Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Muktar Uba, Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    A nan muka ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye daga nan sashen Hausa na BBC.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta yi Allah wadai da 'yanke hukuncin kisa ba tare da shari'a ba' a Mali

    Mali

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta ƙasa da ƙasa ta yi Allah wadai da abin da ta kira yanke hukuncin kisa ba tare da an gudanar da shari'a ba kan wasu mutane sama da ashirin da sojoji suka yi a ƙasar Mali.

    Ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan yanayin mutuwar mutanen.

    Mutanen waɗanda dukkansu ƴan kabilar Fulani ne, an tsare su ne a ranar Litinin a ƙauyen Diafarabé da ke gaɓar kogin Neja inda aka zarge su da zama ƴaƴan ƙungiyoyi masu ikirarin jihadi.

    Gano gawarwakinsu da aka yi a wani tsibiri ya haifar da mummunar zanga-zanga wanda mata da ƙananan yara ne suka jagoranta.

  3. Gwamnatin Sokoto ta ƙuduri aniyar yaƙi da sha da fataucin kayan maye

    Sokoto

    Asalin hoton, Abubakar Bawa

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya nanata ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar hana sha da fataucin kayan maye a faɗin jihar.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen bikin ƙaddamar da sake buɗe Masallacin Juma'a na Shagari, wanda gwamnatin ta sabunta, inda ya ce aikin Hisbah na jihar na ƙwace kwalaban giya da lalata su a na cikin ƙoƙarin gwamnatin na yaƙi da baɗala a jihar.

    "Ina yabawa da ƙoƙarin ƴan Hisbah bisa ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da ayyukan assha a cikin al'umarmu," in ji gwamnan, kamar yadda kakakinsa, Abubakar Bawa ya bayyana a wata sanarwa.

    Ya nanata cewa Hisbah za ta cigaba da aikinta, amma ya ce za ta riƙa amfani da doka da oda musamman na kare ƴancin ɗan'adam.

    A game da masallatan Juma'a, gwamnan ya ce yanzu haka suna sabunta masallatan Juma'a guda 63 a ɓangarori da dama na jihar.

    Ya ce masallatan Juma'a suna samun kason wata-wata daga gwamnati, sannan limamai da na'ibansu da ladanai suna samun alawus na wata-wata daga gwamnatin jiha.

    A nasa ɓangaren, Mai alfarma Sarkin Musulmi, wanda Farfesa Sambo Wali Junaid ya wakilta, ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin, inda ya bayyana sabunta masallatan a matsayin aiki mai kyau.

  4. Yaƙi da ta'addanci na kowa ne - Babban hafsan tsaron Najeriya

    Musa

    Asalin hoton, X/Defence Headquarters

    A Najeriya shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro inda suka tattauna a kan matsalolin tsaron da ma matakan da ake shirin ɗauka domin magance su.

    An dai gudanar da taron ne a fadar shugaban Najeriyar da ke Abuja, daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar sabbin hare-haren mayaƙan Boko Haram da ISWAP a shiyar arewa maso gabas da kuma na ƴan bindiga yankunan arewa maso yamma da sauransu.

    Haka kuma an gudanar da taron ne bayan matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka kwanan nan na kafa wata runduna ta musamman da ake kira Forest Guards da za su yi aikin karaɗe dazuka har 1,129 da ake da su a faɗin Najeriya domin yaƙi da ƴanbindiga.

    Bayan kammala taron ne hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi wa manema ƙarin bayani daga cikin abubuwan da suka tattauna, inda ya ce aikin samar da tsaro ba na dakarun sojoji ba ne kaɗai ba, sannan ya ce ya wajaba al’umma su fahimci faɗa ne da ya game kowa."

  5. Kan ƴan Houthi muka yi luguden wuta a Yemen - Isra'ila

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta ce ta kai hare-hare a kan waɗanda ta ce ƴan Houthi ne a gaɓar Hodeidah da Salif da ke Yemen.

    Ma'aikatar tsaron ƙasar ta fitar da wasu hotunan Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da wasu manyan sojojin ƙasar a sansanin sojin saman ƙasar.

    A farkon makon nan ne sojojin Isra'ila suka fitar da sanarwar gargaɗi ga mutane cewa su kwashe kayayyakinsu su ƙaurace wa yankin Hodeidah da Saif da wata gaɓar tekun ta Ras Isa.

    Ƴan Houthi dai suna cigaba da kai hare-hare domin cimma Isra'ila duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙasar da ta shiga da Amurka.

