Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya 05/04/2025

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu

  2. Dubban mutane sun shiga zanga-zangar adawa da tsadar muhalli a Sifaniya.

    Dubban mutane sun shiga zanga-zanga a faɗin Sifaniya sakamakon tsadar muhalli.

    Mutane na bayyana takaicinsu game da tsadar kuɗin hayar gidaje da kuma ƙarancin gidaje masu sauƙi.

    Matsalar ta ta'azzara ne bayan ƙaruwar ziyarar masu yawon bude ido, abinda ya sanya aka mayar da gidaje da dama masaukan baƙi na haya.

    Gwamnatin Sifaniya na ƙoƙarin samar da gidaje masu sauƙi a faɗin ƙasar.

  3. Trump ya yi kira ga Amurkawa su yi tsayin daka kan sabbin sauye-sauyensa

    Shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, cewa Amurkawa su yi tsayin daka yayin da yake bijiro da sabbin sauye-sauyen harajin shigar da kayayyaki ƙasar.

    Mista Trump ya bayyana sauye-sauyen nasa a matsayin juyin juya halin tattalin arziƙi.

    Tuni kasuwannin hannun jari suka shiga ruɗani.

    Beijing ta nemi Amurka ta daina amfani da haraji a matsayin makamin daƙile ciniki.

  4. Dubban Amurkawa na zanga-zangar adawa da matakan Donald Trump

    Dubban Amurkawa sun fantsama a birnin Washington da sauran biranen Amurka domin yin zanga-zangar adawa da matakan Shugaba Trump .

    Zanga-zangar ita ce mafi girma tun bayan komawarsa karagar mulki a watan Janairin bana.

    ƴan gwagwarmaya da ƙungiyoyin ma'aikata sun haɗa kai ƙarƙashin inuwar abin da suka kira ''haɗa hannu waje guda'' domin nuna turjiya kan matakan gwamnatin Trump na rage yawan ma'aikatun gwamnati da kuma taƙaita iko a fadar White House.

    Ƙungiyoyin na nuna fargabar cewa ayyukan gwamnati masu muhimmanci da dimokraɗiyyar Amurka na cikin hatsari.

    An dai shirya zanga-zangar a duka jihohin ƙasar 50.

  5. Tinubu ya sha alwashin hukunci mai tsanani kan maharan Plateau

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya alƙawarta kama mutanen da suka kai hari wasu garuruwa a Plateau domin su fuskanci hukunci mai tsanani ƙarƙahsin doka.

    Cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu a harin, bayan da wasu ƴan bindiga suka ƙaddamar da munanan hare-hare a garuruwan Ruwi da Tadai da ƙauyukan Manguna da Dafo a ƙaramar hukumar Bokkos.

    Shugaba Tinubu ya jajanta wa gwamnan jihar, Caleb Mutfwang tare da kiran al'umomin garuruwan su bai wa jami'an tsaron haɗin kai wajen kama waɗanda suka kai harin domin kare garuruwansu.

    Shugaban ƙasar ya kuma tabbatar wa gwamnan goyon bayansa wajen kawo ƙarshen zubar da jini da ake yi a jihar.

    Sanarwar ta kuma ce shugaban ya buƙaci hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta yi aiki da sauran hukumomi wajen tallafa wa mutanen da ke buƙatar taimakon gaggawa sakamakon hare-haren.

    "Rahoton samun hare-haren ƴanbindiga a Plateau ya matuƙar baƙanta min rai. Ba za mu lamunci hare-hare kan mutanen da ba su ji ba su gani ba. Don haka na umarci jami'an tsaro su farauto maharan, kuma dole za su fuskanci hukunci mai tsanani idan aka kama su'', in ji Shugaba Tinubu.

  6. Ministan ilimin Najeriya na so a faɗaɗa shirin NYSC zuwa shekara biyu

    Ministan ilimi na Najeriya, Olatunji Alausa ya yi kira da a faɗaɗa shirin yi wa ƙasa hidima, NYSC daga shekara ɗaya zuwa shekara biyu.

    Mista Alausa ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa babban daraktan hukumar, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ziyara a ofishinsa ranar Juma'a.

    Haka kuma ministan ya buƙaci a faɗaɗa tare da inganta shirin koya wa masu yi wa ƙasa hidima sana'o'i.

    Minista ya kuma yaba wa ayyukan hukumar NYSC, musamman wajen tantance tare da gano matasan da suka je sansanonin NYSC da takardun kammala karatu na bogi.

    Ya kuma ce ma'aikatarsa za ta ci gaba da aiki tare da da hukumar wajen inganta harkokin ilimi a faɗin ƙasar.

