Bankwana
Masu bibiyar shafin kai tsaye na BBC Hausa, a nan muka kawo ƙarshen rahotannin na yau Lahadi.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/10/2024
Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Mukhtar
Masu bibiyar shafin kai tsaye na BBC Hausa, a nan muka kawo ƙarshen rahotannin na yau Lahadi.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an hukumar zaɓe a Tunusia, sun ce kashi kalilan cikin waɗanda shekarunsu ya kai kaɗa ƙuri'a ne suka shiga zaɓen shugaban ƙasa na ranar Lahadi.
Ana sa ran fadar adadin wadanda sukai zaben a hukumance, ko da ya ke ana sa ran adadin zai fi na kashi 11 cikin 100 na masu kada kuri'a a zaben 'yan majalisun da aka yi na bara.
Ana kallon zaɓen a matsayin wani mataki na shugaba Kais Sa'eed na ci gaba da zama kan madafun iko, la'akkari da yawancin abokan takara da hamayyarsa su na garƙame a gidan kaso, ko sun yi gudun hijira zuwa wata ƙasar.
Cikin shekaru 5 da suka gaba shugaba Kais ya mamaye da iko da daukacin Tunusia.
Isra'ila na cikin shirin ko ta kwana gabanin cika shekara ɗaya da harin da Hamas ta kai mata, wanda ya hallaka sama da Isra'ilawa 1200.
Mutane na ci gaba da tunawa da waɗanda suka rasu watanni 12 da suka gabata, inda ƴan uwa da abokan arziki ke kai ziyara inda aka kai harin ciki har da wurin kalankuwar mawaka na Nova inda aka fi zubda jini.
Firai ministan Benyamin Netanhayu ya gabatar da jawabi ga sojin Isra'ila yana mai cewa shekara ɗaya da ta wuce ƙasar ta shiga tashin hankali, kuma duniya ta shaida yadda suka maida martani.
Duk da matakan da aka ɗauka, wata ƴar sandan iyakar Isra'ila ta mutu kuma wasu 10 sun jikkata, a harin da aka kai kudancin garin Beersheba.

Asalin hoton, reut
Ƴan sanda a Afirka ta kudu sun kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan wasu ƴan uwa 18, a wani ƙauye, a makon jiya.
Ministan ƴan sanda Senzo Mchunu ya bayar da tabbacin kamen a wajen taron addu'oi ga mutanen 18 da aka kashe, a garin Lusikisiki, wajen da aka aikata kisan.
Ya kuma ce nan ba da jimawa ba za su sanar da ƙarin mutum daya da suke sa ran kamawa a game da kisan.
Jama'ar Afirka ta Kudu sun kaɗu da yadda wasu ƴan bindiga suka buɗe wuta kan gidaje biyu, suka kuma kashe mata 15 da kuma maza uku.
Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ce shekarun mutanen da aka kashen sun kama daga 14 zuwa 64.
Ƴan sandan sun ce za su gabatar da mutanen uku a gaban ƙuliya ranar Litinin.

Asalin hoton, EPA
Ƴan sanda a Pakistan sun ce sun kama mutane aƙalla ɗari tara daga cikin magoya bayan tsohon firaiministan ƙasar, Imran Khan, a rana ta biyu ta zanga-zanga a yankin Punjab.
An ci gaba da kama mutane a ranar Lahadi, inda ƴansanda suka ce an kashe jami'i ɗaya an kuma raunata wasu 30.
Hukumomi sun rufe hanyar da ta haɗa Islamabad da birnin Lahore, da sauran hanyoyin yankin.
Magoya bayan Imran Khan suna zanga-zanga ne domin nuna rashin jin daɗin su a game da ci gaba da tsare shi, da kuma jinkirin aiwatar da hukuncin kotun ƙolin ƙasar a kan kujerun majalisar dokoki.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyoyin fararen hula sun ce an kashe fararen hula aƙalla tara, an kuma raunata wasu gommai a rana ta biiyu ta hare-haren sojin Sudan.
