Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/05/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi da Abdullahi Bello Diginza da Aisha Aliyu Jaafar

  1. An harbe wasu Isra'ilawa biyu a birnin Washington na Amurka

    An harbe wasu ma'aikatan ofishin jakadancin Isra'ila biyu, mace da namiji a birnin Washington a lokacin da suke barin wani taro a wani gidan tarihin Yahudawa.

    Shugaban ƴansandan birnin Pamela Smith, ta ce wani mutum mai suna Elias Rodriguez ne ya tunkari waɗanda lamarin ya rutsa da su tare da buɗe wuta, kujma tuni suka kama shi.

    Wani da abun ya faru a kan idonsa ya ce mutumin ya yi ta ihun neman yancin Falasɗinawa, yana cewa ya yi hakan ne don nuna goyon baya ga mutanen Gaza.

    Babbar Lauyar gwamnatin Amurka Pam Bondi, wadda ofishinta ke kusa da wajen, ta ce ta ruga don ta ga me ke faruwa, kuma abun da ta tarar ya munana, kamar yadda ta ce.

  2. Trump ya titsiye shugaban Afirka ta Kudu a Amurka

    Shugaban Amurka Donald Trump ya titsiye takwaransa na Afrika ta kudu, har ma ya kunna masa wani bidiyo don tabbatar da ikirarinsa cewa ana yi wa manoman farar fata a Afrka ta kudu kisan kiyashi.

    Cikin wanin bidiyo da shugaban na Amurka ya kunna wa Ramaphosa ya nuna wasu dubban kaburbura da Mista Trump ya ce na manoman da aka kashe ne, kodayake bai bayyana inda aka nadi bidiyon ba.

    A nasa ɓangare Mista Ramaphosan ya yi watsi da zargin na Trump, yana mai cewa ya je tattauna batun kasuwanci ne, don haka ba abun da ya kai shi kenan ba.

    Jaridu a masana sun sha musanta zargin na Mista Trump.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar ranar Alhamis.

    barkanmu da sake haɗuwa da ku a daidai wannan lokaci, inda za mu kewaya da ku faɗin duniya domin kawo muku halin da ta wayi gari.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.