Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/07/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/07/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir da Aisha Babangida

  1. Dole ne Tinubu ya kawo ƙarshen zubar da jini a Zamfara - Amnesty

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu

    Ƙungiyar kare hakkin bila'adama ta Amnesty International ta ce ya zama "wajibi" shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar an kawo ƙarshen kashe-kashen mutane da ke faruwa a jihar ta Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    Amnesty ta faɗi hakan ne a wani martani da ta mayar bayan kisan da ƴan bindiga suka yi wa mutane aƙalla 38 da suke garkuwa da su kisan gilla a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda da ke jihar ta Zamfara.

    Sanarwar da Amnesty ta fitar a shafinta na X, ta ce "babu wani yanki na Zamfara da ke cikin aminci tun daga shekarar 2018.

    "A cikin shekara biyu da suka gabata an kashe sama da mutum 273 da yin garkuwa da mutane 467," in ji sanarwar.

    "Hukumomin Najeriya na da nauyin da ya rataya a kansu bisa dokokin ƙasa da na duniya, na kare dukkanin al'umma ba tare da nuna bambanci ba," in ji sanarwar.

    Zamfara na daga cikin jihohin Najeriya waɗanda suka shafe tsawon shekaru suna fama da matsalar ƴan fashin daji masu kisa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

    A lokuta daban-daban hukumomin Najeriya sun yi iƙirarin kashe manyan jagorori ƴan bindiga da ke jihar, sai dai kashe-kashen na baya-bayan nan na nuna cewa akwai sauran rina a kaba.

    A tattaunawarsa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, Manniru Haidara Ƙaura ya ce yawancin waɗanda aka kashen matasa ne.

    "Bayanin da muka samu shi ne sun yi musu yankan rago ne. Abin da ya faru shi ne ƴanbindigar sun nemi kuɗin fansa kuma aka harhaɗa aka ba su kamar yadda suka nema, inda kuma suka saki mutum 18 da suka haɗa da mata 17 da ƙaramin yaro guda ɗaya, a ranar Asabar,"in ji Haidara.

  2. Akwai yunwa ta gaske a Gaza - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce "akwai yunwa ta gaske" a Gaza.

    Shugaban na Amurka ya faɗi hakan ne bayan Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yanace kan cewa babu yunwa a yankin.

    Lokacin da aka tambaye shi ko ya yadda da abin da Netanyahu ya fada cewar "ƙarya ce tsagwaronta" idan aka ce Isra'ila na ta'azzara yunwa a Gaza, shugaban na Amurka ya ce: "Ban sani ba...amma yaran nan da ka gan su, suna cikin yunwa...wannan yunwa ce ta gaske."

    Lokacin da ya yi magana sa'ilin da ya gana da Firaiministan Birtaniya Keir Starmer, Trump ya ce: "Babu wanda ya yi abin a zo a gani a can. Gaba ɗaya wurin ya lalace...Na faɗa wa Isra'ila cewa ƙila ya kamata su sauya salo."

    Kalaman Trump na zuwa ne bayan shugaban hukumar kai agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana buƙatar abinci mai "ɗimbin yawa" domin magance halin yunwa da yankin ke ciki.

  3. Tinubu ya yi wa ƴanmatan Najeriya da suka lashe kofi ruwan miliyoyi

    Tawagar Super Falcons da suka lashe kofin mata na Afirka a ranar Asabar

    Asalin hoton, X/CAFonline

    Bayanan hoto, Tawagar Super Falcons da suka lashe kofin mata na Afirka a ranar Asabar

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bai wa ƴan wasan tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar 24 - Super Falcons - tukwicin kuɗi dala 100,000 kowanne, kimanin naira miliyan 153.

    Haka nan ya bai wa kowa daga cikinsu kyautar gida mai ɗaki uku, yayin da ya bai wa tawagar masu horas da su kyautar dala 50,000.

    Tinubu ya sanar da hakan ne a yau Litinin sa'ilin da ya tarbi tawagar matan bayan nasarar da suka samu ta lashe kofin ƙwallon ƙafa na Afirka karo na 10.

    A ranar Asabar ne Super Falcons suka lallasa Atlas Lionesses na Morocco da ci uku da biyu a wasan ƙarshe na gasar cin kofin da Moroccon ta karbi baƙunci.

    Baya ga kyautar kuɗi da gida, Tinubu ya kuma karrama ƴan wasan da lambar girmamawa ta ƙasa ta OON.

    Haka nan kuma ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta bai wa tawagar ta Super Falcons kyautar kudi naira miliyan 10.

    Bayanan bidiyo, Kalli yadda Super Falcons suka koma Abuja bayan lashe kofi

    A lokacin da yake jawabi, Tinubu ya ce: "Na karɓi wannan kofi a madadin ƴan Najeriya, kuma zan ce muku: mun gode da wannan ƙwazo, saboda haka na karrama ƴan wasan da masu horas da su 11 da lamabar girmamawa ta Officer of the Order of the Niger (OON).

