Sai da safe
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Juma'a.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 08/11/2024
Abdullahi Bello, Isiyaku Muhammed, da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Juma'a.
Ana tuhumar wasu mutum uku a birnin New York da hannu a wani shirin Iran na yunƙurin kashe wasu Amurkawa ciki har da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Donald Trump.
Ma'aikatar shari'a ta zargi cewa a watan da ya gabata, rundunar juyin-juya halin Iran ta umarci Farhad Shakeri ya shirya yadda za a kashe Mista Trump.
Mista Shakeri ba shi cikin kotu a lokacin shari'ar, inda ake kyautata zaton yana Iran.
Sauran mutanen biyu dukkaninsu 'yan New York ne, kuma ana tuhumar su da kitsa kashe wani ɗanjaridar Amurka da ya yi fice wajen sukar Iran.

Asalin hoton, Reuters
Ofishin shugaban ƙasar Ukraine ya tabbatar da cewa attajirin duniya Elon Musk ya shiga tattaunawar da Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump ya yi da Shugaba Zelenskey ta waya.
"Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Trump ya yi hirar ne tare da Elon, sannan kuma Zelenskey ya gode masa game da [layin intanet na] Starlinks," kamar yadda wata majiya daga ofishin Mista Zelenskey ta shaida wa BBC.
"Gajeruwar hira ce da Elon Musk, amma kuma sun daɗe suna magana da Trump. Kusan minti 30 suna magana," a cewar majiyar.
Ukraine na amfani ne da layin intanet Sterlinks da Elon Musk ya mallaka domin samun sabis a wurare masu muhimmanci.

Asalin hoton, Kano State Government
Gwamnan jihar Kano a arewacin Najeriya ya bayyana aniyarsa ta sauke duk wani kwamashinansa da "aka gano ba shi da himm" a aikinsa nan gaba kaɗan.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature ya fitar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamatin da ke duba ƙwazon kwamashinonin.
"Nan gaba kaɗan al'umma za su ji matakin da gwamnatin za ta ɗauka," in ji sanarwar.
Ya ƙara da cewa “gwamnan ya ce rahoton ma ba zai yi wani amfani ba yanzu saboda tsawon shekara ɗaya da rabi da ya yi yana aiki ntare da su ya ba shi damar gane himmarsu ciki da baya, saboda haka da kansa zai yanke hukuncin”.
Yanzu haka dai jam’iyyar NNPP mai mulki a Kanon na fama da rikici, musamma a ɓangaren ƙungiyar Kwankwasiyya da tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ke jagoranta, inda wasu ‘jiga-jigai suka ce sun fita daga cikinta.

Asalin hoton, Katsina State Government
Gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ƙaddamar da sabbin rukunin jami’an tsaro na da ake kira KTS C-Watch.
Dakarun tsaron unguwannin 550 su ne kashi na biyu da Gwamna Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar a yau Juma'a da zimmar yaƙi da 'yanfashin daji masu sacewa da kashe mutane haka kawai.
"Mun ɗauki mutum 6,652 domin daƙile matsalar tsaro. Sannan mun nemi masu gari, da limamai, da ladanai, tare da ba su albashi a matsayin wani ɓangare na shirin samar da tsaro a unguwanni," a cewar gwamnan.

Asalin hoton, Katsina State Government

Asalin hoton, Katsina State Government

Asalin hoton, Reuters
Shugabar Mexico Claudia Sheinbaum ta ce Donald Trump ya taɓo batun iyakar ƙasar da Amura lokacin da suka yi magana ta waya ranar Alhamis.
"Ya yi maganar iyaka. Na faɗa masa cewa e tabbas akwai batun iyakar, amma ya kamata a samu lokacin tattaunawa kan hakan," kamar yadda ta faɗa wa manema labarai.
Wannan ne karon farko da shugabannin suka yi magana bayan zaɓensa a matsayin shugaban ƙasa.
sai dai Ministan Harkokin Wajen Mexico Juan Ramon de la Fuente ya ce tsarin su na kula da kan iyaka na aiki yadda ya dace kuma ba za su sauya ba.

