Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 24/08/2025.

Taƙaitattu

  • Latsa nan ku shiga tasharmu ta WhatsApp
  • Rundunar sojin Najeriya ta musanta yunƙurin juyin mulki
  • Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 21 daga hannun 'yanbindiga a jihar Kwara
  • Shugaba Tinubu ya koma Najeriya bayan taron Italiya
  • 'An kashe Falasɗinawa 11 a Gaza'
  • Ba zan yi takarar shugaban ƙasa da Tinubu ba - Wike
  • An gano hanyar gwajin cutar kansa a matakin farko

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunoni 140

    Ukraine

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaƙi ɗari da arba'in.

    Wannan ce musayar fursunoni ta baya-bayan nan tsakanin ƙasashen wani lamari da ke nuna ɗaya daga cikin batutuwan haɗin kai tsakanin ƙasashen masu rikici da juna.

    Rasha ta ce sojojinta suna Belarus inda suke samun kulawar likitoci. Ta kuma ce Kyiv ta maido mata da mutum takwas daga yankin Kursk.

  2. Ƙungiyar Houthi na ɗanɗana kuɗarta - Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce hare-haren da suka kai kan cibiyoyin Houthi a Yemen sun lalata fadar shugaban ƙasa da ke Sanaa da kuma cibiyar samar da lantarki da ke birnin.

    Ya dage cewa ƙungiyar Houthi da ke samun goyon bayan Iran na ɗanɗana kuɗarta ne kan hare-haren da ta kai kan Isra'ila.

    Mayaƙan Houthi sun ce hare-haren Isra'ila sun halaka mutum biyu tare da raunata wasu talatin da biyar.

    A cewar wakilin BBC, shekaran jiya Juma'a, ƴan Houthi sun ce sun kai hare-hare uku kan Isra'ila har da guda da suka kai kan babban filin jirgin saman kasar.

    Tun farko, sojojin Isra'ila sun ce ƴan Houthi sun yi amfani da makami mai linzami a hare-haren da suka kai baya-bayan nan a ƙasar.

  3. Ƴansanda sun ce sun kashe ƴanbindiga uku a Kebbi

    Ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan jihar Kebbi ta ce jami'anta sun samu nasarar kashe ƴanbindiga uku, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK47 da harsasai da dama a yankin ƙaramar hukumar Shange da ke jihar.

    A wata sanarwa da jaridar Daily Trust ta ruwaito daga kakakin rundunar, CSP Nafiu Abubakar, rundunar ta ce ƴansanda sun fafata da ƴanbindigar ne a yankin na Shanga tare da taimakon ƴan-sa-kai, sannan wasu sun tsere da raunuka.

    "Bayanan sirri muka samu cewa ƴanbindiga na taruwa a wani daji a kusa da titin Tungargiwa da Saminaka, suna kitsa garkuwa da matafiya a hanyar, shi ne jami'anmu suka kai ɗauki"

    Kakakin ya ƙara da cewa wasu ƴanbindigar sun kai hari a garin Kesan da ke Shanga ɗin dai, inda suka yi garkuwa da mutum ɗaya mai suna Abdulmumini Alhaji Ahmadu mai shekara 25.

    Ya ce amma daga bisani ƴansandan sun bi ƴanbindigar, inda suka samu nasarar ceto mutumin, "amma sun harbe shi a ƙafa."

  4. Ba Rasha ba ce ke tarnaƙi ga tsagaita yaƙi a Ukraine - Amurka

    Amurka

    Asalin hoton, Reuters

    Mataimakin shugaban Amurka ya musanta batun da ake cewa Rasha tana jan ƙafa a ƙoƙarin da ake na ganin an samu zaman lafiya a Ukraine.

    JD Vance ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta NBC cewa a karon farko Moscow ta amince da wasu muhimman batutuwa tun bayan da ta ƙaddamar da mamaya kan Ukraine shekara uku da rabi da suka gabata.

    Ya ce sun haɗa da bayar da tabbacin tsaro don tabbatar da cewa ba za a sake mamaye Ukraine ba.

    A Kyiv, Shugaba Volodymyr Zelensky ya aika wani saƙo domin bikin ranar ƴancin kai a ƙasarsa.

