Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 29 zuwa 5 ga watan Disamba 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 29 zuwa 5 ga watan Disambar 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An raba jadawalin Gasar Kofin Duniya 2026

    Rukunin A:

    • Mexico
    • Afirka ta Kudu
    • Koriya ta Kudu
    • Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin D

    Rukunin B:

    • Canada
    • Qatar
    • Switzerland
    • Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin A

    Rukunin C:

    • Brazil
    • Moroko
    • Scotland
    • Haiti

    Rukunin D:

    • Amurka
    • Paraguay
    • Australia
    • Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin C

    Rukunin E:

    • Germany
    • Ivory Coast
    • Ecuador
    • Curacao

    Rukunin F:

    • Netherlands
    • Japan
    • Tunisia
    • Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Uefa rukunin B

    Rukunin G:

    • Belgium
    • Egypt
    • Iran
    • New Zealand

    Rukunin H:

    • Spain
    • Saudi Arabia
    • Uruguay
    • Cape Verde

    Rukunin I:

    • France
    • Senegal
    • Norway
    • Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Fifa rukunin 2

    Rukunin J:

    • Argentina
    • Algeria
    • Austria
    • Jordan

    Rukunin K:

    • Portugal
    • Uzbekistan
    • Colombia
    • Ƙasar da za ta fito a wasan cike gurbi na Fifa rukunin 1

    Rukunin L:

    • England
    • Croatia
    • Panama
    • Ghana
  2. Ƙasashen da har yanzu ba su kammala wasan cike gurbi ba

    Har yanzu akwai wasanni cike gurbi da ba a kammala ba, balle a san takamaimai ƙasashen da za su fito.

    Ƙasashen sun rabu zuwa rukuni shida:

    Wasan cike gurbi na Uefa rukunin A: Italiya, Wales, Bosnia-Herzegovina, Arewacin Ireland

    Wasan cike gurbi na Uefa rukunin B: Ukraine, Poland, Albaniya, Sweden

    Wasan cike gurbi na Uefa rukunin C: Turkiyya, Slovakiya, Kosovo, Romaniya

    Wasan cike gurbi na Uefa rukunin D: Denmark, Czech Republic, Republic of Ireland, North Macedonia

    Wasan cike gurbi na Fifa rukunin 1: DR Congo, Jamaica, New Caledonia

    Wasan cike gurbi na Fifa rukunin 2: Iraqi, Bolivia, Suriname

  3. Donald Trump ya lashe kyautar zaman lafiya ta FIFA

    Shugaban Amurka Donald Trump ya lashe sabuwar kyautar zaman lafiya ta hukumar ƙwallon ƙafa ta FIFA, wato FIFA peace prize.

    FIFA ta ce ta ba Trump wannan lambar yabo ne sanadiyyar rawar da ya taka wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

    An bai wa Trump lambar yabon mai launin zinare, hannuwa riƙe da duniya a sama.

  4. Ana bikin raba jadawalin gasar kofin duniya ta FIFA

    Ana gudanar da bikin raba jaddawalin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya a cibiyar John F Kennedy da ke birnin Washington na ƙasar Amurka.

    Yayin da ya rage saura ƙasa da kwana 200 a fara gasar, kowace ƙasa ta zura ido ta ga ƙasashen da za ta kara da su.

    A wannan karo ƙasashe 48 ne za su kara a gasar, a maimakon 32 da suke bugawa a baya.

    Za a samu rukuni 12, kowane ƙunshe da ƙasashe hudu.

  5. Arsenal: Mosquera zai yi jinyar aƙalla mako shida

    Arsenal ta ƙara faɗawa cikin matsalar ƴan wasan baya masu jinya, inda aka tabbatar cewa ɗan wasanta Cristhian Mosquera zai iya shafe aƙalla mako shida yana jinya.

    Duk da haka ana sa ran za a sake yi wa ɗan wasan, ɗan asalin ƙasar Spain gwaji domin tantance munin raunin nasa, wanda ya samu a karawar Arsenal da Brentford.

