Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Messi ya zama kan gaba a cin kwallaye a gasar kofin duniya mai 18

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
Argentina 2 , Austria 0 at Full time
Argentina
Austria
Full time
Hutun rabin lokaci Argentina 1 , Austria 0

Key Events

Argentina

  • L. Messi Goal 38 minutes, Goal 90 minutes plus 5

Austria

    Ba da ƙwallo a ci
    Argentina,F. Medina (38 minutes)

    Taƙaitattu

    Rahoto kai-tsaye

    Mohammed Abdu tare da taimakon AI

    1. , Argentina 1-0 Austria

      Argentina na shirin saka Julian Alvarez a cikin wasan nan, kenan za ta kara karfi ko ta samu kara na biyu - cin kwallo daya hadari ce komai na iya faruwa.

    2. , Argentina 1-0 Austria

      Kyaftin din Austria nake kallon wato David Alaba yadda yake bayar da gudunmuwa, wanda ya bar Real Madrid a karshen kakar da ta wuce.

      Ya sha jinya sosai, amma kalli yadda taka leda kamar ba shi ba.

    3. Argentina ta yi canjin dan wasa, Argentina 1-0 Austria

      Canjin yayi, domin Cristian Romero ya sha gwagwarmaya. An maye gurbinsa da Nicolas Otamendi.

    4. , Argentina 1-0 Austria

      Austria ta buga kwallon kai tsaye zuwa wajen golan Argentina, inda Martinez ya buge ta domin tana da zafi ba zai iya kamawa ba.

      Dama mai kyau ta farko da Austria ta samu a zagaye na biyun nan.

    5. , Argentina 1-0 Austria

      Austria ta samu bugun tazara mai kyau ko za ta amfani da wannan damar?

    6. , Argentina 1-0 Austria

      An yi bugun tazarar amma dabara ya yi kwallon zuwa cikin gidan Austria, amma babu wani hadari.

    7. , Argentina 1-0 Austria

      Messi ya dawo zagaye na biyu da kwarin gwiwa, inda aka yi bani in baka da shi ya jawo kwallon a guje zuwa gidan Austria, amma an yi masa keta an busa bugun tazara.

    8. , Argentina 1-0 Austria

      Messi ya samu dama mai kyau ya ja kwallo zuwa gidan Austria ya yi kokarin yanke gola, amma kwallon ya yi yawa ya fita waje.

      An kuma hura cewar ya fara da satar gida.

    9. , Argentina 1-0 Austria

      Cristian Romero yana kwance a kasa, amma Argentina za ta ci gaba da wasa daga baya an doki kafar Lionel Messi ya fadi kasa ya rike kafarsa..

    10. Mun koma zagaye na biyu, Argentina 1-0 Austria

      Mun koma zango na biyu za kuma a yi minti 45 za kuma yi hutun shan ruwa daga nan mu tantance wadda za ta yi nasara a karawar nan.

    11. Yadda aka gara kwallo a zagayen farko

    12. An busa hutu - za su je su huta

      Za su huta minti 15 daga nan su dawo a karasa minti 45 a wasa na bibiyu a gasar cin kofin duniya a rukuni na 10.

    13. , Argentina 1-0 Austria

      Argentina tana ta kashe lokaci, inda take bani in baka daga hagu zuwa dama tana tuttura kwallon baya daga nan ta kara matsawa gaba.

      Messi yana ta tafiya a cikin tdakiyar fili ba abinda ya dame shi.

    14. Minti bakwai aka kara, Argentina 1-0 Austria

      Ko Austria za ta farke kwallon da aka zura mata ko Argentina za ta je hutu da wannan sakamakon?

      Argentina tana da maki shida da cin kwallo hudu a wasa biyu daga cikin rukuni na 10 a gasar cin kofin duniya.

      Ita take rike da kofin da ta lashe a Qatar a 2022.

    15. Katin gargadi, Argentina 1-0 Austria

      An bai wa Stefan Posch katin gargadi, sakamakon rike Thiago Almada da ya yi.

    16. GOAL - Argentina 1-0 Austria, Lionel Messi

      Shi kenan ya kafa tarihi!!!!

      Lionel Messi shi ne dan wasan da ya fi yawan zura kwallaye a gasar cin kofin duniya, yayin da ya ci Austria kwallo mai kyau aka bugo daga gefen hagu, shi kuma yana gidan Austria bai bata lokaci ba ya buga ta faɗa raga.

      An kafa tarihi a filin wasa da ke Dallas a Amurka.

    17. , Argentina 0-0 Austria

      Argentina ta ruga da gudu da kwallon ta hannun Lautara Martinez amma mutum biyar sun hau kansa, ya yi kokarin bai wa Enzo Fernandez kwallon amma ta yi yawa.

    18. , Argentina 0-0 Austria

      Nahuel Molina ya yi kuskure a tsakiyar filin bayan da ya kayar da Marcel Sabitzer har kasa ƙasa.

      Dan wasan Austrian yana taka leda mai kyau, kuma karo na 100 da yake buga wa kasarsa tamaula.

    19. , Argentina 0-0 Austria

      Lionel Messi ya shiga cikin gidan Austria ya kuma buga ta taba gola ta koma wajen abokan hamayya.

      Argentina na samun damar maki a karawar nan. Messi na barar da kwallaye kam da yanzu sun kai wasu ukun rigis.

    20. , Argentina 0-0 Austria

      An ci gaba da wasan, kuma Austria na kai kora, kamar Argentina ta koma tare gida, amma wasan ya fara kyau.