  6. Mata sun yi zanga-zangar adawa da wariyar jinsi a Bangladesh

    Ɗaruruwan mata sun gudanar da wani gagarumin gangami a Dhaka babban birnin ƙasar Bangladesh domin nuna goyon bayansu ga kwamitin da gwamnati ta kafa domin magance matsalar wariyar jinsi.

    Hukumar kula da harkokin mata ta bayar da shawarwarin da suka haɗa da ƙara yawan kujerun ‘yan majalisa da mata ke riƙe da su da kuma bai wa mata cikakken haƙƙin gado.

    Jam'iyyu masu kishin addinin musulunci sun yi kira da a soke hukumar, suna masu cewa sauye-sauyen da take neman kawowa sun saɓa wa dokokin addini.

    Mata masu fafutuka sun ce sun ga yadda ake nuna musu ƙyama da wariya tun lokacin da suka nuna goyon bayansu ga sauye-sauyen da hukumar ta gabatar.

  7. Bankin Duniya zai koma aiki a Syria

    Syria

    Asalin hoton, Reuters

    Bankin Duniya ya ce zai koma aiki a ƙasar Syria bayan ƙasashen Qatar da Saudiyya sun biya basussukan da yake bin ƙasar.

    Bankin na duniya ya daina aiki a ƙasar Syria ne tun bayan da yaƙin basasa ya ɓarke a ƙasar a shekarar 2011.

    A wata sanarwa da bankin ya fitar, bankin ya ce yanzu Syria, "ta kama hanyar gyaruwa da komawa daidai."

    Bankin ya ce aikinsa na farko a ƙasar zai fi mayar da hankali ne kan inganta wutar lantarki a ƙasar.

    Ana ganin dai wannan matakin na bankin duniya a matsayin wani mataki da zai ƙarfafa gwamnatin Ahmed al-Shara, wanda ya zo bayan shugaban ƙasar ya gana da Shugaban Amurka Donald Trump a Saudiyya, inda Trump ya sanar da cewa zai cire wa Syria takunkumi.

  8. An gano birrai na amfani da tsirrai domin 'agajin gaggawa'

    WCS

    Asalin hoton, WCS

    An lura cewa birai a Uganda suna amfani da tsire-tsire daga ganyayyaki da itatuwa don magance raunukan da suka samu; alamun da suka nuna cewa suna ba wa kansu agajin gaggawa, a wasu lokuta.

    Masana kimiyya daga Jami'ar Oxford, sun shafe shekaru suna bin rukuni biyu na birran, tare da tattara halayen dabbobin daki-daki.

    Masu bincike sun yi amfani da na’urori waɗanda suka maƙalƙala a jikin dabbobin, ciki har da goggon biri, kuma sun gano yadda waɗannan halittun ke amfani da tsirrai ta hanyoyi daban-daban wajen magance raunukan da suka samu a cikin daji.

  9. Aƙalla mutum biyu ne suka kamu da kyandar biri a Ghana

    Kyandar biri

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar Lafiya ta ƙasar Ghana ta tabbatar da samun aƙalla mutum 2 da suka harbu da cutar kyandar biri wato Monkey PoX a ƙasar.

    Yanzu haka dai hukumomin lafiyar ƙasar sun ce sun duƙufa wajen gano duk mutanen da ake zargin sun yi mu'amala ko sun cuɗanya da waɗanda suka harbu.

    Ana dai nemasu ne domin a killace su domin daƙile bazuwar cutar.

  10. An ɗaure wanda ya kai wa Salman Rushdie hari shekara 25 a gidan yari

    Salman Rushdie

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau Juma'a ne wata kotu ta ɗaure wanda da ya daɓa wa fitaccen marubuci Sir Salman Rushdie - wanda ya yi ɓatanci da Annabi Muhammad a wani littafin da ya rubuta - wuƙa a wani taro a birnin New York zaman shekara 25 a gidan yari.

    An ɗaure wanda ake zargin, Hadi Matar mai shekara 27 ne bisa zarginsa da yunƙurin kisa da ya aikata a farkon wannan shekarar.

    An kai harin ne kan Salman a lokacin da yake jawabi a watan Agustan 2022, inda da aka caccaka masa wuƙa a fuska da wuya. Harin ya yi sanadiyar makancewar idonsa guda ɗaya, sannan hannunsa ɗaya ya shanye.

