Bankwana
A nan muka kawo ƙarshen rahotannin shafin kai-tsaye na BBC Hausa a yau Litinin.
Mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/06/2025.
Daga Usman Minjibir, Aisha Bbabangida da Annur Muhammad
A nan muka kawo ƙarshen rahotannin shafin kai-tsaye na BBC Hausa a yau Litinin.
Mu kwana lafiya.
Iyalan ɗan majalisar dokokin Uganda da aka yi garkuwa da shi a karshen makon da ya gabata, sun ce ya kuɓuta da ransa, amma akwai alamun azabtarwa a jikinsa.
Barnabas Tinkasimire na jam'iyya mai mulki yayi kaurin suna wajen sukar gwamnatin shugaba Yoweri Museveni.
A ranar Lahadin da ta gabata ne ƙungiyar fafutuka ta Uganda ta yi Allah wadai da yadda tawagar jami’an tsaro suka tafi da shi, a wani gidan Mai a Kampala babban birnin ƙasar.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta majalisar ɗinkin duniya ta koka akan matsawa jam’iyyun hamayya gabanin zaɓen ƙasar a shekara mai zuwa.
Isra'ila ta kai sabbin hare-hare ta sama a Gaza, inda rahotanni ke cewa ta kashe mutane 60, wasu daga cikin su a kan layin karɓar tallafi.
Jami'an kiwon lafiya sun ce mutane aƙalla 20 wani harin na daban ya kashe a wata cibiyar ƴan jarida da masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam a Gaza.
Wani ganau, Ali Abu Ateila ya ce akwai mata da ƙananan yara a wajen, lokacin da jirgin yaƙi ya buɗe masu wuta.
Rundunar sojin Isra'ila ba ta yi tsokaci a kai ba, amma ta ci gaba da fitar da umarni ga mazauna Gaza domin ganin sun fice daga yankin.
Akwai raɗe-raɗi a Isra'ila cewa wasu janar-janar ɗin sojin ƙasar na ganin cewa dakarunsu sun kusa kammala muradinsu a Gaza.
Majalisar dokokin Amurka ta fara kaɗa ƙuri'a a kan ƙudirin dokar shugaba Trump na haraji da kashe kuɗin gwamnati, bayan shafe makonni ana tuntuɓa a kai.
Ƴan jam'iyyar Republican masu rinjaye a majalisar sun rarrabu a kan yadda za a rage tsare-tsaren tallafi na gwamnati domin ƙara wa'adin dakatar da biyan haraji.
Ƴan jam'iyyar Democrat sun juya baya ga ƙudirin dokar, inda suke sukar yadda ya ke neman rage tallafin kiwon lafiya ga miliyoyin talakawa ƴan Amurka.
Sanata Chuck Schumer na jam'iyyar Democrat ya ce ƙudirin dokar zai ƙwace damar samun tallafin kiwon lafiya ga jama'ar Amurka.
Shugaba Trump na fatan majalisar ta zartar da ƙudirin ya zuwa ranar huɗu ga watan Yuli.
Bayan shafe tsawon yinin yau Litinin ana kai ruwa rana tsakanin mambobin babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, jam'iyyar ta gudanar da taronta na kwamitin zartaswa wato NEC karo na 100.
Taron na zuwa ne bayan wani taron sirri da gwamnonin jam'iyyar suka gudanar a gidan gwamnatin jihar Bauchi da ke unguwar Asokoro a Abuja.
Shugaban jam'iyyar na riƙo, Amb. Iliya Damgum ya shaida wa manema cewa taron ya mayar da hankali kan abu guda ɗaya, kodayake bai bayyana batun ba.
Taron na zuwa ne bayan shafe tsawon yinin ranar Litinin ana dambarwa tsakanin ƴan jam'iyyar game da taron.
A karon farko wata kafar yaɗa labarai mai goyon bayan ƙungiyar IS ta tabbatar cewa an kashe babban kwamandan ƙungiyar a yankin Sahel yayin wani samame a ƙasar Mali.
Kafar Bariqa ta wallafa hotunan gawar Abu al-Dahdah, ɗan asalin ƙasar Morocco.
Rundunar sojin Mali da dakarun Rasha a Afirika sun ce an kashe shi ne a gabashin yankin Maneka a ranar Asabar.
Har yanzu ƙungiyar IS ba ta fitar da bayani ba a kan mutuwar tasa.
Ƙungiyar IS mai alaƙa da Al Qaeda ta zamo barazana ga yankin Sahel, kuma ana zarginta da hannu a mafi yawan munanan hare-haren da ake kaiwa a yankin.
Hukumomi a Kenyan sun ce sun kama mutane 485 a bisa alaƙarsu da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati a makon jiya, wadda ta zamo rikici a sassan ƙasar.