    Mista Alausa ya kuma yi kira da a riƙa tura masu yi wa ƙasa hidima domin koyarwa a makarantun ƙauyuka da karkara, domin cike giɓin malaman da ake da ƙarincin a irin waɗannan makarantu.

  7. 'Birtaniya da Faransa za su aike da dakaru zuwa Ukraine'

    Shugaba Zelensky na Ukraine ya ce an samu gagarumin ci gaba a ganawar shugabannin sojin Ukraine suka yi da takwarorinsu na Birtaniya da Faransa.

    Ya ce a matakin farko ƙasashen sun tsara yadda za su girke dakarunsu a Ukraine.

    Birtaniya da Faransa na jagorantar yunƙurin ƙasashen Turai na tura ''dakaru Ukraine'' idan an dakatar da yaƙin.

    Shugaban sojin Faransa ya ce za a yi hakan ne domin tabbatar da zaman lafiya a Ukraine, wani muhimmi ƙudiri ga tsaron ƙasashen Turai.

    A nata ɓangare Rasha na adawa da girke kowaɗane irin dakaru na ƙungiyar NATO a Ukarine.

  8. 'Ƴanbindiga sun kashe fararen hula kusan 200 a Burkina Faso'

    Waɗanda suka tsira daga hare-haren masu iƙirarin jihadi a Burkina Faso sun ce an kashe fararen hula kusan 200 a yayin hare-haren.

    Shaidu sun ce maharan ɗauke da makamai sun far wa wasu ƙauyuka uku a lardin Sourou, inda suka riƙa kisa kan mai tsautsayi da ɓarnata dukiya.

    Da yawa daga cikin waɗanda aka kashe matasa ne da suka shiga aikin sa kai domin taimaka wa gwamnati yaƙar masu iƙirarin jihadi.

    Hare-haren sun auku ne bayan sojojin sun ƙaddamar da mummunan hari kan masu iƙirarin jihadin a yankin.

    Mazauna ƙauyukan dai sun ce sun faɗa wa sojojin su zauna a ƙauyukan saboda fargabar harin ramuwar gayya daga masu iƙirarin jihadin.

  9. Rashin tsaron Filato ya wuce rikicin fulani da makiyaya - Gwamnati

    Gwamnan jihar Filato a Najeriya, Caleb Mutfwang ya ce hare-hare da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan jiharsa sun wuce batun rikicin manoma da makiya, inda ya ce wasu ne suke ɗaukar nauyin rikice-rikice domin hana jihar zaman lafiya.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen taron baje-kolin kayayyakin ado da Tincity Fashion ta shirya mai taken, “The Plateau Experience”, da aka yi a ranar Juma'a a Abuja.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito daga kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa gwamnan ya ce burin maƙiyan jihar ne su jefa tsoro da firgici ga ƴan jihar.

    "Babban burin maƙiyanmu shi ne su jefa jihar cikin ruɗani da tashin hankali, amma za mu magance matsalar domin ba za mu ba su dama ba.

    "Duk wanda yake tunanin wannan kashe-kashen wai rikicin fulani da makiyaya ne, bai fahimci lamarin ba ne. Wani shiryayyen al'amari ne da wasu suka shirya domin ba sa so jiharmu ta zauna lafiya.

    "Ina so in tabbatar wa ƴan jiharmu ta Filato cewa Allah zai taimake mu, ya ba mu nasara a kansu domin lokacinsu na kusa ƙarewa," in ji shi.

  10. Ɓera ya kafa tarihin gano wuraren da ake binne nakiyoyi

    Wani ɓera ɗan Afirka mai suna Ronin ya kafa tarihin gano ababen fashewa 15 waɗanda aka binne tun a shekarar 2021 a ƙasar Cambodia.

    Kundin bajinta na Guinness ya ce aikin da Ronin yake yi yana da matuƙar muhimmanci wajen inganta rayuwar waɗanda suke fargabar taka nakiya da aka binne a ƙasa.

    Kamfanin Apopo ne ke horas da ɓeraye don yin amfani da su a irin waɗannan ayyuka.

    Zuwa yanzu akwai ɓeraye aƙalla guda 104 a ƙarƙashin kulawar kamfanin Apopo, wanda yake ƙasar Tanzania.

  11. Yin hira da baƙin fuska na taimaka wa walwalar ɗan'adam

    Hatta 'yar gaisuwa da za ku yi wa juna kamar "barka" ko "sannu" a kan titi ko a shagon sayen kayayyaki za ta iya ƙara farin ciki a zukata.

    Sakamakon wani bincike da aka gudanar a Turkiyya a kwanan nan ya ƙara bayani kan sauran bincike a duniya game da yadda hulɗa tsakanin mutane za ta iya haɓaka walwalarsu.