A ranar Asabar sojin suka tarwatsa hanyar da ta haɗa babban birnin ƙasar, Khartoum da kuma yankin Darfur da ke ƙarƙashin ikon mayaƙan RSF.
Ƙungiyoyin fararen hula sun ce ko a ranar Juma'a, sojojin sun kashe fararen hula aƙalla 60 a arewacin Darfur.
Bidiyon da aka wallafa sun nuna aka tarwatsa kasuwar El Koma, da kuma gawarwaki da dama a ƙasa.
Sojojin na ƙoƙarin ƙwato yankin da mayaƙan na RSF suka ƙwace iko ne.
Mutane aƙalla miliyan goma yaƙin ya raba da muhallin su.

Asalin hoton, AA
Hukumar zaɓen mai zaman kanta ta jihar Rivers, RSIEC, ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar Action Alliance (AA), Uzodinma Nwafor, a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar Etche da ke jihar.
Rahotonni sun ambato shugaban hukumar zaɓn jihar, Adolphus Enebeli, na bayyana haka ranar Lahadi a binrin Fatakwal.
Mista Enebili ya ce jam'iyyar ta AA ta kuma cinye zaɓen duka kansilolin ƙaramar hukumar 19.
Tun da farko dai hukumar zaɓen jihar ta sanar da cewa jam'iyyar APP ta lashe zaɓen a ƙananan hukumomi 22 cikin 23 na jihar kafin a kammala tattara sakamakon ƙaramar hukumar ta Etche.
Nan gaba a yau ne gwamnan jihar, Siminalayi Fubaru zai rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Fatakwal.

Asalin hoton, MDA
An raunata wasu mutane da dama tare da kashe wata mata mai shekara 25 a wani harin bindiga da aka kai wata tashar mota a Isra'ila.
'Yansanda sun ce "suna sa ran harin ta'addanci ne" aka kai Beersheba a kudancin Isra'ila.
Jami'an lafiyar Isra'ila sun ce likitoci na duba mutum 10 da suka samu raunuka, inda wasu daga cikinsu suka samu raunin harbin bindiga.
'Yansanda sun ce an kashe maharin.

Asalin hoton, CBN
Gwamnatin Najeriya ta ce ƙasar ta fara sayar da ɗanyen mai da tataccen mai da kuɗin ƙasar wato naira.
Ministan kuɗi da tattalin arzikin na ƙasar, Wale Edun ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ma'aikatar kuɗin ƙasar, ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar.
Sanarwar ta ce an fara sayar da ɗanyen man da kuɗin naira ne tun daga ranar ɗaya ga watan Okotoban da muke ciki.
Ministan ya ce hakan na daga cikin matakin da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka da ake sa ran zai haɓa tattalin arzikin ƙasar da ci gaba da zaman lafiya da dogaro da kai.
Mista Edun ya ce Najeriya za ta ci gaba da bin matakan da suka dace, lura da halin da kasuwannin ɗanyen a duniya ke ciki wajen ciyar da ƙasar gaba.
Matakin na zuwa ne mako tara bayan majalisar zartarwar ƙasar ta amince da ƙudurin Shugaba Tinubu na umartar kamfanin NNPCL ta sayar wa matatar mai ta Dangote da sauran matatun cikin gida ɗanyen mai da kuɗin ƙasar wato naira.
Masu sharhi dai naganin matakin sayar da man da naira maimakon dala zai age farashin kuɗin ƙasar waje a ƙasa, lamarin da suke ganin zai karya farashin dala tare da rage hauhawar farashi a ƙasar.
Ministan Ilimi, Abbas halabi na Lebanon ya ce ƙasar za ta ɗage fara sabuwar shekarar karatu.
Mista Halabi ya ce yanzu za a fara sabuwar shekarar karatun ta bana za ta fara daga ranar 4 ga watan Nuwamba saboda matsalar 'Hatsarin tsaro'.