    "Bugu da ƙari na bayar da umarnin a bai wa dukkanin ƴan wasa da masu horas da su gidaje masu ɗakuna uku-uku.

    "Haka nan kuma, akwai kyautar kudin naira kwatankwacin dala 100,000 ga kowace ƴar wasa 24 da kuma dala 50,000 ga tawagar masu horaswa."

  4. MDD ta yi Allah-wadai da harin ƴan bindiga a Gabashin DR Congo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ya Allah-wadai da wani mummunan hari da 'yan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar IS suka kai a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo inda aka kashe akalla mutane 43.

    Mafi yawan waɗanda suka mutu mabiya addinin Kirista ne, ciki harda wasu mutane da ke cikin ibada a lokacin da dakarun Allied Democratic Forces (ADF) suka kai harin a daren Asabar.

    Ana kuma zargin cewa wasu mutane da dama an sace su a lokacin harin.

  5. Adadin mutanen da suka mutu a Gaza tun fara yaƙi ya kai 59,921

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar lafiyar Hamas a Gaza ta bayyana cewa mutane 100 sun mutu cikin sa’o’i 24 da suka gabata, lamarin da ya kai jimillar mutanen da suka mutu tun bayan fara yaƙin zuwa 59,921.

    Haka kuma, an ƙarin 382 ne suka jikkata, wanda hakan ya sa adadin waɗanda suka jikkata ya haura zuwa 145,233.

    Wannan sabon adadi na mace-mace ya zo ne bayan dakartar da kai hare-hare na sa'o'i 10 domin isar da kayan jin ƙai a Gaza da Isra'ila ta amince da daga ƙarfe 10:00 zuwa 20:00 na agogon gida.

    Tun a baya an sanar da cewa mutum 14 sun mutu sakamakon yunwa da rashin abinci mai gina jiki cikin sa’o’i 24 da suka wuce.

  6. Thailand da Cambodia sun amince da tsagaita wuta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Thailand da Cambodia sun amince da tsagaita wuta ba tare da ɓata lokaci ba kuma ba tare da wani sharaɗi ba” bayan kwana biyar na faɗa a kan iyakar ƙasashen biyu.

    Faɗar ta yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 33 tare da raba dubban mutane da muhallansu.

    “Wannan babban mataki ne na farko wajen rage rikici da dawo da zaman lafiya da tsaro,” in ji firaministan Malaysia, Anwar Ibrahim, yayin da yake sanar da dakatar da faɗa yana mai cewa an cimma matsaya cewa za a daina faɗa daga ƙarfe 12 na dare.

    A farko, Thailand ta ƙi amincewa da tayin shiga tsakani da Anwar ya bayar, sai dai ta amince daga bisani bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba za a cigaba da tattaunawar haraji ba har sai “an daina faɗa”.

    Tashin hankali a kan tsohuwar takaddamar kan iyaka ya ƙara ƙamari a watan Mayu bayan wani sojan Cambodia ya mutu a wata arangama.

    Daga bisani kuma Thailand ta sanya takunkumi ga 'yan ƙasa da yawon bude ido daga shiga Cambodia ta hanyar ƙasa, yayin da Cambodia ta haramta shigo da wasu kayayyaki daga Thailand.

    Lamarin ya ƙara ta’azzara a makon da ya gabata, bayan wani soja dan Thailand ya rasa ƙafarsa a fashewar bam.

  7. Yadda ƴanbindiga suka yi wa mutum 38 yankan rago a Zamfara

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴanbindiga sun kashe wasu mutum 38 ta hanyar yi musu yankan rago, daga cikin mutum 56 da suka yi garkuwa da su sakamakon gaza biyan kuɗin fansa da ƴanbindigar suke nema.

    Mutanen da aka kashe ɗin sun kasance ƴan ƙauyen Banga da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara.

    Shugaban ƙaramar hukumar, Manniru Haidara Ƙaura wanda ya shaida wa BBC yadda al'amarin ya faru, ya ce yawancin waɗanda aka yi wa yankan ragon matasa ne.

  8. Faransa da Saudiyya na jogorantar tattaunawar samar da ƙasashen Isra'ila da Falasɗinu

  9. Ciwon hanta da hanyoyin kamuwa da shi

  10. Hotuna daga taron tattaunawar zaman lafiya tsakanin Thailand da Cambodia

  11. Za a fuskanci katsewar wutar lantarki a Legas tsawon kwana 25

  12. Tarayyar Turai da Amurka sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci

  13. Thailand da Cambodia za su tattauna matakan zaman lafiya yayin da rikicin iyaka ke tsananta

  14. Tsagaita wutar sa'a 10 a Gaza ta fara aiki domin shigar da kayan agaji