    An kai wa Salman harin ne kimanin shekara 35 bayan ya fitar da littafansa mai suna 'The Satanic Verses' wanda ya tayar da ƙura, har aka fara yi wa rayuwarsa barazana saboda yadda ya kwatanta Annabi Muhammad a ciki.

    Haka kuma an yanke wa Matar hukuncin shekara bakwai da ɗoriyar shekara uku kan raunata wanda yake tattaunawa da Salman, Henry Reese.

    Sai dai zai gudanar da zaman gidan yarin ne a tare saboda dukkan mutanen sun ji raunin a lokaci guda, kamar yadda alƙalin kotun gundumar Chautauqua County, mai shari'a Jason Schmidt ya bayyana a ranar Juma'a.

  11. Za mu yi abin da ya kamata kan hana shigar da abinci Gaza - Trump

    UAE

    Asalin hoton, Getty Images

    A daidai lokacin da yake ƙarƙare rangadin da yake yi a ƙasashen yankin Gulf, shugaba Trump ya ce akwai mutanen Gaza da dama da ke fama da yunwa saboda haka Amurka za ta duba yanayin tare da yin duk abin da ya dace a yankin.

    Mr Trump bai bayar da cikakken bayani a kan abin da Amurkar za ta yi ba a yayin da yake jawabi a Hadaddiyar Daular Larabawa, inda suka sanya hannu kan yarjejeniyar gina katafariyar cibiyar nazarin kirkirarriyar basira ta AI a wajen Amurka.

    Yarjejeniyar da suka ƙulla na daga cikin yarjejeniyoyin da shugaba Trump ya sanya hannu a ziyara da suka kai Gabas tsakiya.

    Cibiyar za ta ƙara tasirin da kamfanonin fasahar Amurka ke da su a duniya.

  12. Wakilan Rasha da Ukraine sun fara tattaunawa a Istanbul

    Turkey

    Asalin hoton, Getty Images

    Wakilan Rasha da Ukraine sun fara tattaunawa a birnin Istanbul na Turkiyya irinta ta farko a tsakanin ƙasashen.

    Akwai rahotannin da ke cewa ba a kai ga cimma yarjejeniya ba, sannan kuma ba a sa ran samun wani cigaba mai ma'ana ba.

    Ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana cewa " wannan tattaunawa ita ce irinta ta farko tsakanin ɓangarorin biyu da ke rikici da juna tun 2022. Dole mu yi amfani da wannan dama domin ganin an samu cigaba wajen samun zaman lafiya."

    Rasha ta tura wata ƙaramar tawaga bayan Mista Putin ya yanke shawarar ƙin halartar tattaunawar.

    Shugaba Trump ya sake nanata cewa zai shirya ganawa da shugaban na Rasha nan da bada jimawa ba.

  13. Ƴan majalisar Najeriya na son tilasta ƴan ƙasar yin zaɓe

    NASS

    Asalin hoton, NASS

    A Najeriya ‘yan majalisar dokokin ƙasar sun sake zama inda suka yi karatu na biyu ga ƙudurin dokar nan da ke neman yin gyaran fuska ga dokar zaɓe ta 2022 da za ta tilasta ‘yan ƙasar jefa ƙuri’a a lokacin manya da ƙananan zaɓuka masu zuwa.

    Wannan sabon ƙudurin doka dai ya janyo rarrabuwar kai a majalisar dokokin Najeriyar.

    Yayin da wasu ƴan majalisar ke ganin zai zama tamkar take ‘yancin ‘yan ƙasar ne, wasu kuwa na bayyana shi a matsayin mataki mai kyau, wanda idan ya zama doka za a iya cin tara ko kuma yanke masa hukuncin zaman gidan kaso duk wanda ya ƙi yin zaɓe.

    ‘Yan majalisar dokokin sun gudanar da muhawara tare da tattaunawa game da shirin yin gyaran fuska ga dokar shekarar 2022 da ta shafi zabe domin tabbatar da kowane dan Najeriya ya sauke nauyin da ke kansa na yin zabe.

    Sun bayyana cewa akwai bukatar cin tarar naira dubu 100 ga duk wanda ya ki jefa kuri’a ko kuma dauri a gidan yari nana tsawon watanni shidda ko ma duka biyu.

    ‘Ƴan majalisar dai sun kai ga yi wa kudurin karatu na farko da na biyu, da kakakin majalisar wakilan kasar Tajudeen Abbas ya jagoranci zaman.

