan cewa ganawar kai tsaye zai taimaka wajen tura tattaunawar gaba.

  5. An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Plateau

    Aƙalla mutum 10 ne aka kashe tare da sace shanu a wani sabon rikici da ya ɓarke a yankin ƙaramar hukumar Riyom a jihar Plateau.

    Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata amfanin gona da sace shanu da kashe wasu dabbobin, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels a ƙasar ya ruwaito.

    Cikin wata sanarwa da rundunar soji ta 'Operation Safe Haven' ta fitar ta ce rikicin ya fara ne tun a ranar Litinin 12 ga watan Mayun da muke ciki, a lokacin da aka zargi wasu fusatattun matasa da kashe wasu shanu da suka yi zargin sun shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan da ke ƙaramar hukumar ta Riyom.

    A ranar 13 ga watan ne kuma aka zargi wasu makiyaya da kai hari ƙauyen Danchindo domin ramuwar gayya, tare da kashe mutum huɗu kafin su tsare bayan zuwan jami'an tsaro.

    Haka kuma a ranar 14 aka zargi wasu mahara da kashe dabbobi 26 tare da raunata wasu a garin Darwat.

    Daga baya kuma aka zargi wasu makiyaya da kai hari ƙauyen Wereng Kam tare da kashe mutum shida.

  6. Red Cross ta ce ta kwashe jami'an tsaron DR Kongo fiye da 300 daga Goma

    Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta kwashe sojojin gwamnatin Kongo da ƴansanda fiye da 300 daga birnin Goma da ke gabashin ƙasar cikin tsawon mako biyu.

    Birnin Goma ya faɗa hannun ƙungiyar 'yan tawayen ta M23 da ke samun goyon bayan Rwanda a watan Janairu bayan wani ƙazamin faɗa.

    Majiyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun ce kusan sojoji da ƴansanda dubu biyu ne suka nemi mafaka a sansanonin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD.

  7. Za mu ci gaba da karya farashin shinkafa - BUA

    Shugaban rukunin kamfanonin kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta sake rage farashin shinkafa da sauran kayan abinci, wanda ya ce tun shekarar da ta gabata yake ta sauka.

    Abdul Samad Rabiu ya bayyana haka ne ranar Alhamis jim kaɗan bayan ganawarsa ta Tinubu a fadar shugaban ƙasar.

    Shugaban na BUA ya yaba wa Tinubu kan bayara da damar shigo da wasu kayan abinci da ya yi, yana mai bayyana matakin da 'kyakkyawa'' da ya ce ya taimaka wajen karyewar farashin kayan abinci a ƙasar.

    A watan Yulin 2024 ne gwamnatin Shugaba Tinubu ta bayayna dakatar da karɓar kudin fito na shigo da kayan abinci a wani mataki na magance hauwarar farashin kayayyaki.

    BUA ya zargi masu sayen kayyaki domin ɓoyewa da haddasa tashin farashin.

    Ya ce da zarar lokacin girbe amfanin gona ya yi, sai wasu su riƙa sayen kayan suna ɓoyewa, har tsawo wata uku, daga baya kuma su fito da kayan su tsawwala farashi domin sayarwa kamfanonin sarrafa abinci .

    To sai dai ya ce bayan matakin shugaban ƙasar, kamfanonin sarrrafa shinkafa sun shigo da wadataccen kaya, lamarin da ya sa dole masu ɓoye kayan suka fito da nasu suna sayarwa a farashi mai sauƙi.

    ''Wannan shi ne abin muka yi, kuma za mu ci gaba da yin haka domin mara wa matakin gwamnati baya na tabbatar da farashin abinci ya sauka, kuma na tabbata farashin zai ci gaba da sauka''.

    Kalaman BUA na zuwa ne a daidai lokacin da rahoton hukumar Ƙididdiga na ƙasa NBS ke nuna cewa an samu raguwar farashin kayyaki a ƙasar a watan Afilu idan aka kwatanta da watan Maris da ya gabata.

  8. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, Hajji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza da Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kada ku manta da shafukanmu da sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.