Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 24/06/2024.

Taƙaitattu

  • Ana yi mana zagon ƙasa a harkar man fetur - Dangote
  • An kusa kawo ƙarshen luguden wuta da ake yi a Gaza - Netanyahu
  • Aƙalla mutum 16 sun mutu a wata gobara a Koriya ta Kudu
  • Cin bashin da ƴan Najeriya ke yi ya ƙaru saboda matsin rayuwa – CBN
  • An ƙaddamar da taro kan rashin tsaro a Najeriya
  • Ƴansanda sun kori ƴandaba da mafarauta daga fadar Kano

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, A'isha Babangida, Umaymah Sani, Ahmed Bawage

  1. Cin bashin da ƴan Najeriya ke yi ya ƙaru saboda matsin rayuwa – CBN

    Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da rahoton cewa, ƴan Najeriya sun koma cin bashi daga bankuna da manhajojin karɓar bashi saboda tsananin tsadar rayuwa domin samun biyan buƙata.

    CBN ya ce an samu ƙaruwar masu ciyo bashi da kashi 12 cikin 100, inda ya kai kusan tiriliyan ₦3.9 a watan Janairun 2024.

    An danganta wannan ƙaruwar ciyo bashin da hauhawar farashin kayan masarufi.

    Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ruwaito cewa hauhawar farashin kaya ya kai kashi 33.95 cikin 100 a watan Mayu.

    Hakan ya sa babban bankin ƙasar ya ƙara yawan kuɗin ruwa a jere zuwa kashi 26.25 bisa 100.

    Hauhawar farashin kaya ya jefa ƴan Najeriya cikin wani mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya ƙara tsadar rayuwa.

    Wani bincike da SBM Intelligence ya gudanar ya nuna cewa kashi 27 cikin 100 na 'yan Najeriya masu yawan samun kudin shiga daban-daban a yanzu sun dogara ne ga manhajojin ƙarbar bashi domin gudanar da abubuwan rayuwa yayin da ake fama da hauhawar farashin kaya.

    Ƙaruwar buƙatun ciyo bashi ta hanyar manhajar ƙarbar bashi ko kuma daga bankuna yana nuna tsananin tasirin hauhawar farashin kaya ga ƴan Najeriya, musamman waɗanda ke da ƙarancin kuɗi.

  2. An kusa kawo ƙarshen luguden wuta da ake yi a Rafah - Netanyahu

    Firaiminista Benjamin Netanyahu ya ce an kusan kawo karshen luguden wutar da ake yi a birnin Rafa da ke kudancin Gaza, amma zai ci gaba da yaki da Hamas sai sai sun kauda ta daga madafun iko.

    Netanyahu ya ce: "Bayan kammala wannan, za mu samu damar nausa dakarunmu zuwa arewaci, za mu yi hakan, sannan za mu dawo da mazauna yankunan arewaci da kudanci da aka kwashe, ta amfani da dabarun diflomasiyya".

    A bangare guda ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant, ya isa birnin Washington na Amurka, domin tattaunawa kan yakin Gaza da tashin hankali tsakaninsu da kungiyar Hezbollah ta Lebanun.

  3. Barka da warhaka!

    Barkan ku da zuwa shafin labaran BBC Hausa kai-tsaye na ranar Litinin 24 ga watan Yunin 2024.

    Monday tushen aiki...

    Za ku iya yin tsokaci kan labaranmu a shafin facebook, X da kuma Instagram.

    Da fatan za ku kasance tare da mu.