    Ya bayyana cewa abin da Ukraine kawai take nema shi ne zaman lafiya mai ɗorewa amma za ta ci gaba da yaƙi don samun ƴancinta idan har ba a ji kiran ba.

  5. Haɗarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum shida a Sokoto

    Zubaida Umar

    Asalin hoton, Zubaida Umar

    Wani sabon haɗarin kwale-kwale ya yi ajalin aƙalla mutum shida a Garin-Faji da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

    A wani rubutu da shugabar hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, Zubaida Umar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce haɗarin ya auku ne a lokacin da mutum 30 suke tafiya a ranar Juma'ar da ta gabata.

    Ta ce sun samu labarin aukuwar lamarin ne a ranar Asabar, inda jami'anta da haɗin gwiwar jami'an hukumar agajin gaggawa ta jihar Sokoto da sojoji da sauran masu da tsaki suka kai ɗauki.

    Ta rubuta cewa an ceto mutum 21 da matuƙa kwale-kwale biyu, "amma mutum shida sun rasu, sannan har yanzu ana neman mutum uku," in ji ta, sannan ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin neman su.

    Ta ce tuni mutanen garin suka birne waɗanda suka rasu, sannan ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar sufurin ruwa su tabbatar ana bin dokokin sufurin ruwa domin kare yawaitar haɗari.

  6. 'Dakarun RSF sun yi garkuwa da mata shida a Sudan'

    Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Sudan na nuna cewa dakarun RSF sun harba bama-bamai a wani asibiti da ke yankin Arewacin Dafur na Sudan.

    Ganau da ƙungiyoyin agaji sun ce dakarun na RSF sun samu nasarar kai harin ne bayan sun kutsa sansanin ƴan gudun hijira na Abu Shouk da ke kusa da birnin El-Fasher, inda bayan harin kuma suka yi garkuwa da mata shida da ƙananan yara biyu.

    Yanzu dai birnin El-Fasher ne kawai babban birni da ke ƙarƙashin kulawar sojojin ƙasar a yammacin Darfur.

    Tun daga watan Maris ne dakarun RSF suka ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a garin El-Fasher da maƙwabtan a yunƙurinsu na ƙara ƙarfi a yammacin ƙasar.

    Tun a watan Afrilun shekarar 2023 ne dai aka fara gwabza yaƙin basasar Sudan, inda ake gwabzawa tsakanin sojojin ƙasar da ƴantawayen RSF.

  7. An hana bikin Ranar Ƙauyawa a Jalingo

    Majalisar Musulmi a garin Jalingo na jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ta sanar da matsayar malamai da sarakuna ta hana bukukuwan Ranar Ƙauyawa da ake yi idan za a yi aure da ajo da sauran bukukuwan da ta ce sun saɓa da addini.

    Majalisar ta ce bukukuwan sun saɓa da addini kuma ana yaɗa abin da suka kira da alfasha, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito a jiya Asabar.

    "Majalisar ta haramta tarukan bukukuwan Ranar Ƙauyawa da Ajo da sauran bukuwa marasa kyau a lokacin bukukuwan aure," in ji Imam Tajudeen Nuhu a madadin majalisar ta Taraba.

    Majalisar ta ce duk wani wanda ya karya dokar, "babu limamin da zai ɗaura masa aure ko ya jagoranci bikin aure a gidan, ko jagorantar jana'iza ko wa'azin aure ko halartar raɗin suna a gidansa.

  8. Koriya ta Arewa ta ce ta yi gwajin makamai masu linzami biyu

    Makaman Koriya ta Arewa

    Asalin hoton, Reuters

    Kafar yaɗa labarai ta Koriya ta Arewa ta ce ƙasar ta yi harba wasu makamai biyu masu linzami na kariyar samaniya bisa jagorancin Shugaba Kim Jong Un.

    Makaman na da "nagartar yaƙi" kuma suna aiki ne da "fasaha ta musamman", in ji kamfanin dillancin labarai na Korean Central News Agency (KCNA).

