Ukraine ta ce Rasha ta mata luguden wuta duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
Ma'aikatar tsaro a Ukraine, ta ce Rasha ta ƙaddamar da harin bama-bamai kusan 100 a yankin Sumy, tun bayan fara aikin jarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana uku da ta fara aiki a daren jiya Laraba.
Kawo yanzu babu cikakken bayani kan ko an fafata da sojojin ƙasashen biyu, sai dai sararin samaniyar Ukraine ya kasance shiru ba kamar yadda aka saba gani a baya ba.
Hukumomin Ukraine sun yi amanna Rasha ta ɗauki matakin tsagaita wutar ne domin faretin sojinta, a daidai lokacin da shugaba Zalensky ya ce idan da gaske Putin ya ke a dakatar da wutar na tsahon wata guda.