    Raunin Mosquera ya ƙara jefa Arsenal cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi, wadda manyan masu tsaron bayanta Gabriel Maghales da William Saliba ke jinya.

    Mosquera da Piero Hincape ne suka cike gurbin manyan masu tsaron bayan na Arsenal, to amma yanzu da wannan matsala, Arsenal za ta so Saliba ya dawo taka leda cikin hanzari.

    A ɓangare daya ana sa ran Gabriel Maghales ba zai dawo wasa ba har sai cikin watan Janairu.

  6. Wane hali ake ciki kan raunin ƴan wasan Arsenal?

    Mai horas da ƙungiyar Arsenal Mikel Arteta ya gana da manema labarai a ranar Juma'a, sai dai bai bayar da amsa kai-tsaye ba game da ko ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Declan Rice zai yi wasa ranar Asabar a karawar da za su yi da Aston Villa ba.

    Ya ce “Bari mu gani, za mu yi atisayi a yau. Ko wace awa tana da muhimmanci domin mu gane waɗanne ƴan wasa ne za su yi wasa, sannan mu yanke hukunci.”

    A game da batun ɗan wasan baya Cristhian Mosquera ya ce: “Wannan ne ba mu da tabbas, za mu yi wani gwajin a yau domin ganin wane hali ake ciki.

    Game da Trossard da William Saliba: “Ƴan kwanaki ne suka rage musu (su dawo)”.

  7. Yadda za a yi karon-batta a Premier cikin ƙarshen mako

    A wannan mako akwai karawa tsakanin ƙungiyoyin Premier da za su ɗauki hankali.

    Ƙungiyar da ke kan tebur, wato Arsenal za ta kara da ta uku Aston Villa; karon-batta ne tsakanin ƙungiyoyi biyu da ke kan ganiya.

    Ga yadda ƙungiyoyin za su kara:

    Asabar, 6 ga watan Disamba

    • Aston Villa v Arsenal
    • Bournemouth v Chelsea
    • Everton v Nottingham Forest
    • Manchester City v Sunderland
    • Newcastle United v Burnley
    • Tottenham Hotspur v Brentford
    • Leeds United v Liverpool

    Lahadi, 7 ga watan Disamba

    • Brighton v West Ham United (
    • Fulham v Crystal Palace

    Litinin, 8 ga watan Disamba

    • Wolves v Manchester United (20:00)
  8. Ekong ya yi ritaya daga buga wa Najeriya tamaula

    Ƙyaftin ɗin tawagar Najeriya, William Troost-Ekong ya sanar da yin ritaya a lokacin da Super Eagles ke shirin shiga gasar cin kofin Afirka da za a yi a Morocco daga cikin watan Disamba.

    Troost-Ekong, mai shekara 31, ya sanar da hakan da cewar wasan da ya buga wa kasar da Jamhuriyar Congo a wasan cike gurbin shiga gasar kofin duniya da Super Eagles ba ta kai bante ba

    Mai tsaron bayan ya fara taka leda a 2015, wanda ke taka leda tare da Leon Balogun — waɗanda suka kai Najeriya gasar kofin duniya a Rasha a 2018 da taka leda a wasannin cin kofin Afirka.

    Ya lashe lambar yabo uku ciki har da Tagulla a Rio Olympics a 2016 da wata Tagulla a Afcon 2019.

    Shi ne ya lashe ƙyautar fitatcen ɗan wasa a gasar cin kofin Afirka da aka yi a 2023 da Ivory Coast ta lashe, Najeriya ta yi ta biyu.

    Ya buga wa tawagar Najeriya wasa 83 da cin ƙwallo takwas cikin kaka 10.

    A watan Agustan 2024 ne Ekong ya koma taka wa ƙungiyar Al-Kholood ta Saudiyya leda daga PAOK ta ƙasar Girka.

  9. Ba na shiga shafukan sada zumunta don kauce wa zagi – Amorim

    Mai horas da ƴan wasan Manchester United, Ruben Amorim ya bayyana cewa ba ya shiga shafukan sada zumunta domin kare kansa da iyalansa daga zagi.

    Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano munanan saƙonni a shafukan sada zumunta, ciki har da barazanar kisa da fyaɗe kan masu horaswa da ƴan wasan ƙungiyoyin gasar Premier da gasar mata ta Super League, a watan da ya gabata.

    Amorim da mai horas da ƙungiyar Liverpool Arne Slot da na Newcastle Eddie Howe na daga cikin waɗanda aka fi yi wa waɗannan saƙonni a gasar ta Premier.

    “Abu ne da aka saba gani a kowace sana’a,” in ji Amorim.

    “Ba na karantawa; nakan kare kaina. Ba na kallon talabijin idan ana magana kan Manchester United, ba don ban amince da abin da ake faɗi ba – a mafi yawan lokuta na yarda haka ne – to amma hanya ce ta kare lafiyata.

    “Abin da nake ji a matsayina na mai horaswa ya isa. Ba sai na ƙara da yadda wani ke ji ba. Abu mafi muhimmanci shi ne - na kare kaina.”

    Binciken BBC ya duba saƙonnin shafukan sada zumunta da aka wallafa a lokacin wasanni 10 na gasar Premier, da wasa shida na gasar mata a ranakun 8 da 9 ga watan Nuwamba.

    Binciken ya gano kalamai na ɓatanci da nuna wariyar launin fata da ƙiyayya da barazanar cin zarfi.

    An fi yin irin waɗannan kalamai ne kan masu horaswa, fiye da ƴanwasa, kuma kashi 82% na saƙonnin an wallafa su ne a shafin X, wato Twitter.

    Alƙaluman da aka tattara sun nuna cewa matsalar cin zarafin a shafukan sada zumunta na ƙaruwa.

    “Nakan yi asarar kuɗi daga masu ɗaukar nauyi,” in ji Amorim.

    Zan iya samun kuɗi sosai a Instagram (amma) gara na kare kaina da iyalina da rayuwata a kan samun daloli ko fama-famai.

    Manchester United ta kammala gasar Premier a kakar da ta gabata a matsayi na 15, wanda shi ne mafi muni tun bayan faduwa daga gasar da ta yi a kakar 1973-74.

  10. Haaland ya zama na 35 da ya ci ƙwallo 100 a Premier League

    Erling Haaland ya zama na 35 da ya ci kwallo 100 a Premier League, bayan da Manchester City ta je ta dura 5-4 a ragar Fulham, shi ne ya fara zura ta farko a Craven Cottage.

    Ɗan wasan tawagar Norway shi ne na farko da ya yi wannan bajintar a karancin wasa na 111, ya haura tarihin Alan Sherar da ya yi a 1995 da tazarar wasa 13 tsakani.

    Haaland zai kuma ƙalubalanci Sherer mai tarihin cin ƙwallaye a gasar mai 260.

    Ɗan wasan City ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Etihad zuwa kaka tara da za ta kare a karshen 2033/34.

  11. Nice ta yi tur da wasu magoya bayanta suka ci zarafin ƴan wasa da ma'aikata

    Kungiyar Nice ta la'anci wasu magoya bayanta "cikin kakkausar magana" bayan da 'yan wasa da ma'aikatan suka fuskanci cin zarafi lokacin da suka koma gida, bayan shan kashi 3-1 a hannun Lorient a ranar Lahadi.

    An bayar da rahoton cewa cikin wadanda aka kai wa hari akwai Terem Moffi da Jeremie Boga da daraktan wasanni Florian Maurice, yayin da gungun magoya baya kusan 400 suka taru a lokacin da bas ɗin kungiyar ta isa cibiyar horon ƴan wasa.

    Shaidu sun ce magoya bayan sun toshe hanyar da bas ɗin za ta shiga, sun kunna abubuwa masu tartsatsin wuta, suna rera wakokin ɓatanci tare da yi wa 'yan ƙwalon da ma’aikata ihu, lamarin da ya dauki kusan mintuna 45.

    'Dan wasan Ivory Coast Jeremie Boga yana jinya tun daga Litinin sakamakon abin da ya faru, a cewar kafofin yaɗa labaran Faransa.

