Libya ta kama ma'aikata ƴan ci-rani 1,500 marasa takardu
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Libya sun ce sun kama wasu ma'aikata ƴan ƙasashen waje marasa takardun zama a ƙasar, kimanin 1,500.
An gudanar da samamen kamen ne a cikin dare.
Ma'aikata daga ƙasashen waje - waɗanda mafi yawa suka fito daga Masar da sauran ƙasashen Afirka - ne ke rayuwa cikin fargaba a manyan sansanoni da akan zagaye da katanga da ƙofa ana kullewa.
Ministan ƙwadago na Libya, Ali al-Abed ya ce za su tantance mutanen tare da mayar da su ƙasashensu na sali.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai ƴan ci-rani 800,000 a sansanoni daban-daban na arewacin Libya - waɗanda yawancinsu ke sa ran tsallakawa zuwa nahiyar Turai.
Hukumar zaɓen Kamaru ta yi watsi da buƙatar takarar Maurice Kamto
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar zaɓe ta ƙasar Kamaru ta yi watsi da buƙatar babban ɗan'adawa na ƙasar, Maurice Kamto ta tsayawa takarar shugaban ƙasa domin ƙalubalantar shugaba Paul Biya mai shekara 92 a duniya.
A watan Oktoba mai zuwa ne ake sa ran gudanar da zaɓen, inda hatta wasu daga cikin ministocin gwamnati mai ci suka nuna aniyar ƙalubalantar Biya.
Shugaban hukumar zaɓen ƙasar ta ELECAM, ya karanto sunayen mutum 13 waɗanda hukumar ta amince da su domin yin takara, amma a ciki babu sunan Mista Kamto.
Babu wani dalili da aka bayar na rashin jin sunan nasa a cikin jerin.
Shugaba Paul Biya ya shafe shekara 43 a kan mulki, kuma shi ne shugaban ƙasa da ke kan mulki mafi tsufa a duniya.
A farkon wannan wata na Yuli ne ya nuna aniyarsa ta sake yin takara a zaɓen mai zuwa.
Mista Kamto shi ne ya zo na biyu a yawan ƙuri'u a zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta 2018, lokacin da Biya ya lashe zaɓen duk da zarge-zargen maguɗi.
An kama mutum biyu kan zargin yi wa budurwar da ta suma fyaɗe
Asalin hoton, Getty Images
Ƴansanda a jihar Bihar da ke gabashin ƙasar Indiya sun kama mutum biyu bisa zargin su da yi wa wata mata fyaɗe a cikin motar ɗaukar marasa lafiya.
Hukumomi sun ce an kwashi budurwar ce domin kai ta asibiti bayan ta yanke jiki ta suma a lokacin jarrabawar ɗaukar aiki a gundumar Gaya.
Matashiyar ta ce ta gane cewa an mata fyaɗe ne bayan ta farfaɗo a kan gadon asibiti.
Mutanen biyu da aka kama ba su ce uffan ba game da zargin, cikin su har da direban motar.
Indiya na cikin ƙasashen da aka fi yi wa mata fyaɗe a duniya, inda alƙaluma suka nuna cewa akan samu rahoton yin fyade kimanin 83 a kowace rana.
Yunwa ta kashe yara 600 a arewacin Najeriya cikin wata shida - MSF
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Zaftare kuɗaɗen agaji da ƙasashen duniya ke bayarwa na barazanar ta'azzara matsalar yunwa a yankuna daban-daban na duniya
Ƙungiyoyin agaji na duniya sun bayyana damuwa game da yawan yunwa da ke ta'azzara a arewacin Najeriya, wadda suka alaƙanta da raguwar kuɗaɗen tallafi daga ƙasashen waje.
Ƙungiyar likitoci ta Medecins sans Frontieres (MSF) ta ce yara 600 ne suka mutu waɗanda take kula da su a sansanoninta cikin wata shida da suka wuce saboda ƙarancin abinci mai gina jiki.
World Food Programme (WFP) ta ce za ta dakatar da bayar da duk wani agajin yaki da yunwa a arewa maso gabashin Najeriya cikin wata mai zuwa saboda ƙarancin kuɗi.