  14. 'Sojoji sun kama tsohon firaiministan Chadi Success Masra'

    Masra

    Asalin hoton, Getty Images

    Jam'iyyar tsohon firaiministan Chadi Success Masra, ta ce sojoji sun kama shi a yau Jumma'a.

    Jam'iyyar ta wallafa wasu hotuna a shafin sada zumunta wanda suka nuna yadda jami'an sojojin suka shiga harabar gidan jagoran 'yan adawar da ke N djamena, babban birnin kasar.

    Kamen nasa ya zo ne makonni bayan Mista Masra ya zargi shugaban ƙasar Mahamat Idriss Deby, da gaza martaba yarjejeniyar da aka cimma watanni 18 da suka wuce.

    Yarjejeniyar za ta ba wa Mista Masra damar komawa daga gudun hijirar da yake a Amurka.

    A watan Janairun 2024 ya karɓi muƙamin firaiminista amma daga baya suka shiga 'yar tsama inda a nan ne aka yi watsi da batun muƙamin nasa sannan aka ƙwace fasfonsa.

  15. 'Kusan mutum 100 ne suka mutu a ƙasa da sa’o’i 12 a Gaza'

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Wani mai magana da yawun hukumar kare rayuka ta Hamas a Gaza, Mahmoud Basal, ya ce mutanen da suke rasa rayukansu ya haura zuwa kusa da mutum 100 sakamakon hare-haren Isra’ila a arewacin Gaza cikin ƙasa da sa’o’i 12.

    A wani sakon da ya wallafa a Telegram, Basal ya bayyana halin da ake ciki a arewacin Gaza a matsayin “rana mai jini da wahala.”

    Isra’ila dai ta sha alwashin ƙara ƙaimi a hare-harenta a Gaza tare da sake mamaye dukkan yankin muddin Hamas ba ta amince da tayin tsagaita wuta na ɗan lokaci da kuma sako sauran fursunoni kafin karshen ziyarar shugaban Amurka Donald Trump a yankin ba.

  16. An saki tsohon shugaban Gabon da iyalansa bayan shekara biyu a tsare

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An saki tsohon Shugaba Gabon, Ali Bongo tare da matarsa Sylvia da ɗansa Noureddin bayan kwashe kusan shekara biyu a tsare inda a halin yanzu sun bar ƙasar zuwa Angola

    Iyalan dai sun fuskanci tuhuma kan cin hanci da rashawa tun bayan kifar da gwamnatin Bongo a juyin mulki na shekarar 2023.

    Fadar shugaban Angola ta tabbatar da isowarsu birnin Luanda, gurin suka koma bayan wata ganawa tsakanin shugaban Angola João Lourenço da sabon shugaban Gabon, Brice Oligui Nguema.

    Har yanzu ba a bayyana ko shari’ar da ake yi wa Sylvia da ɗanta za ta ci gaba ba.

    Ali Bongo ya jagoranci Gabon na tsawon shekaru 14 bayan mahaifinsa, Omar Bongo, wanda ya mulki ƙasar sama da shekaru 40.

    Duk da arzikin man fetur a ƙasar, kashi ɗaya bisa uku na al’ummar Gabon na rayuwa cikin talauci, lamarin da ya janyo suka kan dangin Bongo da zargin amfani da dukiyar ƙasa don amfanin kansu—zarge-zargen da suka musanta.

  17. Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon fafaroma

    ...

    Asalin hoton, Tinubu/X

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon fafaroma, Leo XIV da za a gudanar a birnin Rome na asar Italiya.

    Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce Tinubu zai tafi Rome a ranar Asabar domin halartar bikin, bisa gayyatar da sabon fafarman ya aike masa.

    Sanarwar ta ce Tinubu zai yi bulaguron ne tare da manyan jagororin ɗariar Katolika na Najeriya domin shaida bikin rantsar da sabon fafaroman wanda shi ne na 267.

    Fadar shugaban ƙasar ta ce cikin takardar gayyatar sabon fafaroman ya bayyana alaƙar ƙashin kai da Najeriya, yana mai cewa ''ƙasarka mai girma na da mutuƙar muhimmanci a gareni, saboda na yi aiki a majami'ar Apostolic Nunciature da ke birnin Lagos a shekarun 1980''.

  18. An kama aƙalla mutum 82 a rikicin ƙabilanci a Chadi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni na cewa an kama mutane 82 a kasar Chadi a ci gaba da wani bincike da ake gudanarwa bayan kashe mutane 35 a wani rikici a kudu maso yammacin kasae.

