Ƙarshen rahotonni
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Asabar.
Za mu kawo muku wasu rahotonni gobe da safe a wani shafin daban.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 1/11/2025
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Asabar.
Za mu kawo muku wasu rahotonni gobe da safe a wani shafin daban.

Asalin hoton, EPA
Babbar jam'iyyar hammayya ta Tanzania Chadema ta kira nasarar zaben da Shugaba Samia Suluhu ta samu a matsayin ba'a ko muzanci ga zaben.
Mai magana da yawun jam'iyyar ya ce kamata ya yi a samu wata hukuma ta gaskiya da aka yarda da ita ta shiga lamarin tare da gudanar da sabon zabe.
Kakakin ya ce jami'an tsaro sun kashe mutum 800 da ke zanga-zanga kan yadda aka yi zaben, alkaluman da gwamnati ta yi watsi da su da cewa an yi karin gishiri sosai.
Wakiliyar BBC ta ce majiyoyin diflomasiyya sun ce an kashe daruruwan mutane a lokacin tashin-tashinar.
Da take karbar takardar shedarta ta cin zaben, Shugaba Suluhu ta ce: "Masu zanga-zangar ba su san yakamata ba kuma ba masu kishin kasa ba ne - kuma abu ne da kowa ya gani cewa 'yan Tanzania sun yi gamganko sun zabi shugaba mace."

Asalin hoton, Reuters
Ana samun rahotanni masu karo da juna daga birnin Pokrovsk da ake fafata yaƙi tsakanin dakarun Rasha da na Ukraine - wanda ke yankin Donestsk a Ukraine ɗin.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce an yi wa sojojin Ukraine ƙawanya a yankin, har ma sun fara zubar da makamansu suna mika wuya, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin Rashar ta ruwaito.
Ita kuwa rundunar sojin Ukraine cewa ta yi ta samu ci gaba a inda dakarunta suke a wasu gundumomi na birnin mai matukar muhimmanci.
Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce tsaron birnin abu ne da suke bai wa fifiko, yayin da rahotanni ke cewa Ukraine din ta tura zaratan sojojinta na musamman yankin.

Asalin hoton, EPA
Da alama tsarin mulkin dimokutradiyya na gaskiya - Liberal Democracy a Turance - da ya ƙunshi jam'iyyu, da zaɓuka, da 'yancin ƙungiyanci, yana fuskantar matsala a nahiyar Afirka.
Daga cikin ƙasashe 55 na nahiyar, 28 na da shugabannin kama-karya amma waɗanda aka zaɓa, 12 ba zaɓaɓɓu ba ne, 13 ne kacal ke da cikakken tsarin zaɓe, sai kuma biyu kacal (Seychelles da Afirka ta Kudu) da aka yi imanin su ne ke bin cikakken tsarin dimokuraɗiyya, kamar yadda cibiyar V-Dem Institute ta bayyana mai nazarin kan harkokin mulkin dimokuraɗiyya.
V-Dem cibiya ce da ke nazari da bincike a ƙasar Sweden. Takan fitar da bayanai kan dimokuraɗiyya mafiya girma game da dimokuraɗiyya a ƙasashe 202 tun daga 1789 zuwa 2024.
Ta fitar da jerin ƙasashen Afirka 15 da suka kwatanta tsarin dimokuraɗiyya na gaskiya.
Ga cikakken labarin a nan: Ƙasashen Afirka 15 da suka fi kwatanta dimokuraɗiyya ta gaskiya

Asalin hoton, Brandon Drenon/BBC
Al'ummar yankunan da guguwar Melissa ta ɗaiɗaita sun faɗa wani irin mugun hali na buƙatar agajin gaggawa.
An hango mutanen suna kutsawa cikin kantunan da guguwar ta lalata suna wawason abinci da abin sha da sauran kayayyakin buƙata.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin zaƙolu waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Mazauna yankunan sun ce kwana uku ke nan suna cikin tashin hankali da damuwa, kamar yadda suka shaida wa BBC.
Sun ce ba su ga ko tirela ɗaya ta kayan agaji ba, inda suka ce dole sun koma roron abinci a cikin baraguzan gini suna ci.
"Dole mu yi amfani da duk abin da muka gani ko dai a titi ko a kantuna," in ji wani mai suna Demar Walker.
Ya ce shi ma sai da ya tsallaka cikin wani katafaren kantin sayar da kayayyaki, sannan ya ɗebo abin da zai iya ɗebowa, sannan ya wurga wasu kayayyakin zuwa ga waɗanda suke waje.
Sai dai wasu sun ce ana karya doka wajen wawushe shaugnan mutane a yankin Black River.
"Mutane suna fasa shagunan mutane suna kwashe kayayyaki," in ji wani mai suna Aldwayne Tomlinson.

Asalin hoton, PDP
Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP ta dakatar da babban sakatarenta, Sanata Samuel Anyanwu, wanda na hannun damar Ministan Abuja Nyesom Wike ne.
Bayan Anyanwu, jam'iyyar ta dakatar da wasu shugabanninta da ake ganin suna da alaƙa da tsohon gwamnan na jihar Rivers.
Sakataren yaɗa labaran PPD na ƙasa Debo Ologunagba ya ce jam'iyyar ta yanke shawarar dakatar da mutanen ne tsawon wata ɗaya bayan taron gaggawa na kwamatin gudanarwa da ta yi yau Asabar.
Sauran waɗanda aka dakatar su ne babban lauyan jam'iyyar Kamaldeen Ajibade SAN, da sakataren tsare-tsare Umar Bature, da mataimakin babban lauya.
Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan wata kotu a Abuja ta dakatar da PDP daga gudanar da babban taronta na ƙasa da ta shirya gudanarwa a birnin Ibadan na jihar Oyo a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba.
Sai dai jam'iyyar ta ce za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta na taro a daidai lokacin da ta ɗaukaka ƙara.