Yawan kuɗin da aka daina bayarwa, wanda gwamnatin Amurka karƙashin Donald Trump ta fara yi, ya haɗu da hauhawar farashi da kuma hare-haren masu iƙirarin jihadi domin ta'azzara lamarin.
Labarai da dumi-dumi, Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce ƙarin mutum biyar sun mutu saboda yunwa
Ma'aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta ce ƙarin mutum biyar sun mutu saboda yunwa cikin awa 24 da suka gabata.
Ma'aikatar ta ce adadin ya sa jimillar mutanen da suka mutu sakamakon yunwa ya kai 127.
Cikin wannan adadi har da yara 85.
Tinubu ya faɗa wa 'yanmatan Najeriya 'ku ciyo mana kofi'
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi tawagar ƙwallon ƙafa ta matan ƙasar da ta kai masa kofin gasar ƙasashen Afirka yayin da suke shirin buga wasan ƙarshe a yau Asabar.
Najeriya za ta kara da mai msaukin baƙi Morocco a birnin Rabat domin neman lashe kofin a karo na 10 jimilla, yayin da Moroccon ke neman kofin a karon farko.
"A madadin ƙasar nan baki ɗaya, muna goyon bayanku tare da yin addu'ar ku yi nasara a daren yau, yayin da kuke neman kafa tarihin cin kofi na 10," a cewar Tinubu cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar.
Yadda Buhari ya ƙi karɓar kyautar jirgi yana kan mulki - Garba Shehu
Asalin hoton, State House
Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari, Mallam Garba Shehu, ya bayar da labarin yadda marigayin ya ƙi karɓar wasu kyautuka lokacin yana mulki, ciki har dakyautar jirgin sama.
Da yake magana ta cikin shirin Inside Sources na Channels TV, Garba Shehu ya ce Buhari ya ƙi amincewa da karɓar kyautar agogon lu'ulu'u wani ɗankasuwa a Najeriya ya ƙera da sunansa a jiki, da kuma kyautar jirgin sama da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi masa tayi.
"Shugaban ƙasa ya kalli agogon, ya ce 'Agogon lu'ulu'u? Ba zan iya saka wannan ba. Ku faɗa masa yana ƙoƙari...kuma za mu ci gaba da ƙarfafa masa gwiwa. Ya ci gaba da ɗaukaka sunan Najeriya, amma ku mayar masa da agogon nan. Ba zan iya amfani da shi ba.'," kamar yadda Garba ya bayyana ranar Juma'a.
Ya kuma bayar da labarin ziyarar da Buhari ya kai birnin Dubai a 2016, inda shugaban ƙasar ya yi masa tayin kyautar jirgin sama da zai yi amfani da shi har bayan ya sauka daga mulki, amma marigayin ya ƙi karɓa saboda ba gwamnatin Najeriya za a ba wa ba.
"Sarkin Abu Dhabi ya tambayi shugaban ƙasa [Buhari] wane nau'in jirgi ya fi so. Sai [Buhari] ya ce idan gwamnatin Najeriya za a ba wa zan karɓa. Sai sarkin ya ce a'a naka ne na ƙashin kai, ta yadda ko da ka bar mulki za ka ci gaba da amfani da shi.
"Buhari ya ce ba ni buƙatar jirgi idan na bar mulki, ba zan ma iya kula da shi ba," in ji Garba Shehu.
Buhari ya mulki Najeriya daga watan Mayun 2015 zuwa Mayun 2023, kuma ya rasu a ranar 13 ga watan Yuli.
Kuna iya karanta bayani kan rayuwarsa a labaran da ke ƙasa:
'Yanmajalisar Birtaniya 220 na neman ƙasar ta amice da ƙasar Falasɗinu
Asalin hoton, PA Media
'Yanmajalisar Birtaniya 220 sun nemi gwamnatin ƙasar ta amince da ƙasar Falasɗinu cikin wata wasiƙa da suka aika wa Firaminista Keir Starmer.
Suna son ƙasar ta bi sawun Faransa - da wasu ƙasashe na MDD - wajen amincewa da ayyana 'yancin cin gashin kai na ƙasar Falasɗinawa.
