Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 24 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Me zai bambanta zaɓen Najeriya mai zuwa da waɗanda suka gabata?

    Ƴan Najeriya na sa ran ganin sauye-sauye a hanyoyin gudanar da zaɓukan ƙasar a zaɓen 2027 da ke tafe nan da shekara guda.

    Ana sa ran ganin sauye-sauyen ne bayan fara aiki da sabuwar dokar zaɓen ƙasar da aka yi wa gyaran fuska.

    A makon da ya gabata ne shugaban ƙasar da ya sanya hannun kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar ta 2026, in da aka samar da manyan gyare-gyare, wadanda za su shafi tsarin gudanar da zaɓukan ƙasar.

    Sauye-sauyen na zuwa ne bayan ƙorafe-ƙorafen ƴan ƙasar, kan wasu dokokin zaɓen ƙasar da suke ganin ba su dace da yanayin ƙasar ba.

    An dai kai ruwa rana a majalisar dokokin ƙasar kafin amincewa da sabbin dokokin, lamarin da ya kai ƙungiyoyin fararen hula shirya zanga-zangar matsin lamba ga majalisar dokokin ƙasar domin amincewa da sakamakon.

    An ɓullo da sauye-sauyen masu yawa a tsarin zaɓen ƙasar, kama daga kan fitar da ƴan takara zuwa yakin neman zaɓe da ma tattara sakamako.

    Masu sharhi kan al'amuran siyasa na ganin akwai sauye-sauye da za a gani a tsarin zabukan kasar masu zuwa.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.