Kamfanin diallancin labarn Lebanon ya ambato ministan na cewa jami'o'i masu zaman kansu za su iya komawa karatu daga gobe Litinin la'akri da halin da makarantun nasu ke ciki.
Akwai ɗalibai fiye da miliyan guda a ƙasar, waɗanda a yanzu haka ke hutun ƙarshen zangon karatu
Wata ƙungiyar masu rajin kishin Islama a Iraƙi ta ce ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa uku a yankin Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye da safiyar yau, kamar yadda wata sanarwa da ƙungiyar Hezbollah ta fitar.
Ƙungiyar - wadda ke ƙawance da Hezbollah da sauran ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran - na adawa da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya.
A wasu lokutan waɗannan ƙungiyoyi na ayyana kansu da 'Dakarun Turjiya'
Kawo yanzu rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba game da rahoton, kuma ba a sani ba ko harin ya yi mata wata ɓarna.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban sojin Burkina Faso ya ce yana shirin ƙwace lasisin haƙar ma'adinai da aka bai wa kamfanonin ƙasashen waje domin bayar da su ga ƙungiyoyin haƙar ma'adinai na cikin ƙasar.
Captain Ibrahim Traore ya bayyana haka ne cikin wata hira da wani gidan radiyon ƙasar kan cikar juyin mulkin - da ya kai shi kan karagar mulkin ƙasar - shekara biyu.
Shugaban dai bai bayyana sunayen kamfanonin da zai ƙwace wa lasisin ba.
Kamfanonin haƙar ma'adinai na ƙasashen Australian da Birtaniya da Canada da kuma Rasha na daga cikin kamfanonin da yanzu haka ke aikin haƙar ma'adinin zinare a Burkina Faso.
Matakin na zuwa ne bayan makamancinsa a ƙasashen Mali na Jamhuriyar Nijar, waɗanda dukansu yanzu ke ƙarƙashin mulkin sojoji.
A duka ƙasashen uku an samun ƙaruwar ayyukan masu iƙirarin jihadi, lamarin da ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, yake kuma barazana ga ayyukan haƙar ma'adinai.
Rundunar sojin Isra'ila IDF, ta ce dakarunta sun kashe wani kwamandan ƙungiyar Hezbollah mai suna Khader Ali Tawil.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, IDF ta ce Khader ya yi aiki tare da wasu mutum biyu Muhammad Haidar da Hassan Nathir al-Ra'ini, da aka kashe farkon makon nan.
IDF ta ce mutanen uku ne suka jagorancin ƙaddamar da harin makami mai linzami da ya faɗa wa garin Kfar Yuval da ke kan iyakar arewacin Isra'ila a watan Janairu.
Harin ya yi sanadin mutuwar Barak Ayalon, wanda ke cikin tawagar masu bayar da agajin gaggawa na garin, tare da mahaifiyarsa mai shekara 76.
Kawo yanzu dai Hezbollah ba ta mayar da martani kan sanarwar sojojin na Isra'ila ba, tun bayan fitar da ita da safiyar yau.
Wani yaro matashi ya mutu bayan da aka caccaka masa wuƙa har fiye da sau 50 sannan aka cinna masa wuta a birnin Marseille na ƙasar Faransa.
Masu shigar da ƙara sun ce wani gungun masu safarar ƙwaya ne suka yi hayar yaron domin razanar da abokan faɗansu ta hanyar ƙona musu wani ɓangare na ƙofar shiga dabarsu, to amma sai suka ganshi inda nan take suka kashe shi.
Su ma ɗaya bangaren sun ɗauki hayar wani yaron domin kai harin ramuwar gayya, to amma sai ya samu saɓani da direban da ya ɗauke shi a mota, lamarin da ya sa ya kashe direban.
Birnin Marseille ya fuskanci rikice-rikice masu alaƙa da ƙungiyoyin 'yan daba masu safarar ƙwaya, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutum 50 a shekarar da ta gabata.