    "Gwajin na ranar Lahadi na nuni da fasahar da makaman biyu ke da ita wajen lalata makamai masu linzami da aka harbo ta sama," a cewar KCNA.

    An yi gwajin ne 'yan awanni bayan Koriya ta Kudu ta tabbatar cewa ta yi harbin gargadi kan dakarun Arewa da suka tsallaka cikin iyakarta na ɗan lokaci.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dakarun Arewa kusan 30 suka tsallaka iyakar ƙasashen biyu da ke da matuƙar tsaro.

  9. Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 64 cikin awa 24 a Birnin Gaza, in ji ma'aikatar lafiya

    Birnin Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Jiragen sama da tankokin yaƙi na Isra'ila na ci gaba da yi wa Birnin Gaza luguden wuta domin ƙwace iko da shi.

    Falasɗinawa mazauna yankin kusa miliyan ɗaya sun ce suna jin rugugi marasa ƙaƙƙautawa a arewaci da gabashin birnin.

    Dakarun Isra'ila sun sake komawa sansanin Jabalia da ke arewacin zirin.

    Falasɗinawa 64 aka kashe zuwa yanzu tare da raunata kusan 300 cikin awa 24 da suka gabata, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza.

    Ta ce jimillar mutanen da Isra'ila ta kashe tun daga Oktoban 2023 sun kai 62,686, da kuma jikkata 157,951.

  10. Japan za ta bai wa Najeriya rancen dala miliyan 190 don inganta lantarki

    Adebayo Adelabu

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Ministan Lantarki Adebayo Adelabu (tsakiya) na cikin tawagar da Shugaba Bola Tinubu ke jagoranta a taron ƙasashen Afirka na Japan

    Ministan Lantarki a Najeriya ya ce Adebayo Adelabu ya ce gwamnatinsu na shirin karɓar rancen dala miliyan 190 daga Japan domin "inganta ɓangaren makamashi mai dorewa".

    Acewar wata sanarwa daga ma'aikatarsa a ranar Asabar, ministan ya bayyana haka ne yayin taron ƙasashen Afirka da Japan da ke gudana a birnin Yokohama.

    Ma'aikatar ta ce tawagar wakilan Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta tattaunada kamfanoni a ɓangaren lantarki da makamashi.

    Da yake magana yayin taron, Mista Adelabu ya ce hukumar Japan International Cooperation Agency (JICA) ce za ta bayar da lamunin, inda shirin zai samar da makamashi maras gurɓata muhalli ga yankunan da ba su fiya samun sa ba a Najeriya.

    "Wannan ƙari ne kan dala miliyan 750 da Bankin Duniya ya ba mu ƙarƙashin shirin Mission 300 Compact da zai samar da makamashi mai ɗorewa da tabbatacciyar lantarki ga mutum miliyan 17 a Najeriya," in ji sanarwar.

  11. Birtaniya za ta sauya yadda ake neman mafaka a ƙasar

    Masu zanga-zanga a Birtaniya

    Asalin hoton, PA Media

    Gwamnatin Birtaniya na shirin sauya tsarin yadda ake neman mafaka a ƙasar da zimmar rage yawan baƙin da ke zama a otel kafin a amince da buƙatarsu.

    Za a kafa wata hukuma mai zaman kanta da za ta dinga sauraron ƙorafe-ƙorafen mutane cikin sauri.

    Sakatariyar Harkokin Cikin Gida Yvette Cooper ta ce yunƙurin zai taimaka wajen rage ɓata lokaci.

    An sha sukar gwamnatin domin ta rage dogaro da otel-otel wajen ajiye masu neman mafaka, har ma aka dinga yin zanga-zanga a faɗin ƙasar ranar Asabar game da shirin.

    Ministoci sun ci alwashin daina amfani da otel-otel a majalisar dokoki, amma har yanzu akwai masu neman mafaka 32,000 da ke zaune a otel-otel.

  12. 'Yansandan Najeriya sun kama matashi da zargin daddatsa matar ɗan'uwansa

    Wani mutum a bayan kanta

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yansanda a jihar Kwara da ke tsakiyar Najeriya sun kama wani mutum mai suna Sylvester Enemo da zargin kashe wata mai ciki Esther Enemo a Ilorin babban birnin jihar.

