Labarai daga duniyar wasanni na 27/06/2024

Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 27 ga watan Yuni, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Euro 2024: Muhimman abubuwa 10 da suka faru a zagayen rukuni, Euro 2024

    Georges Mikautadze

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Georges Mikautadze na Georgia ne kan gaba a cin ƙwallaye da guda uku

    Yayin da aka kammala wasannin zagayen rukuni a gasar Euro 2024 jiya Laraba, tawagogi 24 sun buga wasa 72 a tsakaninsu.

    Daga cikinsu 16 sun yi nasarar kaiwa zagaye na biyu kuma na sili ɗaya ƙwala.

    Ga wasu daga cikin alƙaluma na abubuwan da suka faru a zagayen:

    • An buga wasa 72
    • An ci ƙwallo 81
    • Sifaniya ce kaɗai ta ci wasanninta uku
    • Sifaniya ce kaɗai ba a zira wa ƙwallo a raga ba
    • Jamus ta fi kowace tawaga cin ƙwallaye (8)
    • Jamus da Portugal ne suka fi kowace tawaga yawan riƙe ƙwallo a wasa, inda suka riƙe jimillar kashi 64.3 na ƙwallon
    • Georges Mikautadze na Georgia ne kan gaba a cin ƙwallaye (3)
    • Cristiano Ronaldo ne ya fi kowa yawan yunƙurin cin ƙwallo (12)
    • Romelu Lukaku na Belgium ne ya fi kowane ɗan wasa ɓarar da babbar dama (6)
    • Giorgi Mamardashvili na Georgia ne ya fi kowane gola hana ƙwallo shiga raga bayan ya kare 20
  2. Attajirin Georgia ya yi wa tawagar ƙasar kyauta bayan doke Portugal

    Georgia

    Asalin hoton, Reuters

    Bidzina Ivanishvili, tsohon firaministan Georgia, ya yi alƙawarin bai wa tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar kyautar fan miliyan 8.4 bayan sun yi bajintar doke Portugal a gasar Euro 2024.

    Georgia wadda tsohon ɗan wasan Faransa Willy Sagnol ke jagoranta, ta baje Portugal ne a jiya Laraba domin samun gurbi a zagayen 'yan 16, inda za su buga da Sifaniya.

    Ivanishvili wanda ya kafa jam'iyyar Georgian Dream kuma ya zama firaminista a 2012, ya ce nasarar a kan Portugal "abar tarihi ce kuma wadda aka daɗe ana buri".

    Attajirin ya kuma ce zai ba wa tawagar ƙarin fan miliyan 8.4 (Lari miliyan 30 kuɗin ƙasar) idan suka sake doke Sifaniya.

    A ranar Lahadi ne Georgia za ta fafata da Sifaniyan a filin wasa na Cologne da ke Jamus da misalin ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya da Nijar.

  3. Euro 2024: Jadawalin fafatawar zagayen 'yan 16

    Euros

    Asalin hoton, PA Media

    Bayan kammala wasannin cikin rukuni a gasar kofin ƙasashen Turai, hukumar ƙwallon ƙafa ta Uefa ta fitar da jadawalin karawar zagayen sili ɗaya ƙwala.

    Alhamis da Juma'a ranakun hutu ne a gasar, inda za a ci gaba da gumurzu ranar Asabar.

    Ƙasashen da za su buga zagayen su ne:

    • Switzerland v Italy - Asabar, 29 ga watan Yuni (5:00)
    • Germany v Denmark - Asabar, 29 ga watan Yuni (8:00)
    • England v Slovakia - Lahadi, 30 ga watan Yuni (5:00)
    • Spain v Georgia - Lahadi, 30 ga watan Yuni (8:00)
    • France v Belgium - Litinin, 1 ga watan Yuli (5:00)
    • Portugal v Slovenia - Litinin, 1 ga watan Yuli (8:00)
    • Romania v Netherlands - Talata, 2 ga watan Yuli (5:00)
    • Austria v Turkey - Talata, 2 ga watan Yuli (8:00)

    Duka lokutan agogon Najeriya ne da Nijar da Kamaru da Chadi.

    Jadawalin Euros
  4. Maraba

    Kun shigo shafin labarin wasanni tare da Umar Mikail a wannan rana ta Alhamis.

    Ku biyo ni domin sanin abubuwan da ke faruwa a duniyar wasannin, musamman game da gasar Euro 2024 da kuma Copa America.