  12. Fifa za ta raba jadawalin gasar cin kofin duniya ranar Juma'a

    Ranar Juma'a za a raba jadawalin gasar cin kofin duniya ta badi da za a yi a birnin Washington din Amurka da tawaga 48 za ta yi tata burza a wasa 104.

    Canada za ta shirya wasa 13 har da 10 a cikin rukuni da za a yi a birnin Toronto da Vancouver,

    haka ma 13 za ayi a Mexico da guda 10 a cikin rukuni da za a yi a birnin Guadalajara da kuma na Monterrey, yayin da za a yi 11 a Amurka.

    Za a yi bikin bude gasar a birnin Mexico a Estadio Azteka, sannan a rufe labulen wasannin ranar 19 ga watan Yuli a MetLife a birnin New Jersey.

  13. Afirka ta Kudu ta bayyana ƴan wasan da za su buga mata kofin Afirka

    Tawagar Afirka ta Kudu ta bayyana yan wasa 25 da za su wakilce ta a gasar cin kofin Afirka da za a yi a Morocco cikin watan Disamba - ciki har da biyu a karon farko da aka baiwa goron gayyata.

    Kociya, Hugo Bross ya kira matashi mai shekara 20 Shandre Campbell mai taka leda a Club Brugge da kuma Tylon Smith mai wasa a Queens Park Rangers, na kuma yi mamakin hakan.

    Afirka ta Kudu, wadda za ta je gasar cin kofin duniya da za a yi a badi a Amurka da Canada da kuma Mexico,

    Za ta kara a gasar kofin Afirka da za a fara a cikin watan nan tare da yan wasa tara da suka fafatawa a babbar gasar tamaula ta Afirka da aka yi a Ivory Coast.

    Afirka ta Kudu za ta fara wasa a birnin Marrakech a Morocco ranar 22 ga watan nan da Angola a rukuni mai zafi da ya hada da Masar da Zimbabwe.

  14. Mount na fatan United za ta ɗora daga kokarin da ta yi a Palace

    Mason Mount ya bukaci yan kwallon Manchester United su ci gaba da sa damtse da kwazo kamar yadda suka je suka doke Crystal Palace 2-1 a Premier League ranar Lahadi - ko sa samu komawa buga Champions League a badi.

    United ta taka rawar gani da cin Palace a Selhurst Park, wadda karon farko da aka doke ta a gida tun bayan wata tara, inda Joshua Zirkzee da kuma Mount, suka ci mata kwallayen.

    Wasa na hudu daga bakwai da Ruben Amorim ya yi nasara da hakan ya kai United mataki na bakwai a teburi da tazarar maki hudu tsakani da Manchester City ta biyu a lokacin da za a yi dan karen wasannin da yawa a cikin watan nan na Disamba.

  15. Za a kece raini tsakanin Barcelona da Atletico a daren Talata

    Barcelona za ta karɓi baƙuncin Athletico Madrid ranr Talata a gasar La Liga da za su fafata a Camp Nou.

    Barcelona tana matakin farko a teburin babbar gasar tamauala ta Sifaniya da maki 34, ita kuwa Athletico tana mataki na hudu a teburi da maki 31.

    Wasannin da suka buga a kakar 2024/2025

    Copa del Rey ranar Laraba 2 ga watan Afirilun 2025

    • Atl Madrid 0 - 1 Barcelona

    Spanish La Liga Ranar 16 ga watan Maris din 2025

    • Atl Madrid 2 – 4 Barcelona

    Copa del Rey ranar Talata 25 ga watan Fabrairun 2025

    • Barcelona 4 – 4 Atl Madrid

    Spanish La Liga ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024

    • Barcelona 1 – 2 Atl Madrid

    Barcelona za ta buga karawar ba tare da Ter Stegen da Gavi da kuma Fermín ba, saboda jinya.

  16. Guardiola bai fayyace ranar da Rodri zai koma taka leda ba

    Har yanzu Manchester City ba ta fayyace ranar da Rodri zai koma buga mata tamaula ba.