Daraktan sashin binciken manyan laifuka na ƴansandan Nairobi Mohamed Amin ya ce ana zargin mutanen ne da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da kisa da ta'addanaci da sata da lalata kayan gwamnati da kuma kai wa ƴansanda hari.
Ya ce daga cikin mutane 485 da aka kama, tuni aka gurfanar da 448 a gaban kuliya, yayin da ake ci gaba da bincike a kan sauran 37.
Mr.Amin ya ce akwai shaidun da aka samu a hannun waɗanda aka kaman masu nuni da hannun su a tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar.
Ya kuma tabbatar da cewa akwai wasu mutanen da masu bincike ke bibiya domin tabbatar da zargin da ake masu na tayar da tarzoma.
Daraktan sashin binciken manyan laifuka na ƴansandan Nairobi ya kuma sanar da cewa an kashe ƴansanda aƙalla 11 a lokacin zanga-zangar, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Tawagar gwamnatin Najeriya ta ziyarci iyalan marigayi Alhaji Aminu Dantata a birnin Madina na Saudiyya domin yin ta'aziya da kuma tsara janaizar hamshaƙin ɗan kasuwan.
Alhaji Aminu Dantata ya rasu a ranar Asabar, yana da shekara 94, a birnin Abu Dhabi na haɗaɗɗiyar daular Larabawa.
Kafin rasuwar tasa ya bayar da wasiyyar a binne shi a birnin Madina kuma ana shirin cika wannan buri nasa a ranar Talata.
Tawagar gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin ministan tsaron ƙasar Muhammad Badaru Abubakar, ta isa birnin Madinah ranar Litinin da safe.
Sauran ƴan tawagar sun haɗa da babban lauyan gwamnati kuma ministan shari'a, Prince Lateef Fagbemi da ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris da ƙaramin ministan samar da gidaje, Yusuf Abdullahi Ata.
Akwai kuma fitattun malaman addinin musulumci da suka haɗa da Dr. Bashir Aliyu Umar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Khalifa Abdullahi Muhammad.
Alhaji Mustapha Junaid da wasu daga cikin iyalan marigayin, da suka haɗa da matansa da ƴaƴa da jikoki ne suka tarbi tawagar.
Iyalan ɗan ƙasar Kenyan nan mai sayar da kaya a kan titi wanda ke jinyar harbin da ƴan sanda suka yi masu yayin zanga-zanga sun ce ɗan uwan nasu ya mutu.
Boniface Kariuki, mai shekara 24, an harbe shi ne lokacin da ƴansanda ke tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Nairobi makonni biyu da suka wuce.
Hukumar kare ƴancin ɗan Adam ta ƙasar ta ce mutane aƙalla 19 aka kashe a yayin zanga-zangar gama gari domin neman a yi adalci ga malamin makaranta kuma ɗan fafutuka da aka tsare, kuma ya mutu a hannun jami'an tsaro, Albert Ojwang.
Hukumar ta ce akwai kuma wasu mutane 15 da suka ɓace tun bayan fara zanga-zangar.
Ministan harkokin cikin gida na Kenya ya ce masu zanga-zangar suna ƙoƙarin hamɓarar da gwamnati ne.
Bayan shafe tsawon yinin yau ana kai ruwa tsakanin mambobin babbar jam'iyyar hamayya ta PDP daga ƙarshe dai jam'iyyar ta fara gudanar da taron na majalisar zartaswa wato NEC.
Shugaban jam'iyyar na riƙo, Amb. Iliya Damgum ya shaida wa manema cewa taron zai mayar da hankali kan abu guda ɗaya, kodayake bai bayyana batun ba.
Damagum ya kuma ja hankalin ƴanjarida su guji yaɗa labaran da ka iya haifar da ruɗani a jam'iyyarsa
Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa.
Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya tabbatar wa da BBC ɗage jana'izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina.
''Akwai ƙa'idoji da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana'iza a ƙasar, to yanzu haka ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,''in ji ministan.
Mohammed Idris ya ce idan an kammala za a ɗauko gawar daga Hadaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Saudiyya.
Ya ƙara da cewa tuni ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana'izar.
Bayanai sun ce Alhaji Aminu Ɗantata ne ya bar wasiyyar binne shi a birnin Madina, inda kuma ƴan'uwansa suka nemi amincewar hukumomin Saudiyya game da buƙatar, suka kuma amince da ita.
Tun da safiyar yau ne tawagogin gwamnatin tarayya da na gwamnatin jihar Kano suka tafi Saudiyyar da nufin halartar jana'izar da aka shiryi yi a yau Litinin.
