An samu dogayen layuka a gidajen mai da ke Mali

Asalin hoton, AFP
An samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen man fetur a Bamako babban birnin kasar Mali bayan shafe' wata guda da mayakan kungiyar da ke da alaka da Al ka'ida suka hana shigo da man fetur ta hanyar kai wa manyan motoci masu dakon mai hari a manyan hanyoyin kasar.
Wasu daga cikin gidajen mai da aka tilastawa rufewa a makon daya gabata a yanzu sun sake budewa bayan tankokin mai fiye da 300 sun shiga cikin kasar daga Ivory tare da rakiyar sojojin.
Gwamnatin sojin ta ba ‘yan kasar tabbacin cewa lamarin na dan lokaci ne, amma kuma akwai fargabar man da ake ajiye da shi zai iya karewa a dan lokaci kankani, baya ga wasu da ke korafi game da karuwar farashinsa.
A ‘yan makonnin nan ma akwai birane da wasu sassan kasar da suka yi fama da karancin man da ma wutar lantarki.
Wasu daga cikin al’ummar kasar musamman a yankin Mopti na ci gaba da korafin yadda kasuwancinsu ke ci gaba da fuskantar matsala musamman wadanda ke safarar danyen kifi domin kuwa karancin wutar lantarkin na barazana ga yadda zaake adana shi.
Shekaru biyar da suka gabata, lokacin da gwamnatin sojin kasar ta kwace mulki, ta samu gagarumin goyon bayan al’ummar ta Mali, inda ta dauki alkawurra da dama cikin su har da kawo karshen matsalar tsaro da ‘yan aware wadanda galibinsu ‘yan kabilar buzaye ne da kuma ke da karfin iko a arewacin kasar suka haddasa, kuma daga bisani mayakan IS suka goya musu baya.
Wasu hotunan da aka yada a kafafen sada zumunta, sun nuna yadda jama’a suka yi dandazo a gidajen mai da ke Bamako babban birnin kasar inda suke kwashe tsawon lokaci sun jira.
Wani gidan rediyo mai suna Nostalgia ya ruwaito cewa farashin mai a birnin na Bamako ya karu da fiye da kashi 200 cikin dari.
Gwamnatin kasar dai ta bayyana cewa tana yin duk mai yuwa domin samar da mafita.




