Asalin hoton, NUT
Ƙungiyar Malamai ta Najeriya NUT, ta kararrama wasu gwamnonin ƙasar shida kan abin da kira 'ƙoƙarinsu bunƙasa harkokin ilimi a jihohinsu.
An gudanar da bikin karramawar ranar Asabar a Abuja, babban binrin ƙasar, lokacin da ƙungiyar ta gudanar da bikin 'Ranar Malamai da Duniya'.
Gwamnonin da aka karrama a lokacin bikin sun haɗa da na Kano, Abba Kabir Yusuf, da na Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da na Oyo, Seyi Makinde da na Benue, Hyacinth Alia da na Enugu, Peter Mbah da kuma gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris.
Shugaban ƙungiyar NUT na ƙasa, Comrade Titus Ambe, ya ce an zaɓo gwamnonin ne la'akari da irin ƙoƙarinsu wajen bunƙasa fannin ilimi a jihohinsu, musamman tallafa wa malamai da samar da abubuwan ci gaba a fannin koyo da koyarwa a jihohinsu.
Cikin wata sanarwa da sakataren ya ɗa labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf - wanda ya yi jawabi a madadin sauran takwarorinsa gwamnonin shida, ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da bai wa fannin bunƙasa ilimi fifiko, saboda muhimmancinsa wajen ci gaban yara masu tasowa
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnan tarayya, Sanata George Akume ya yaba wa gwamnonin bisa jajircewarsu wajen bunƙasa fannin ilimi a jihohinsu.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun yi wa garin Jabaliya da ke arewacin Gaza ƙawanya, bayan da ta ce Hamas na ƙoƙarin sake farfaɗo da ƙarfinta a yankin.
Ta ce ta kai gomman hare-hare kafin dakarun nata su shiga yankin, ciki har da wanda ta kai kan rumbunan ajiye makamai da gine-ginen ƙarƙashin ƙasa na ƙungiyar.
Hamas ta ce aƙalla mutum 24 ne suka mutu bayan da ISra'ila ta kai harin Bom kan masallaci da makaranta a tsakiyar Gaza.
Sojojin na Isra'ila sun ce Hamas na amfani da ginin a matsayin sansaninta.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga cikin wakilan BBC da ke aiko da rahotonni daga birnin Beirut ya kira daren da ya gabata da ''mummunan daren hare-hare da birnin ya fuskanta'' tun fara yaƙi tsakanin Isra'ila da Hezbollah.
Hotuna da bidiyoyin da aka yaɗa da safiyar yau, sun nuna yadda yahaƙi ya mamaye saman birnin.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-haren ne kan maɓoyar mayaƙan Hezbollah.
Sojojin na Isra'ila sun kuma bayar da sabon umarni ga mazauna wasu yankunan birnin su fice, yayin da ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare kan gine-gine masu alaƙa da Hezbollah.
A can kan iyakar kudanci kuwa, sojojin Isra'ilar sun ce Hezbollah ta harba makaman roka 30 zuwa birnin Kiryat Shmona da ke arewacin Isra'ila, inda dama mafi yawan mazauna birnin sun tsere, yayin da Hezbollah ta ce mayaƙanta sun dakatar da sojojin Isra'ila daga wani yunƙurinsu na shiga wani ƙauyen Lebanon da asubahin yau Lahadi.

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Tunisiya na kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar da ake ganin ba makawa shugaban ƙasar mai ci, Kais Saied, ne zai yi nasara.
An dai ɗaure manyan masu sukar shugaban ƙasar - a wani mataki da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil-adama suka kira ''tuhume-tuhumen da aka kitsa'' - lamarin da ya sa a yanzu mutum biyu ne kawai ke takara da shugaban ƙasar.
Hukumar zaɓen ƙasar - da Mista Saied ta kafa - ta hana wasu fitattun 'yan siyasar ƙasar uku shiga zaɓen saboda abin da ta kira 'rashin cancanta'.
