Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/01/2026

Wannan shafi ne da kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 21 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • An fitar da sunayen mutanen da aka sace a Kaduna
  • An yanke wa tsohon firaminstan Koriya ta Kudu hukuncin ɗaurin shekara 23
  • Sojojin sun gano makeken kabarin ƴan Boko Haram a yankin Timbuktu
  • Al-Shabaab ta ƙwace muhimmin tsibirin Kudhaa a Somaliya
  • Mutum 39 sun mutu a Khartoum na Sudan sakamakon zazzaɓin Denge
  • Trump na kan hanyar zuwa Switzerland bayan samun matsalar jirgi
  • Kotu ta yanke wa mutumin da ya harbi tsohon firaminstan Japan hukuncin rai da rai
  • Yadda ƴansanda suka yi amai suka lashe kan sace mutane a Kaduna

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage

  1. Yadda ƴansanda suka yi amai suka lashe kan sace mutane a Kaduna

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta sanar da sauya matsayar da ta ɗauka a baya cewa ba a sace mutane ba a garin Kurmin Wali na ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda a yanzu rundunar ta tabbatar da garkuwa da mutanen.

    A ranar Litinin aka fara samun rahotannin cewa wasu mahara sun shiga ƙauyen na Kurmin Wali tare da sace mutane kimanin 170 a yankin mai fama da matsalar tsaro.

    Amma a ranar Litinin ɗin, sarkin Kurmin Wali, Ishaku Dan'azumi ya tabbatar wa BBC cewa maharan sun je ƙauyen ne a ranar Lahadi, inda suka sace mutane sama da 160.

    "Sun zo ranar Lahadi wurin karfe 9, lokacin muna coci, suka bazu a garin, suka sa mu a tsakiya.

    "Waɗanda suke a hannunsu yanzu 166," in ji Ɗan'azumi.

    Shi ma shugaban ƙungiyar CAN a arewacin Najeriya Jospeh Hayab ya tabbatar wa kafafen yaɗa labarai batun sace mutunan a ranar ta Litinin.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.