Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi a kan Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya na ranar 29/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammad da Aisha Aliyu Jaafar

  1. 'Yadda na rasa hannuna ɗaya a wajen aiki'

    A ranar 28 ga Afrilu, ana bikin World Day for Safety and Health at Work domin tunatar da duniya cewa irin waɗannan haɗurra ana iya kauce musu.

    Wannan rana, wadda International Labour Organization ta assasa, na ƙarfafa muhimmancin kare ma’aikata daga haɗurran da za a iya hana farawarsu.

    Abubakar Hamza, wani tsohon ma'aikacin wani kamfani ne wanda ya rasa hannunsa ɗaya a lokacin da yake aikin gyara shinkafa.

  2. Amfani da cin zarafi a matsayin makamin yaƙi a Sudan na shafar lafiyar ƙwaƙwalwar mata -MDD

    Yadda ake yawaita amfani da fyade da sauran nau'ikan cin zarafin mata a matsayin makamin yaƙi a Sudan ya haifar da babbar matsalar ƙwakwalwa a tsakanin mata da 'yan mata.

    Asusun kula da yawan jama'a na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa nuna ƙyama da ƙarancin ƙwararrun ma'aikatan kiwon lafiya na kara ta'azzara lamarin.

    Jami'ai sun ce da yawa daga cikin waɗanda lamarin ya shafa na fama a matsalar ƙwaƙwalwar ba tare da sanar da kowa ba, kuma suna bukatar tallafi cikin gaggawa.

    Sukan fuskanci ƙalubale wajen samun kulawa, inda zuwa asibiti ke kasancewa abu mai hatari , yayin da rahotanni ke cewa wasu asibitoci na ƙarƙashin ikon ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

  3. Yadda IS ta kai mummunan hari a Adamawa

    Kalla bidiyon bayanin yadda IS ta kai mummunan hari a Adamawa

  4. Isra'ila na ci gaba da zafafa hare harenta a kudancin Lebanon duk da tsagaita wuta

    Isra'ila ta zafafa hare haren da take kai wa a kudancin Lebanon, inda ta ce tana kai harin ne kan sansanonin Hezbollah.

    Rundunar IDF ta ce ta kai hari kan wata hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Hezbollah a birnin Qantara mai tsawon Kilomita biyu, ta hanyar amfani da tan ɗari huɗu na abubuwan fashewa.

    Bidiyon da aka wallafa a intanet sun nuna yadda aka lalata birnin bakiɗaya, da yadda wuta da hayaƙi suka cika sararin samaniya.

    Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce hare haren Isra'ila na ci gaba da rutsawa da fararen hula da kuma ma'aikatan ceto.

    Ƙasashen biyu dai na ƙarƙashin wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tangal-tangal, wadda hare haren baya bayan nan ke barazanar sake raunata ta.

  5. Saurin da lalacewar dajin Amazon ke yi ya ragu a shekarar 2025 - Bincike

    Wani bincike da masana kimiyya na Amurka suka gudanar ya gano cewa saurin da lalacewar dajin Amazon ke yi ya ragu a shekarar 2025, bayan asarar da ba a taba samun irinta ba a tarihi a 2024.

    Masu binciken sun ce hakan ya fi nasaba da kokarin da ƙasar Brazil ta yi na dakile sare dazuzzuka a yankin Amazon.

    Sai dai binciken, wanda cibiyar World Resources Institute da kuma jami'ar Maryland suka gudanar ya kiyasta cewa har yanzu ana asarar kusan murabba'in kilomita dubu arba’in da uku na tsofaffin dazuzzukan.

    Wannan yanki ya yi daidai da girman ƙasar Denmark, ko kuma daidai da bacewar filayen ƙwallon ƙafa goma sha ɗaya a kowane minti.

    Binciken ya nuna cewa duk da cewa tsauraran dokokin kare muhalli na iya yin tasiri, har yanzu asarar filayen dazukan ta zarce wadda ake samu shekaru goma da suka gabata yawa.

    Masana kimiyyar sun kuma yi gargadin cewa ƙaruwar yanayin zafi na iya ƙara haddasa gobarar daji a ƙarshen wannan shekara.

  6. Mun ci galaba kan abokan gabanmu da ƙarfin soji - Trump

    A yayin da ya ke karɓar baƙuncin Sarki Charles na 3, Shugaban Amurka Donald Trump ya ɗan yi tsokaci game da rikicin Gabas ta Tsakiya, inda ya ce Amurka na ‘ƙoƙari’ a yaƙinta da Iran.

    ‘’ Mun ci galaba kan abokan gaban mu da ƙarfin soji’’ in ji shi, ba tare da ambato Iran ba.

    Ya kuma ƙara da cewa ‘’ ba za mu taɓa bari abokan gaban mu su mallaki makaman nukiliya ba, Charles ma ya yarda da hakan, fiye ma da ni’’.

  7. Yan sanda sun kama wanda ake zargi da shirya harin bom mafi muni a Colombia

    Yan sandan Colombia sun ce sun kama wani uban daba da ake zargi da shirya harin bom mafi muni da aka kai wa fararen hula a ƙasar cikin shekaru da dama.

    A ranar Asabar ne mutane 21 suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a harin da aka kai kan wata babbar hanya a kudu maso yammacin Colombia.

    Wakilin BBC ya ce sojojin Colombia sun haɗa kai da ’yan sanda a wani samame da suka kai domin cafke José Vitoncó a birnin Palmira da ke yammacin ƙasar.

    Shugaban ƙasar, Gustavo Petro, ya bayyana harin a matsayin “na ta’addanci”, yana mai cewa wata ƙungiyar masu safarar hodar iblis ce ta kai shi, wadda ke da alaƙa da Iván Mordisco, wanda ake nema ruwa a jallo a ƙasar.

  8. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da kasancewa damu a shafinmu na BBC hausa kai tsaye na yau Laraba.

    Kamar dai yadda aka saba wannan shafi ne da zai kawo muku labarai na abubuwan da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, da Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance tare da mu, kuma za ku bibiye mu a shafukan mu na sada zumunta kamar Facebook, X, Instagram da kuma YouTube domin kallon bidiyo da tafka muhawara.