    "Mun gano cewa hira da mutanen da mutum bai sani ba na da tasiri a kyautatuwar rayuwar mutum," in ji Esra Ascigil, shugabar marubuta binciken na Tsangayar Zamantakewa a Jami'ar Sabanci.

  12. Me tsarin mulki ya ce kan bai wa mataimakin shugaban Najeriya riƙon ƙwarya?

    'Yan Najeriya musamman ƴan siyasa da ƴan gwagwarmaya na ci gaba da cecekuce kan tafiye-tafiyen da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke yi zuwa ƙasashen waje ba tare da bai wa mataimakainsa riƙon ƙwaryar gudanar da harkokin gwamnati ba.

    A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasar ya tafi "ziyarar aiki" ta mako biyu zuwa ƙasar Faransa, kamar yadda fadarsa ta bayyana cikin sanarwar tafiyar.

    Sanarwar ta ce shugaban zai yi amfani ziyarar ne wajen nazarin yadda gwamnatinsa ta kasance a daidai lolacin da take dab da cika rabin wa'adi.

  13. Ƴansanda na binciken hargitsin da aka samu a masallaci saboda mariya Sheikh Dutsen Tanshi

    Kwamishinan ƴansandan jihar Bauchi a Najeriya, Sani-Omolori Aliyu ya yi kira ga ƴan jihar da su kwantar da hankalinsu kan hargitsin da aka samu a wani masallaicin jihar kan batun marigayi Sheikh Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi.

    A wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya ce, "a ranar 4 ga Afriku ne wasu suka kai ƙarar cewa limamin masallacin Galli da ke Jahun, Ahmad Isa Jaja a cikin hudubarsa ya faɗa wasu kalamai game da Marigayi Malam Abdulaziz Idris da ba su yi wa ɗalibansa daɗi, inda suka taru a masallaci domin nuna rashin daɗinsu."

    Sanarwar ta ce hakan ya sa kwamishinan ƴansandan jihar Sani-Omolori Aliyu, ya tura jami'ai na musamman domin tabbatar da kaucewa tayar da zaune tsaye.

    "Da jami'anmu suka isa masallacin, sun samu nasarar tseratar da limamin da fatattakar wadanda suka taru cikin ƙwarewa, sannan kwamishinan ƴansanda ya yi umarni a ƙaddamar da bincike domin gano musabbabin lamarin," in ji sanarwar.

  14. 'Waɗanda aka kashe a Filato sun kai 52'

    Waɗanda suka rasu a harin da wasu mahara suka kai a ƙaramar hukumar Bokkos na jihar Filato da ke Najeriya sun ƙaru zuwa 52, kamar yadda ƙungiyar ci gaban al'adun Bokkos ta bayyana.

    Shugaban ƙungiyar, Farmasum Fuddang ne ya bayyana wa tashar Channels haka, inda ya ce an binne mutum 31 a rami ɗaya a ranar Alhamis, sannan akwai wasu guda biyar da suka ƙone a ƙauyen Hurti, sai kuma wasu guda 11 a ƙauyen Ruwi, da wasu guda huɗu a ƙauyen Manguna, da kuma wani mutum a ƙauyen Daffo.

    A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Filato ta yi kira ga ƴan jihar su kwantar da hankalinsu a daidai lokacin da ake cigaba da neman waɗanda ba a gani ba.

    Kwamishinar watsa labarai ta jihar, Joyce Remnap ta ce an tura jami'an tsaro yankunan domin tabbatar da zaman lafiya ya wanzu.

    "Sannan an kama wasu waɗanda ake zargi suna da hannu a kashe-kashen," in ji ta, sannan ta ƙara da cewa, "muna kira da a guji ɗaukar doka a hannu."

    Tun a farkon harin ne dai ƙungiyar makiyaya ta Gan Allah ta fito ta ce maharan ba fulani ba ne, kuma ba su da wata alaƙa da su.

  15. Muller zai bar Bayern Munich bayan 25 a ƙungiyar

    Ɗanwasan Jamus, Thomas Muller zai bar Bayern Munich a ƙarshen kakar bana bayan kusan shekara 25 yana taka leda a ƙungiyar.

    Muller mai shekara 35 ne ya fi buga wa ƙungiyar wasa, inda ya buga wasa 743, sannan shi ne na uku a zura ƙwallaye, inda yake da ƙwallaye guda 247.

    Ya fara ƙwallo a ƙungiyar ne tun yana ƙarami a sashen horar da matasa, kafin ya fara wakiltar babbar ƙungiyar a shekarar 2008.

  16. Ƙasashen ECOWAS za su tattauna kan harajin ƙasashen AES

    Ƙungiyar ECOWAS za ta gudanar da taron na musamman domin tattaunawa kan harajin kayayyaki da ƙungiyar ƙasashen AES suka lafta wa ƙasashenta.

