Al'ummomi da dama ne a jihohin Kaduna da Zamfara ke zaune cikin duhu sakamakon rufe hanyoyin wutar lantarki da ma’aikata na kamfanin samar da wutar lantarki na Kaduna wato Kaduna Electric suka yi.
Ma’aikatan dai sun ce sun ɗauki matakin ne don nuna rashin jin daɗin su akan korar ma’aikata 900 da hukumomin kamfanin suka yi ba tare da biyansu hakkokin su ba.
Matakin ɗauke wutar lantarkin ya haddasa wahalhalu ga dubban masu sana’o’i waɗanda ke dogaro da wutar lantarkin wajen gudanar da harkokin su.
Auwalu Mai nama bakin Kawo Road a jihar Kaduna ya bayyana wa BBC yadda matsalar ta jefa su cikin takaici.
''Wannan rashin wuta ta haifar mana da mummunar hasara, ga nama nan da yawa an fito da shi ya lalace, ga kifi nan shi ma an tafka hasararsa, kayan ciki da kai da ƙafa, mun yi hatsara ba ƙarama ba''.
Shi kuwa Muftahu mai sana'ar ɗinki ya ce ya shafe tsawon kwana uku bai yi aiki ba, saboda rashin wutar lantarkin.
''Akwai ɗinkunan biki da za a yi amfani da su daga Juma'a da Asabar, amma yanzu haka kayan na nan ajiye ban ɗinka ko kala guda ba, na kunna inji na saka galan guda, amma ko rabi ban yi ba ya ƙare ''.
Shi ma Jamilu Idris mai sana'ar walda a birnin Kaduna ya shaida wa BBC yadda matsalar ta shafi sana'ar tasa.
''Ga ayyuka birjik a ƙasa, amma saboda rashin wutar dole sai dai mu haƙura, ɗan abin da muka ajiye don inganta sana'ar tamu, a yanzu shi muke ci'', kamar yadda ya bayyana.
Ma’aikatan kamfanin na Kaduna Electric, sun ce za su maido da wutar ne kawai idan kamfanin ya yi abin da ya dace na biyan mutanen da ya sallama haƙƙokinsu, idan ma ba zai mayar da su aikin ba.
A nasa ɓangare kamfanin na Kaduna Electric cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ma'aikata 450 ne ya sallama, ba 900 ba kamar yadda ƙungiyar ma'aikatan ke iƙirari, kuma ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon matsalar rashin kuɗi da kamfanin ke fuskanta.
Haka kuma kamfanin ya bai wa mutane haƙuri sakamakon kwanaki da suka ɗauka ba tare da wutar lantarkin ba.