Asalin hoton, Reuters
Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba shi da wani zaɓi "da ya wuce" korar dubun dubatar baƙin haure da ba su da izinin zama a ƙasar.
Cikin wata tattaunawa da NBC ranar Alhamis, shugaban ya ce: "Ba magaanr abin da za mu samu ko rasawa ba ce. Ba haka ba ne - ba mu da wani zaɓi ne. Idan ana kashe mutane, jagororin 'yanƙwaya na lalata ƙasashe, to yanzu za su koma ƙasashensu saboda ba za su zauna mana a nan ba."
Ko da gwamnatin ta yi nasarar koro baƙin a hukumance, to za ta sha fama wajen yadda za ta aiwatar da hakan. Ƙwararru na ganin hakan zai laƙume biliyoyin dala kafin a iya mayar da mutum miliyan ɗaya gida.
A shekarar 2021 aka dakatar da shirin kai samame kan wuraren ayyukan baƙin, wanda gwamnatin Trump ta aiwatar.
Adadin mutanen da ake kamawa a cikin Amurka tare da mayar da su ƙasashensu bai wuce 100,000 ba cikin shekara 10, amma sun kai har 230,000 a shekara a farkon mulkin Barrack Obama.

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin Turai da ke gudanar da taro a birnin Budapest na shirin kaddamar da wani tsari da zai inganta goggayarsu kafin zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya shiga ofis.
Suna ta nazari kan wasu jerin daftari har 170 da masana tattalin arziki daga Italiya suka samar da hadin gwiwar tsohon Firaminista Mario Draghi.
Babban abin da ake ganin zai iya zame musu cikas shi ne inda za a samar da kudaden aiwatar da shirin - shin daga asusun kasashen ne ko hukumar Tarayyar Turai? Da kuma ko abu ne da za su iya neman rance daga kasuwannin duniya?.
Mista Draghi dai ya yi gargadin cewa muddin suka tsaya sanya to makomarsu na cikin hadari.

Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf
A jihar Kano, wacce ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya, gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2025 a gaban majalisar dokokin jihar.
Kasafin kuɗin na bana wanda shi ne na biyu da gwamnan ya gabatar ya kai fiye da naira biliyan 500B.
Duk da kasancewar jihar cibiyar harkokin kasuwanci amma ta na sahun gaba wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, abin da ya sa gwamnati ta ware fiye da kashi 31 na kasafin ga ilimi.
Ma'aikatu da kuɗin da aka ware musu:

Asalin hoton, GODWIN OBASEKI/FACEBOOK
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ce ya samu labarin cewa EFCC za ta kama shi da zarar ya miƙa mulki a makon gobe.
Sai dai gwamnan ya ce ko kaɗan shi ba ya tsoro ko fargaba domin za a bincike shi a game wa'adin gwamnatinsa, kamar yadda jaridar Thisday ta ruwaito shi yana faɗa a taron EdoBEST da aka yi a Abuja.
"Na samu labarin cewa EFCC za ta kama ni makon gobe. Duk inda suka ajiye ni, zan yi amfani da damar domin gudanar da bincike.
"Mun yi aikace-aikace muhimmai, sannan mun ba mutanen jihar Edo da abubuwan da suka fi buƙata muhimmanci. Don haka me zai sa in yi fargaba? na yi abin da zan iya yi, amma za su iya zuwa su ci gaba da bi-ta-da-ƙullin da za su yi, wannan matsalarsu ce."