Majalisar dokokin ƙasar ta kuma cire wa kotu ikonta na warware rigingimun siyasa.
Abokan fafatawar Mista Saied a zaɓen na yau su ne Ayachi Zammel, wanda yanzu haka ke ɗaure a gidan yari saboda samunsa da laifin ƙarya a wasu takardun zaɓe, da kuma Zouhair Maghzaoui, wanda tsohon aboki ne ga shugaban ƙasar.
Kusan mutum miliyan 10 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen.

Asalin hoton, NYSC
Hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya NYSC ta ce dalilin da ya sa aka samu jinkirin fara biyan sabon ƙarin alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima, shi ne gwamnati ba ta sakar wa hukumar kuɗin sabon ƙarin ba.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban hukumar Birgediya Janar Yus'au Dogara Ahmed, ya ce a hukumance sun samu takardar amincewa da ƙarin, amma ba a riga aka sakar wa hukumar kuɗin ba.
''Ai ba ma su kaɗai ba, har ma'aikatan hukumarmu suma an yi musu ƙarin, su kan nasu ma ya kai kusan wata huɗu zuwa biyar, amma ba a fara biyansu ba, amma muna sa rai nan ba da jimawa ba, za a fara biya, amma bai riga ya zo hannunma ba tukunna'', in ji.
''Bayanin da muka samu ba a ce mana cewa yaushe za a fara biya ba, amma dai an tabbatar mana cewa an yi musu ƙari daga ranar 29 ga watan Yulin 2024'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
A cikin watan da ya gabata ne hukumar NYSC ta fitar da sanarwa yin ƙari a alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima daga naira 33,000 zuwa 77,000.
Sanarwar ta ce ƙarin sabon alawus ɗin zai fara aiki ne daga watan Yulin wannan shekarar, abin da ke nuna cewa masu yi wa ƙasa hidimar za su samu ariyas na aƙalla wata uku.
To sai dai da dama daga cikin masu hidimar ƙasar sun saka rai da ganin ƙarin a alawus ɗin a watan da ya gabata.
Jam'iyyar Action People’s Party (APP) ta lashe zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 22 cikin 23 na jihar Rivers da aka gudanar ranar Asabar.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta na jihar (RSIEC), Adolphus Enebeli ne ya bayyana sakamakon ranar Asabar da daddare a Fatakwal, babban birnin jihar.
Haka kuma, hukumar zaɓen ta dakatar da bayyana sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Etche, saboda a cewarta har lokacin ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar.
Shugaban na RSIEC ya kuma ce za a bayyana sakamakon zaɓen kansilolin duka mazaɓun jihar 319 tare da na shugaban ƙaramar hukumar Etche da zarar an kammala tattara sakamakon.
Tun da farko dai jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ta ce ba za ta shiga zaɓen ba, sakamakon umarnin wata kotu da ta hana gudanar da zaɓen, kodayake gabanin zaɓen uwar jam'iyyar ta ƙasa ta yi kira ga 'yan jam'iyyar su shiga zaɓukan.
Gwamnan jihar Siminalayi Fubara na takun-saƙa da tsohon gwamnan jihar, ministan Abuja Nyesom Wike, kan jagoirancin jam'iyyar PDP a jihar.
Rikicin nasu ya yi ƙamari ne lokacin da aka gudanar da zaɓen shugabannin jam'iyyar jihar, bayan da tsagin Wike ya samu a nasara kan tsagin Fubara, lamarin da ya sa magoya bayan Fubara suka fice daga PDP zuwa APP, inda suka yi takarar a can, shi kuwa Gwamna Fubara ya goyi bayansu.
Abin da masu sharhi ke kallon wani mataki ne na ficewar Fubara daga PDP, kodayake bai fitar da wata sanarwa a hukumance ta aniyar ficewa daga jam'iyyar ba.