Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 14/05/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Badamasi Abdulƙadir Mukhtar

  1. Isra'ila ta tsananta hare-hare a Gaza

    Sojojin Isra'ila sun tsananta kai hare-hare a arewacin Gaza, inda cikin dare, aka samu rahoton mutuwar sama da mutane hamsin.

    Likitoci sun ce yara na daga cikin wadanda aka kashe a hare haren da aka kai a sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia.

    An kai hare-haren ne ta sama, bayan da Isra'ila ta ba da umarnin ficewa, tare da gargadin fararen hula da su kara nausawa kudancin kasar.

    Ko a jiya Talata, sai da wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani katafaren asibiti a Khan Younis da ke kudancin zirin, ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

    Rahotanni sun ce Isra'ilar na fakon dan uwan shugaban Hamas da aka kashe Yahya Sinwar ne.

  2. Assalamu alaikum

    Ma'abota BBC Hausa barkanmu da hantsin yau Laraba.

    Sannunmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Ku kasance da mu