    Dan kwallon tawagar Sifaniya, wanda ya yi doguwar jinya a bara sakamakon raunin gwiwa, ya yi wa City wasa daya a kakar nan - sannan da yin dakika 60 daga karawa 10 da kungiyar Etihad ta yi a bayan nan.

    Mai shekara 29 ba zai yi fafatawar da City ta je gidan Fulham ba a Premier League ranar Talat,

    Kuma da kyar ne idan zai iya fuskantar Sunderland a Etihad ranar Asabar a dai babbar gasar tamaula ta Ingila.

  17. Za a buga wasa uku a Premier League ranar Talata

    A daren Talata za a ci gaba da wasan mako na 14 a gasar Premier League da za a yi karawa uku.

    • Bournemouth da Everton
    • Fulham da Manchester City
    • Newcastle United da Tottenham

    Kungiyar da Thomas Frank ke jan ragama tana 12 a teburin Premier, wadda ba ta yi nasara ba a wasa hudu baya.

    Ita kuwa kungiyar St James Park sai a ranar Asabar ta ci wasan farko a waje a bana, wadda ta je ta dura 4-1 a gidan Everton.

    Kuma kociyan Newcastle, Eddie Howe ya ce Yoane Wissa zai ci gaba da jinya, wanda har yanzu bai yi mata wasa ba tun bayan da ta sayo shi kan fara kakar nan.

    Ta dauki dan kwallon daga Brentford, wanda ke fama da ciwon gwiwa.

  18. Kamaru ta kori mai horas da tawagarta

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Kamaru (FECAFOOT) ta sanar da korar mai horas da babbar tawagar ƙwallon ƙafar maza ta ƙasar, Indomitable Lions, Marc Brys daga aikinsa, makonni kaɗan gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka.

    Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan saɓa ƙa'idoji da dama da kocin ya yi.

    Haka nan matakin na zuwa ne kimanin kwana biyu bayan sake zaɓen Samuel Eto'o a matsayin shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar a wa'adin jagoranci na biyu.

  19. An raba maki tsakanin Chelsea da Arsenal a Premier League

    Chelsea da Arsenal sun tashi 1-1 a Premier League da suka kara a wasan hamayya ranar Lahadi a Stamford Bridge.

    Ƙungiyoyin sun tashi minti 45 ɗin farko ba ci, sai dai kafin nan an bai wa ɗan ƙwallon Chelsea, Moises Caicedo jan kati a minti na 38, karon farko da aka yi masa jan kati a Premier League a wasansa na 130.

    Haka kuma shi ne na bakwai a Chelsea da aka kora a fafatawar hamayya da Arsenal, kuma na farko tun bayan David Luiz a Satumbar 2017.

    Daga baya Gunners ta farke ta hannun Mikel Merino, kuma ƙwallo na 10 da ya ci da ka a Premier League.

    Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburin Premier League da maki 30 da tazarar biyar tsakani da Manchester City ta biyu da kuma Chelsea ta uku mai 25, bayan wasan mako na 13.

    Ranar Laraba, Arsenal za ta karɓi bakuncin Brenford a wasan mako na 14, yayin da a dai ranar Chelsea za ta kece raini a gidan Leeds United.

  20. Barau FC ta doke Kwara United a Premier ta Najeriya

    Ƙungiyar Barau FC ta yi nasarar cin Kwara United 3-2 a wasan mako na 15 a gasar Premier ta Najeriya ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar mata a Kano, Najeriya.

    Waɗanda suka ci wa Barau FC ƙwallayen sun haɗa da Usman Maidubuji da Mohammed M Umar da kuma Stanley Oganbor.

    Ita kuwa Kwara United ta zura biyu ne ta hannun Chibuzor Ezeh da kuma Johnmark Shirsha.

    Da wannan sakamakon, Barau FC mai ƙwantan wasa tana da maki 16 tana ta 18 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Najeriya.

    Kwara United kuwa tana ta 14 a teburin mai maki 18, bayan wasannin mako na 15.