Rundunar ƴansandan jihar Kebbi ta ce jami'anta sun samu nasarar kashe ƴanbindiga uku, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK47 da harsasai da dama a yankin ƙaramar hukumar Shange da ke jihar.
A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta ruwaito daga kakakin rundunar, CSP Nafiu Abubakar, rundunar ta ce ƴansanda sun fafata da ƴanbindigar ne a yankin na Shanga tare da taimakon ƴan-sa-kai, sannan wasu sun tsere da raunuka.
"Bayanan sirri muka samu cewa ƴanbindiga na taruwa a wani daji a kusa da titin Tungargiwa da Saminaka, suna kitsa garkuwa da matafiya a hanyar, shi ne jami'anmu suka kai ɗauki"
Kakakin ya ƙara da cewa wasu ƴanbindigar sun kai hari a garin Kesan da ke Shanga ɗin dai, inda suka yi garkuwa da mutum ɗaya mai suna Abdulmumini Alhaji Ahmadu mai shekara 25.
Ya ce amma daga bisani ƴansandan sun bi ƴanbindigar, inda suka samu nasarar ceto mutumin, "amma sun harbe shi a ƙafa."