Shugabani da gwamnonin da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Najeriya na ci gaba da tattanawa wajen gani sun shawo kan ɓarakar da ta kunno kai a tsakaninsu da ya janyo tsaiko, wajen gudanar da taron majalisar zartawa na jam'iyyar da aka shirya gudanarwa a yau Litinin.
Tun da safiyar yau ne dai aka ga jami'an 'yansanda da na tsaron fararen hula na Civil Defense suka yi wa ofishin jam'iyyar na Wadata Plaza, Abuja tsinke tare da hana dukkanin manyan jami'an jami'yyar shiga.
Yanzu haka dai kwamitin amintanntu na jam'iyar na gudanar da wani taron sirri a babban ɗakin taro na Ƴar'adu Center da ke Abuja.
Taron nasu na zuwa a daidai lokacin da gwamnonin jam'iyyar da ƴan majalisar dattawa da na wakilai da ke gudanar da wani taron a gidan gwamnatin jihar Bauchi da ke unguwar Asokoro a birnin na Abuja.
Wakilin BBC da ke wurin ya ce duka tarukan biyu ana yi ne da nufin lalubo bakin zaren yadda za a gudanar da babban taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar (NEC) da ake shirin yi a ofishin jam'iyyar da ke Wadata Plaza.
Tun da faro dai kwamitin Amintattun Jam'iyyar sun shirya gudanar da taron nasu ne a ofishin jam'iyyar da ke Wadata Plaza da misaƙalin ƙarsfe 10:00 na safe amma hakan bai samu ba.
Aƙalla Falasɗinawa 20 ne aka kashe a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama wanda ya faɗa kan wani shahararren wurin shan shayi da ƴanfafutika da ƴanjarida da mazauna yankin yammacin Gaza ke amfani da shi, a cewar likitoci da shaidu.
Tawagar masu aikin ceto sun kwashe gawarwakin mutum 20 da wasu da dama da suka samu raunuka daga gidan cin abinci na Al-Baqa, wurin da ya ƙunshi tanti da ke gaɓar teku, kamar yadda mai magana da yawun hukumar kare fararen hula ta Hamas ta Gaza ya shaida wa BBC.
Ya ƙara da cewa jami'an agajin gaggawa na ci gaba da bincike a cikin wani rami mai zurfi da fashewar ta haifar.
Aziz Al-Afifi, wani mai ɗaukar hoto da wani kamfanin kera kayayyaki, ya shaida wa BBC cewa "Ina kan hanyar zuwa wurin shan shayi don amfani da intanet a ƴanmitoci kaɗan, sai ga wata babbar fashewa ta tashi."
"Na gudu zuwa wurin. Abokan aiki na suna can, mutanen da nake haɗuwa da su kowace rana. Wurin ya yamutse, gawarwaki da jini da kururuwa ko'ina."
Mutum biyu ƴan arewacin jamhuriyar Kamaru ne suka shiga sahun masu fafatawa da shugaban ƙasar Paul Biya da ke neman sabon wa'adi.
Mutanen sun haɗa da ministan yawon buɗe ido na ƙasar, Bello Bouba Maigari da tsohon kakakin gwamnati, IssaTchiroma Bakary.
Bello Maigari ya amince da damar yin takara da jam'iyyarsa ta ba shi a zaɓen shugaban ƙasa na watan Oktoba domin karawa da shugaba Paul Biya wanda ya kwashe shekaru 39 a kan karaga.
Har kawo yanzu dai Paul Biya bai sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar ba.
Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya ta tabbatar da kisan riƙaƙƙen ɗan bindigar da ya addabi wasu yankunan jihar.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga ya bayyana kisan Danbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro.
''Danbokolo mutum ne da ya fi Bello Turji fitina, ya fi Turji aikata miyagun laifuka, illa kawai shi Turji sunansa da ya karaɗe kafofin yaɗa labarai'', in ji Ahmad Manga.
''Mutanensa da aka kashe sun haufa 100, saboda haka wannan gagarumar nasara ce a gare mu'', in ji jami'in gwamnatin Zamfarar.
Kacalla Danbokolo ya rasa ransa a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin jami'an sa kai na gwamnatin jihar Zamfara da mayaƙan ɗanbindigar.
Ana kallon mutuwar Danbokolo - wanda ake ganin a matsayin ubangidan Bello Turji - a matsayin cigaba a ɓangaren yaƙi da ƴanbindiga.
Donbokolo ya shafe shekaru masu yawa yana kai hare-hare yankunan jihar Zamfara tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Riƙaƙƙen ɗanbindigar ya gamu da ajalinsa ne tare da wasu ɗimbin mayaƙansa a lokacin da jami'an tsaron sa kai - da gwamnatin jihar Zamfara ta samar.
Mazauna yankin na kallonsa a matsayin mutum marar imani da tausayi da ya addabi yankunansu, ta hanyar kai hare-hare da kisan mutane.