    Rahotonni sun ce matashin mai shekara 29 ya daddatsa gawar matar mai shekara 39 ne, wadda kuma aka ce matar ɗan'uwansa ce, bayan ya halaka ta a unguwar Temidire ranar Laraba.

    Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa mijin matar ya yi tafiya a lokacin da lamarin ya faru.

    "Ƙarin bincike ya sa an gano sassan jikin matar da aka zuba a wani buhu kuma aka jefar a ƙarƙashin wata gada," a cewar sanarwar da kakakin 'yansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta fitar.

    Ta ƙara da cewa jami'anta sun kai gawar Esther asibitin koyarwa na Jami'ar Ilorin.

  13. Masu iƙirarin jihadi sun kori sojojin Mali daga garin Farabougoum

    Sojojin Mali

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Mali ta amince cewa ta bar wani birni da ke tsakiyar ƙasar wanda masu ikirarin jihadi suka kwace, to amma ta bayyana janyewarta daga wajen a matsayin dabara.

    Rahotanni sun ce sojoji da fararen hula sun tsere sun bar Farabougoum wanda ke fama da hare-hare tun a ranar Talatar da ta gabata.

    Wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa masu tayar da ƙayar baya ta JNIM mai alaka da kungiyar al-Qa'ida ne ke iko da birnin.

    Ya ce su ne ma suka jagoranci sallar Juma'a da aka yi a babban masallacin birnin.

    Mai magana da yawun rundunar sojin Mali ya ce suna shirin sake kwace Farabougoum.

  14. Mun kashe 'yan Boko Haram 35, in ji sojin saman Najeriya

    Jirgin sojin sama na Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Airforce

    Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta kashe mayaƙa masu iƙirarin jihadi fiye da 35 a wasu hare-hare da ta kai jiya Asabar a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Ta ce ta kai hare-haren ne a wurare huɗu da ke maƙwabtaka da ƙasar Kamaru bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa sun taru a wuraren.

    A kwanan nan ƙungiyar Boko Haram da Iswap sun matsa ƙaimi wajen kai wa sojoji hare-hare a yankin.

    Sanarwar da rundunar ta fitar ta ƙara da cewa dakarun sojin ƙasa sun tabbatar cewa "yanayi a yankin ya lafa"

    A ranar Juma'a ma rundunar sojin ƙasar ta ce ta kashe wasu kwamandojin Boko Haram biyu da kuma mayaƙa 11 a jihar ta Borno bayan sun daƙile harin da suka yi niyyar kai wa sojoji.

  15. Dubban Isra'ilawa na zanga-zanga kan yaƙin Gaza

    Isra'ilawa

    Asalin hoton, Reuters

    Dubban mutane sun sake yin gangami a sassan Isra'ila suna neman a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yain Gaza.

    Masu zanga-zangar sun ce shirin rundunar sojin Isra'ila na kwace ikon Birnin Gaza zai jefa rayuwar mutanen da suka rage a tsare a hannun Hamas cikin hadari.

    Tsohon ministan tsaron Isra'ila, Benny Gantz, ya yi kira ga 'yan'adawa da su goyi bayan shirin samar da gwamnatin hadaka domin a taimaka wajen sako raguwar mutanen da ke tsare.

    Gwamnatin hadin kan da Firaminista Benjamin Netanyahu ke jagoranta a yanzu ta dogara ne kan samun goyon bayan jam'iyyu masu tsattsauran ra'ayi wadanda ba su goyon bayan a cimma yarjejeniya da Hamas domin a kawo karshen yakin da ake yi.

    A Gaza, ma'aikatar lafiya ta ce mutum 60 sun mutu sakamakon hare-haren Isra'ila da kuma karancin abinci mai gina jiki a jiya Asabar kadai.

    Isra'ilawa

    Asalin hoton, Reuters

  16. Maraba

    Muna yi muku maraba da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Lahadi.

    Za mu kawo abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya daga yanzu har zuwa ƙarfe 9:00 na dare.

    Umar Mikail ne zai kasance da ku zuwa ƙarfe 4:00.