Asalin hoton, Reuters
Rundunar sojin Isra'ila ta ce sassan jikin da Hamas ta mayar mata guda uku ba sa cikin gawarwakin da take garkuwa da su.
Isra'ila ta ce sun gano haka ne bayan binciken ƙwaƙwaf da masananta suka yi, inda suka gano cewa sassan jikin na wasu ne daban.
A ranar Juma'a ne dai Hamas ta miƙa wasu sassan jiki da ta ce gawarwakin mutum uku ne daga cikin Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su.
Daga cikin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka shiga, har da mayar da dukkan waɗanda ƙungiyar ta yi garkuwa da su, masu rai da marasa rai.
Zuwa yanzu dai Hamas ta miƙa mutum 20 masu rai da gawarwaki guda 17.
Sai dai har yanzu Isra'ila na nanata cewa dole Hamas ta miƙa dukkan gawarwakin da ke hannunta domin domin cika alƙawarin tsagaita wuta da aka shiga.

Asalin hoton, Andrew Holness/X
An shafe kwanaki cikin guguwar Melissa da ta yi barna a Jamaica, halin da ake ciki a dan karamin garin Black River ya kasance matsananci.
Gidajen mutane sun koma kufai sai tarkace, rayuwarsu na cikin matsanancin hali, inda mazauna yankin sun koma kamar masu yawon tsintar bola.
Wakiliyar BBC ta ce ba wai mutanen Black River kadai ba akwai wasu dubbai da suka koma suna tsintar kayayyaki a tarkacen shaguna. An ga Jiragen Amurka masu saukar ungulu - da ke nuna alamun samun agajin gaggawa nan ba da dadewa ba.
Goguwar Melissa, ta kasance daya daga cikin mafi muni da ta afka wa yankin inda ta kashe mutum sama da 50 a yankin na Caribbean.

Asalin hoton, Getty Images
Alkalai biyu biyu sun yanke hukuncin cewa gwamnatin Trump ba za ta iya dakatar da tallafin abinci ga miliyoyin Amurkawa ba sakamakon dakatar da ayyukan gwamnati.
Sun ce dole ne gwamnati ta yi amfani da kudade na gaggawa don biyan kudin tallafin na abinci.
Shirin yana ba da tallafi mai mahimmanci ga Amurkawa miliyan 42 masu karamin karfi.
Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan jam’iyyar Democrats da ‘yan Republican a majalisar dokokin kasar ke dora wa juna laifi kan dalilin dakatar da ayyukan gwamnati inda ake dab da shiga wata na biyu.

Asalin hoton, Reuters
Jami'an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan'adawa sun zarta haka.
Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce 'yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.
Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya sake zargin Amurka da kokarin kaddamar da yaki a kasarsa - a yayin da sojojin Amurka ke cikin shiri a yankin Caribbean.
Mr Maduro ya ce Washinton na son hambarar da gwamnatinsa ne domin kwashe arzikin man kasar.
Shugaba Trump da sakararen harakokin wajensa Marco Rubio sun musanta rahotannin cewa Amurka na shirin kadamar da hare-hare kan Venezuela.
Gwamnatin Trump ta nace cewa an girke sojoji ne domin yaki da masu safarar miyagun kwayoyi - amma ta zargi Mr Maduro a matsayin shugaban masu fataucin miyagun kwayoyi kuma Amurka ba ta amince da shi ba a matsayin halastacen shugaban Venezuela

Asalin hoton, PRESIDENCY NG
Gwamnatin Najeriya ta yi martani kan jawabin shugaban Amurka Donald Trump kan zargin kashe kiristoci a Najeriya.
Trump ya ayyana Najeriya a cikin ƙasashen da "yake da yake sa ido a kansu."
Ya ce kiristanci na fuskantar babbar barazana a Najeriya," in ji shi, inda ya ƙara da cewa ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata wannan kisan gillar. "Saboda haka na ayyana Najeriya ƙasar da ake da damuwa a kanta."
Bugu da ƙari, Trump ya ce ya bai wa 'yanmajalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin fara bincike kan hakan kuma su kai masa rahoton sakamakonsa.
A martanin da ya mayar, ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta ce lamarin ba haka ba ne.
A wata sanarwa da kakakin ma'aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ya ce, "duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da ƙasashen duniya ke ba ta musamman kan batun haƙƙin ɗan'adam da haƙƙin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a ƙasar ba haka ba ne. Duk ƴan Najeriya suna suna da ƴancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba."
Sanarwar ta ce a ƙarƙashin mulkin Tinubu, gwamnatinsa na ƙoƙari sosai wajen yaƙi da ta'addanci da ƙarfafa gwiwa da kare rayuwar al'umma ba tare da nuna bambanci.
Gwamnatin ta ce Najeriya za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka da ƙasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴanbindiga da ake zargin Lakurawa ne sun yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar jihar Kebbi Samaila Bagudo.
Rundunar ƴansandan jihar Kebbi sun tabbatar da aukuwar lamarin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ta ce ƴanbindigar sun auka gidan ɗanmajalisar ne da misalin bayan sallar Isha a hanyarsa ta komawa gida.
Kakakin rundunar CSP Nafiu Abubakar ya ce an tura jami'an tsaro yankin domin su ceto shi.
Rundunar ta sake nanata za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen kare rayuwa da dukiyar al'ummar.
Jama'a barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da sake saduwa a wannan safiya ta Asabar daga sashen Hausa na BBC.
Da fata za ku kasance tare da mu.