Ƴansanda sun mamaye hedikwatar jam’iyyar PDP gabanin taronta a Abuja
Ƴan sanda ɗauke da makamai sun mamaye Wadata Plaza, hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, yayin da tashin hankali ke ƙara ƙaruwa dangane da taron kwamitin zartaswa na Kasa (NEC) da ake sa ran gudanarwa a ranar Litinin.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan sanda sun hana Maina Chiroma, ɗaya daga cikin mambobin Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar, shiga cikin harabar hedikwatar.
Wani jami’in jam’iyyar, wanda ya yi magana da gidan talabijin na Channels ba tare da bayyana sunansa ba, ya ce an turo 'yan sandan ne domin hana gudanar da taron na NEC da aka shirya.
Duk da cewa an bar wasu ma’aikatan jam’iyyar sun shiga cikin harabar da farko ba tare da wani cikas ba, daga bisani sai aka tilasta musu fita daga ciki.
Haka kuma, 'yan jarida da ke wajen sun samu umarnin barin harabar hedikwatar jam’iyyar.
An hango wasu daga cikin ‘yan sanda suna toshe titin Dalaba Street, wanda ke kai wa kai tsaye zuwa Wadata Plaza.
Rahotanni dai na cewa a yanzu haka ɓangarori biyu na jam'iyyar na son gudanar da taronsu daban-daban, inda kowane ɓangare ke iƙrarin kasancewa halastacce.