"Shi mutum ne da bai yarda da sulhu ko ta wane hali ba, hatta ɗan'uwansa Bello Turji ya taɓa nuna alamun amincewa da sulhu, amma shi wannan bai taɓa nuna hakan ba'', kamar yadad wani mazaunin yankin ya bayyana.
Wannan ne karo na biyu da jami'an tsaro ke kashe riƙaƙƙun ƴanbindiga da ake ganin a matsayin iyayen gida da Bello Turji.
A watan Satumban 2024 ne jami'an sojojin ƙasar suka kashe Halilu Sububu, wanda ya shi ubangida ne ga Bello Turji a wani kwantan ɓauna da suka yi masa tare da mayaƙansa.
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya yi gargaɗin cewa miliyoyin ƴangudun hijirar Sudan da suka tsere zuwa ƙasashe makwabta na fuskantar haɗarin tsundumawa cikin matsanancin yunwa da rashin abinci mai gina jiki, sakamakon ƙarancin kuɗaɗen tallafi da ya tilasta yanke matakan rage agajin gaggawa.
Tun bayan ɓarkewar yaƙi a Sudan a watan Afrilu na 2023, fiye da mutum miliyan huɗu ne suka tsere zuwa ƙasashe makwabta da suka haɗa da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR) da Chadi da Masar da Habasha da Libiya da Sudan ta Kudu, da kuma Uganda, domin neman abinci da mafaka da kuma tsaro.
WFP ta bayyana cewa tana buƙatar fiye da dala miliyan 200 domin ci gaba da aikin gaggawa na tallafa wa ‘yan gudun hijirar Sudan da ke waɗannan yankuna cikin watanni shida masu zuwa.
Haka kuma, tana neman dala miliyan 575 domin tallafa wa waɗanda suka fi rauni cikin ƙasar Sudan da ke cikin mawuyacin hali.
WFP ta ce rashin wadatar kuɗi yana barazana ga ayyukanta na ceton rai, musamman ga mata, yara da tsofaffi da ke fama da yunwa da matsanancin rashin abinci.
Rundunar ƴansandan Abuja ta musanta rahotannin da ke cewa jami'anta sun karɓe iko da hedikwatar jam'iyyar PDP ta Wadata Plaza a ranar Litinin.
Rundunar ta ce tana son "ta nuna cewa babu gaskiya a rahotonnin sannan ba haka al'amarin yake ba. An kai jami'an ƴansandan ne zuwa wurin taron domin wanzar da doka da oda kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
A wata sanarwa, rundunar ta ce "babu wani lokaci da jami'an ƴansanda suka kulle sakateriyar jam'iyyar ta PDP."
A sanarwar, kwamishinan ƴan sanda na Abujar ya buƙaci kafafen watsa labarai da su yi kaffa-kaffa wajen tantance labarai kafin su wallafa shi.
Isra'ila ta ƙaddamar da ƙarin hare-hare ta sama a Gaza, abin da ya janyo ƙaruwar ɗaiɗaitar daruruwan al'ummar Falasɗinawa kamar yadda shedu suka tabbatar.
Masu aikin ceto sun samo gawar mutum biyar sannan an garzaya da gomman fararen hula zuwa asibitin Ahli da ke birnin na Gaza, kamar yadda kafafen watsa labarai na cikin gida ke rawaitowa.
Luguden wutar ya biyo bayan wani umarni ga jama'a su bar yankin, irinsa mafi girma tun bayan da yaƙin ya yi kome a watan Maris.
Wannan dai na zuwa adaidai lokacin da firaiministan Isra'ila ke fuskantar matsin lamba kan ya mayar da hankalinsa wajen cimma tsagaita wuta a Gaza.
A ranar Litinin ne wa'adin da wata kotu ta bai wa kamfanin Facebook na biyar tarar dala miliyan 290 bisa samun sa da laifin karya dokoki.
A watan Yulin 2024 ne dai kotun ta umarci kafamin da ya biya tarar bayan samun shi da laifin taka dokokin da suka jiɓanci gasa da tallan haja da kuma na bayanan sirri.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko kamfanin na Meta zai biya wannan tara da kuma matakin da gwamnatin ƙasar za ta ɗauka idan kamfanin ya gaza bin umarnin kotun.
A watan Mayu ne kamfanin na Meta mamallakin Facebook ya yi barazanar rufe ayyukansa a Najeriya bisa abin da ya bayyana da tarar da ta wuce hankali.
Wani rahoto ya nuna cewa al'ummar Najeriya ka iya rasa damar ci gaba da hulɗa da shafukan Facebook da Instagram idan dai har kamfanin na Meta ya aiwatar da barazanar da ya yi na rufe ayyukan nasa a ƙasar.