Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muller zai bar Bayern Munich bayan shekara 25 a ƙungiyar
Ɗanwasan Jamus, Thomas Muller zai bar Bayern Munich a ƙarshen kakar bana bayan kusan shekara 25 yana taka leda a ƙungiyar.
Muller mai shekara 35 ne ya fi buga wa ƙungiyar wasa, inda ya buga wasa 743, sannan shi ne na uku a zura ƙwallaye, inda yake da ƙwallaye guda 247.
Ya fara ƙwallo a ƙungiyar ne tun yana ƙarami a sashen horar da matasa, kafin ya fara wakiltar babbar ƙungiyar a shekarar 2008.
Ya lashe gasar Bundesliga 12 da zakarun turai biyu a cikin kofi 33 jimilla da ya lashe a ƙungiyar ta Jamus.
"Ina matuƙar farin cikin nasarorin da na samu a wannan ƙungiyar. Babban ban-kwanan da nake buƙata shi ne mu lashe wasu kofuna a ƙarshen kakar bana," in ji ɗanwasan wanda kwantiraginsa zai ƙare a watan Yuli.
Muller ya buga wa Jamus wasa 131, inda ya zura ƙwallo 45, sannan ya lashe kofin duniya da ƙasar a shekarar 2014.
A kakar bana, wasa 24 Muller ya buga wa Bayern, inda ya ci ƙwallo ɗaya, amma wasa takwas kawai aka fara da shi.
Ƙungiyar ta ce za ta shirya wasa na musamman domin ban-kwana da ɗanwasan, sannan zai buga gasar kofin duniya na ƙungiyoyi wato Fifa Club World Cup wanda za a fara a ranar 15 ga watan Yuni a Amurka.