    A ranar laraba ne rikici ya barke a kauyen Mandakoa da ke kusa da iyakar kamaru.

    Har yanzu ba a san ainihin abin da ya janyo tashin hankalin ba, amma an soma gudanar da bincike kan hakan.

    Gwamnati ta ce irin wannan rikicin da aka saba yi a kasar na da alaka da jayyaya kan filayen noma.

    Rikicin manoma da makiyaya a kasar Chadi ya dade yana ci wa gwamnati tuwa a kwarya, kuma so tari ana samun hasarar rayuka a irin wadannan rikice-rikicen wanda aka gada tun iyaye da kakanni.

    Hukumomin tsaro a Chadi sun ce a yanzu haka sun tura Karin jami’an tsaro a yankin sannan kuma sun sha alwashin daukar matakan kawo karshen zubar da jini.

    A ranar Alhamis, ministocin tsaro da kuma na kula da al’amuran gwamnati sun ziyarci wuraren da aka yi rikicin inda suka bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu.

  19. Ana tafka muhawara kan ƙudirin taimaka wa marasa lafiya su mutu a Birtaniya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan majalisar dokoki a Birtaniya na ci gaba da muhawara kan ƙudirin doka da ke neman halasta taimaka wa marasa lafiya su mutu a Ingila da Wales – karon farko tun bayan da aka yi muhimman sauye-sauye a cikinsa.

    Ƙudirin ya samu amincewa a matakin farko a Majalisar dokokin ƙasar a watan Nuwamba da ya gabata – amma tun daga lokacin, an duba cikakkun bayanansa sosai tare da ƙara gyare-gyare da dama daga ɓangarorin biyu.

    Ba a sa ran kaɗa ƙuri’ar amincewa ko ƙin amincewa da kudirin a yau Juma’a, sai dai ana tsammanin hakan zai faru a watan Yuni.

    Muhawarar farko ta samu cikas a zauren majalisar, inda wasu ƴanmajalisar ke nuna damuwa game da rawar da likitoci za su taka wajen taimaka wa mara lafiya ya mutu, da kuma yiwuwar matsin lamba ga wasu da za su iya jin dole su kawo ƙarshen rayuwarsu.

    A lokacin da take gabatar da ƙudirin, Kim Leadbeater, ‘yar majalisar Labour da ke goyon bayan kuɗirin, ta ce an “ƙara ƙarfi” ga ƙudirin, kuma ya kamata a yi la’akari da sauyin da kulawa ta musamman.

    Ta ce mutane da dama sun “rasa masoyansu a cikin mawuyacin hali mai cike da raɗaɗi da tashin hankali.”

    Amma ‘yar majalisar Conservative, Rebecca Paul, ta ce ba ta goyon bayan ƙudirin, tana mai cewa kamata ya yi a maida hankali wajen inganta kulawa ga mara lafiya maimakon taimaka wa mara lafiya ya mutu.

  20. Ba ma fatan Najeriya ta zama ƙasa mai bin tafarkin jam'iyya ɗaya - APC

    ....

    Asalin hoton, Tinubu/X

    Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Felix Morka, ya bayyana cewa duk da ƙaruwar mutane da ke sauya sheka zuwa jam’iyyar, jam’iyyar mai mulki ba ta da niyyar mayar da Najeriya ƙasa mai jam'iyya ɗaya tak.

    Ya bayyana cewa a lokacin da Jam’iyyar PDP, ke mulki, ta rike fiye da jihohi 28 ba ba a zarge ta da ƙoƙarin mayar da ƙasar ta zama ƙasa mai jam'iyya ɗaya ba.

    Morka ya ce babu wani laifi ga mambobin jam'iyyun PDP da LP da ke sauya sheka zuwa APC idan suna son su haɗa kai da tsarin jam’iyyar mai mulki.

    Ya ce, “Da yawa daga cikin waɗannan mutane na shigowa a cewarsu don zama a ɓangaren da ke kan tsari.

    “A ƙasar mu, duka a cikin ƙundin tsari dokar zaɓe, da kuma sauran dokoki da dama, akwai tsarin da ya tabbatar da cewa Najeriya ƙasa ce mai jam’iyyun siyasa da dama kuma al’umma ce mai ra’ayoyi daban-daban."

    "Don haka, ba za mu iya ba a matsayin jam’iyya muyi abin da zai saɓa wa tsarin mulkin ƙasa ba, ta hanyar mayar da ƙasar ma jam'iyya ɗaya.