    Ƙasashen ECOWAS za su zauna ne a watan da ake ciki na Afrilu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga jami'in watsa labarai na ƙungiyar ƙasashen Joel Ahofodji.

    Ya ce, "za a yi taron ne a ranar 22 ga Afrilu kan harajin kashi 0.5 da ƙasashen AES suka lafta wa kayayyakin da ke shiga ƙasashensu da su daga ƙasashen ECOWAS."

    Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar ƙungiyar ECOWAS ɗin za ta mayar da martani wajen ɗora wa ƙasashen na AES haraji, sai ya ce, "a lokacin taron za a tattauna komai da komai."

    Ƙasashen AES wato Mali da Nijar da Burkina Faso da suke ƙarƙashin mulkin soji ne suka sanar da ɗora wa ƙasashen ƙungiyar ECOWAS da suka fice harajin kashi 0.5 kan kayayyakin da ake shiga da su, "domin samun kuɗaɗen shiga."

    Harajin zai fara aiki ne daga ranar 28 ga watan Maris, amma banda kayayyakin agaji.

    Wannan ya saɓa da yadda aka saba na cinikayya da shiga da fitar da kayayyaki ba tare da shinge ba a tsakanin ƙasashen ECOWAS.

  17. Harajin da Trump ya lafta wa kayayyakin ƙasashen waje ya fara aiki

    Harajin kashi 10 cikin 100 da shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba kan duk kayayyakin da za su shiga Amurka ya fara aiki.

    Matakin da Trump ya sanar a farkon makon nan a wani ɓangare na abin da ya kira ranar ƴanci, ya shafi duk wasu kayayyaki daga kusan kowace ƙasa.

    Daga kayan laturoni zuwa tufafi, farashin kayayyakin da ke shiga Amurka zai ƙaru duk a yunƙurin Trump na haɓaka masana'antun Amurka da kuma magance matsalolin da ake samu ta fuskar kasuwanci.

    Wakiliyar BBC ta ce gwamnatin Amurka ba ta gargaɗi ƴan ƙasar kan cewa za su iya fuskantar tasirin matakan da ya ɗauka ba ko dai nan kusa ko kuma a gaba.

    A ranar Laraba kusan ƙasashe 60 za su fuskanci ƙarin haraji mai tsauri. Mista Trump ya bayyana matakin a matsayin ramuwar gayya ga ƙasashen da yake zargi da cutar da Amurka.

  18. Zelensky ya zargi Rasha da kashe ƴan Ukraine 14 da makami mai linzami

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da kashe ƴan ƙasarsa 14 a wani harin makami mai linzami da ta kai kan yankunan gidaje a Kryvyi Rih.

    Shida daga cikin waɗanda suka mutun yara ne.

    Mista Zelensky dai ya wallafa hotunan gawarwaki kwance a kusa da wani filin wasan yara da kuma rukunin gidajen da aka lalata.

  19. Kotu ta dakatar da gangamin magoya bayan Wike a Bayelsa

    Wata babbar kotu a jihar Bayelsa ta dakatar da magoya bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike daga shirya gangamin siyasa da suke shirin yi a jihar.

    Kotun ta ce a dakata da gudanar da taron har sai ta saurara tare da yanke hukunci.

    Asali dai an shirya gudanar da taron ne a birnin Yenagoa a ranar 12 ga watan Afrilun bana, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Mai shari'a I.A Uzakah ne ya yanke hukuncin mai lamba BYHC/YHC/CV/133/2025, bayan kwamishinan shari'a na jihar Biriyai Dambo ya shigar da ƙara.

    Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Afrilu.

    Ana dai ta cacar-baki ne tsakanin gwamnatin jihar Bayelsa da magoya bayan Wike na jihar, inda magoya bayan ministan suka dage kai da fata sai sun shirya taron gangamin, shi kuma gwaman jihar ya ce allambaran ba a jiharsa ba.

  20. Syria ta caccaki Amnesty International kan zargin 'laifukan yaƙi'

    Gwamnatin Syria ta caccaki wani rahoton ƙungiyar kare haƙƙin biladama ta Amnesty International kan kashe-kashen da aka yi a watan da ya gabata.

    Amnesty ta gano cewa kisan kiyashi a Latakia da Tartus na iya zama laifukan yaƙi.

    A cewar ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Syrian Observatory for Human Rights, jami'an tsaro sun kashe fiye da mutum dubu ɗaya da ɗari bakwai.

    Galibinsu a cewar rahotanni farar hula ne daga al'ummar Alawi waɗanda suka kasance tsiraru.

    Gwamnati ta ce rikicin ya soma ne lokacin da magoya bayan hamɓararren shugaban Syria, Bashar al Assad suka far wa sojoji.