Mai
horas da ƴan wasan Manchester United, Ruben Amorim ya bayyana cewa ba ya shiga
shafukan sada zumunta domin kare kansa da iyalansa daga zagi.
Wani
bincike da BBC ta gudanar ya gano munanan saƙonni a shafukan sada
zumunta, ciki har da barazanar kisa da fyaɗe kan masu horaswa da ƴan wasan
ƙungiyoyin gasar Premier da gasar mata ta Super League, a watan da ya gabata.
Amorim
da mai horas da ƙungiyar Liverpool Arne Slot da na Newcastle Eddie Howe na daga
cikin waɗanda aka fi yi wa waɗannan saƙonni a gasar ta Premier.
“Abu
ne da aka saba gani a kowace sana’a,” in ji Amorim.
“Ba na
karantawa; nakan kare kaina. Ba na kallon talabijin idan ana magana kan
Manchester United, ba don ban amince da abin da ake faɗi ba – a mafi yawan
lokuta na yarda haka ne – to amma hanya ce ta kare lafiyata.
“Abin
da nake ji a matsayina na mai horaswa ya isa. Ba sai na ƙara da yadda wani ke
ji ba. Abu mafi muhimmanci shi ne - na
kare kaina.”
Binciken
BBC ya duba saƙonnin shafukan sada zumunta da aka wallafa a lokacin wasanni 10
na gasar Premier, da wasa shida na gasar mata a ranakun 8 da 9 ga watan
Nuwamba.
Binciken
ya gano kalamai na ɓatanci da nuna wariyar launin fata da ƙiyayya da barazanar
cin zarfi.
An fi
yin irin waɗannan kalamai ne kan masu horaswa, fiye da ƴanwasa, kuma kashi 82%
na saƙonnin an wallafa su ne a shafin X, wato Twitter.
Alƙaluman
da aka tattara sun nuna cewa matsalar cin zarafin a shafukan sada zumunta na
ƙaruwa.
“Nakan
yi asarar kuɗi daga masu ɗaukar nauyi,” in ji Amorim.
Zan
iya samun kuɗi sosai a Instagram (amma) gara na kare kaina da iyalina da
rayuwata a kan samun daloli ko fama-famai.
Manchester
United ta kammala gasar Premier a kakar da ta gabata a matsayi na 15, wanda shi
ne mafi muni tun bayan faduwa daga gasar da ta yi a kakar 1973-74.