Asalin hoton, Twitter/@benmurraybruce
Gwamnatin Najeriya ta ce tana yabawa da jajircewar ƴan ƙasar a daidai wannan lokaci da ake fama da matsaloli a sanadiyar gyare-gyaren inganta tattalin arzikin ƙasar da suka ɓullo da su.
Ministan kuɗi da tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasar, Wale Edun ne bayyana hakan a lokacin da yake yi wa kwamitin harkokin kuɗi na Majalisar Dattawa jawabi, kamar yadda tashar talabijin na Channels ta ruwaito.
Ya ce an kusa gama da shan wahalar, domin a cewarsa an fara ganin nasara a gyare-gyaren da aka ɗauko.
"Manyan gyare-gyaren guda biyu su ne farashin man fetur da kuɗaɗen ƙasashen waje sun an fara ganin haske. Ina ganin akwai buƙatar mu yanawa jajircewar ƴan Najeriya bisa abubuwan da suka jure domin samun wannan nasarar."
A nasa ɓangaren, shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa sun zauna ne domin sanin ko gyare-gyaren da aka ɗauko suna aiki, ko akasin haka.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƙasar Iran Masoud Pazeshkian ya ce ƙasar ba ta damu da ko wanene ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka kammala a Amurka ba.
Sai dai kuma gwamnatin Iran ɗin ta kira nasarar Donald Trump da wata dama ga Amurka ta nazarin abin da ta kira manufofinta marasa kyau na baya, domin ta gyara.
Donald Trump dai ya dauki matakai tsaurara kan kasar ta Iran lokacin wa’adin mulkinsa na farko.
Gwamnatin Najeriya ta bayar da sanarwa cewa daga yanzu kyauta za a riƙa wa mata tiyatar haihuwa, wato Cesarean Sections, a duk faɗin ƙasar.
Ana ganin wannan al'amarin a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata wajen haihuwa.
Haka kuma a wani gefen, ana tunanin matakin zai taimaka wajen magance wahalhalu, da kashe maƙudan kuɗaɗen da ake fama da su yayin duk da ake buƙatar yi wa mace tiyatar ta haihuwa.

Asalin hoton, PDP
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce za su yi duk mai yiwuwa domin su gyara jam'iyyar PDP, domin ita ce za ta gyara Najeriya.
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a lokacin ƙaddamar da kwamitin gwamnoni na jam'iyyar, da kuma fitar da tsare-tsaren cibiyar Peoples Democratic Institute (PDI), wadda cibiya ce ta bincike da aka assasa tun a shekarar 2000 domin bincike da tattara bayanai da horarwa da sauransu, kamar yadda jaridar The Nation ta kalato daga kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN.
Makinde ya ce jam'iyyar ce za ta iya gyara Najeriya, inda ya ƙara da cewa, "za mu gyara PDP, ita kuma sai ta gyara Najeriya."
Ya ƙara da cewa, "a yanzu da muka fara fuskantar 2027, akwai buƙatar PDP ta samar wa ƴan Najeriya wata damar daban. Ƙasarmu na buƙatar gyara da tsari mai kyau. Ƴan Najeriya na jiran PDP ta kawo musu wani zaɓin," in ji shi, inda ya ƙara da cewa tun a 1999 yake cin moriyar PDP, sannan ya ce ba zai so ya gurɓata rijiyar da ya sha ruwa a ciki ba.
A nasa jawabin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya nanata buƙatar da ke akwai na haɗin kai a PDP.

Asalin hoton, EPA
Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa yunwar da ake fama da ita a Najeriya zai iya tsananta a shekarar 2025, inda aka yi hasashen cewa aƙalla mutum miliyan 33 ne za su iya shiga yunwa a shekarar ta baɗi.
Ƴan Najeriya a yanzu sun kai kusan miliyan 223.8.
A rahoton, wanda Cadre Harmonisé ta yi a ƙarƙashin kulawar gwamnatin tarayya, da haɗin gwiwar shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ne ya bayyana hakan, inda rahoton ya yi hasashen cewa ƴan ƙasar aƙalla miliyan 33.1 ne za su fuskanci yunwa.
Rahoton ya ta'allaƙa hasashen ne kan yanayin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar da hauhawar farashin kayayyaki da sauyin yanayi da rikce-rikice a wasu yankuna na arewacin ƙasar.
Rahoton ya ƙara da cewa tsakanin Oktoba zuwa Disamban 2024, kimamin mutum miliyan 25.1 ake hasashen za su yi fama da yunwa, duk da cewa lokaci ne na kakar girbin amfanin gona.