Wakilin BBC ya ce yunƙurin wani mataki ne da ke nuna suka da Allah wadai da abin da Isra'ila ke yi a Gaza yayin da ake fama da bala'in yunwa a zirin.
Sai dai Firaminista Starmer ya ce duk wani yunƙuri na amincewa da ƙasar Falasɗinu mai cikakken 'yanci sai ya jira ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gazan.
Na ga yadda sojojin Isra'ila ke aikata laifukan yaƙi a Gaza - Tsohon sojan Amurka
Asalin hoton, Reuters
Wani tsohon sojan Amurka ya faɗa wa BBC cewa ya ga yadda sojojin Isra'ila da na ƙungiyar raba kayan agaji ke aikata laifukan yaƙi a Zirin Gaza.
Laftanal Kanal Anthony Aguilar ya ce ya ajiye aikinsa tare da ƙungiyar Gaza Humanitarian Foundation (GHF), wadda Amurka da Isra'ila ke goyon baya, saboda laifukan da abokan aikinsa ke aikatawa.
"Na yadda sojojin Isra'ila ke harbin dandazon Falasɗinawa," in ji shi.
Ya ƙara da cewa tun da yake zuwa filin yaƙi a rayuwarsa bai taɓa ganin "irin wannan rashin imani da aikata zalinci a kan fararen hula da ke cikin yunwa ba kamar a Gaza".
Latsa hoton ƙasa ku kalli hirar amma cikin harshen Ingilishi:
Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli hira da Anthony Aguilar cikin harshen Ingilishi:
Ambaliya ka iya auka wa jihar Binuwai a makon nan, in ji NiHSA
Asalin hoton, Nema
Hukumar kula da koguna ta Najeriya ta gargaɗi mazauna wasu ƙananan hukumomi a jihar Binuwai da ke tsakiyar ƙasar game da barazanar ambaliyar ruwa a makon nan.
Wata sanarwa da hukumar Nigeria Hydrological Services Agency (NiHSA) ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta nuna cewa matakin gargaɗin ya kai matuƙa.
Hukumar ta ce ambaliyar ka iya faruwa daga 22 ga watan Yulin nan zuwa 5 ga watan Agusta, wadda za ta iya shafar kogunan Benue da Ngo.
Ma'aikatar Ilimi a Najeriya ta musanta rahoton da wasu jaridu suka ruwaito cewa gwamnatin ƙasar ta ƙayyade shekara 12 a matsayin shekarun da yara za su shiga ajin farko na ƙaramar sakandare wato JSS1.
Cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, mai magana da yawun ma'aikatar Folasade Boriowo ta ce "baki ɗayan rahoton ba daidai ba ne".
"Domin kore wani shakku, mafi ƙanƙantar shekarun shiga JSS1 yana nan a 10," in ji ta. "Bisa doka, babu yaron da zai kammala firamare a ƙasa da shekara 10."
Sanarwar ta ƙara da cewa rahoton bai samo asali daga kowace irin majiyar hukuma ba, sannan kuma Ministan Ilimi Tunji Alausa ya nanata sabon tsari na shekara 16 a matsayin mafi ƙanƙanta kafin shiga jami'a a Najeriya.
Thailand da Camboadia na ci gaba da kai wa juna hare-hare a kan iyaka
Asalin hoton, Reuters
An shiga kwana na uku na faɗan kan iyaka tsakanin Thailand da Cambodia.
Sojojin Thailand sun ce Cambodia ta kai musu hari a yankunansu da ke kusa da gaɓar teku ta kudanci, sai dai sun fuskanci turjiya daga sojojin ruwan da suka fatattake su.
Sama da mutum 30 aka kashe sannan dubbai suka tsere daga muhallansu tun bayan soma wannan rikici a ranar Alhamis, yayin da kowanne ɓangare ke cewa ba shi sarara wa juna.
Cambodia ta faɗa wa kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) cewa tana son a gaggauta tsagaita wuta ba tare da sharuɗɗa ba.
Amma wakilin BBC a Bangkok ya ce ba wannan ne a gaban Thailand ba.
Assalamu Alaikum
Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.
Za mu kawo rahotonnin abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.
Umar Mikail ne ke tare da a wannan hantsi na ranar Asabar.