Asalin hoton, ORTN
A jamhuriyar Nijar, a yankin Tillabéri, yara 53,562 ne ba sa zuwa makarantata dalilin rashin tsaro duk da kasancewar jami’an tsaro na (FDS) da kuma sintirin da suke yi a yankini.
A Torodi kaɗai rahotani sun ambato cewa sama da makarantu 100 ne aka rufe a dalilin matsalar rashin tsaron.
Yankunan kan iyaka da Nijar da Burkina Faso ne suka fi fama da wannan matsalar, yankunan da ke ci gaba da fuskantar barazanar hare-hare daga ƙungiyoyin masu da’awar jihadi.
Sai dai kuma dakarun tsaron ƙasar na ƙoƙari wajen ganin kwanciyar hankali da zaman lafiya sun dawo da za su bada damar cigaba da karatu a yankunan.

Asalin hoton, Daily Trust
A jihar Kano, ƙungiyar likitoci ta umarci likitocin jihar su koma bakin aiki bayan janye yajin aikin da aka wayi gari da shi a asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad a ranar Alhamis.
Likitocin dai sun shiga yajin aikin ne bayan cikar wa’adin sa’o’i 48 da ƙungiyar ta baiwa gwamnan jihar, na ya kori kwamishiniyar jin ƙai ta jihar, Amina Abdullahi HOD, bisa zargin cin zarafin wata likita a asibitin, zargin da ta ce musanta. Duk da cewa likitocin sun janye yajin aikin amma ƴan sa’o’in da aka shafe babu likitoci a asibitin na Murtala Muhammad har an ga tasirinsa, inda ya shafa majinyata.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya taya Donald Trump murnar lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka, inda ya kwatanta shi da "jajirtaccen mutum."
Putin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taro a birnin Sochi, inda ya ƙara da cewa Trump ya sha "gwagwarmaya daga ɓangarori da dama," a hanyarsa ta samun nasara.
Sai dai Putin ya ce ikirarin da Trump ya yi cewa zai kawo ƙarshen yaƙin Rasha a Ukraine, "abun dubawa ne matuƙa."
Da aka tambaye shi ko a shirye yake ya tattauna da Trump, Putin ya ƙara da cewa, "a shirye muke mana."
Tun da farko, shi ma Trump ya bayyanawa kafar NBC News cewa zai gana da Putin a game da yaƙin.

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da ɓullar ƙungiyar lakurawa waɗanda suke tayar da zaune tsaye a tsakanin jihohin Sokoto da Kebbi.
Daraktan watsa labarai na hedkwatar ne ya tabbatar da hakan a Abuja, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito, inda ya ƙara da cewa suna da tabbacin ɓullar ƙungiyar a Sokoto da Kebbi.
Sai dai ya ƙara cewa ƙungiyar ba za ta yi wani tasiri ba, domin a cewarsa sojojin Najeriya a shirye suke, kuma za su ga bayansu cikin ƙanƙanin lokaci.
Lakurawa wata ƙungiya ce ta ƴanbindiga da suka fara addabar mutanen Sokoto da Kebbi, kuma sun fito ne daga ɓangaren yankin Sahel da ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.

Asalin hoton, Reuters
Rundunar ƴansandan Netherland ta kama mutum 57 a birnin Amsterdam bayan wani rikici da ya ɓarke tsakanin magoya bayan ƙwallon ƙafa ƴan Isra'ila da wasu magoya bayan mutanen Falasɗinu.
Firaiminista Dick Schoof ya yi Allah wadai da lamarin, sannan firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce sun tura jarage biyu zuwa Amsterdam domin kwaso mutanen ƙasar, sannan rundunar sojin ƙasar ta ayyana rikicin da "mummunan hari a kan Isra'ila."
Kakakin rundunar ƴansandan ƙasar, ya shaida wa kafafen sadarwa cewa rikicin ya auku ne dandalin Dam da ke babban birnin ƙasar, amma bai bayyana asalin maƙasudinsa ba.
Magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Maccabi Tel Aviv ta Isra'ila sun je Amsterdam ne domin kallon wasan ƙungiyar da ƙungiyar Ajax.
Rikicin ya ƙara zafi ne bayan wasan, inda wani faifan bidiyo da aka riƙa yaɗawa a kafofin sadarwa aka nuna wani mutum ana dukarsa har ya faɗi a ƙasa. Wani bidiyon kuma an ga wani ya faɗi ana ta tattaka shi, sannan ana jin wasu na rera waƙoƙin goyon bayan Falasɗinawa.