Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 12/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Muhammad Annur Muhammad

  1. IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur

    Ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN ta ce mambobinta sun cimma matsaya domin fara sayen man fetur daga matatar man Dangote kai-tsaye.

    Shugaban ƙungiyar ta IPMAN na ƙasa, Abubakar Garima, shi ya bayyana haka a Abuja ranar Litinin bayan uwar ƙungiyar ta gudanar da taro da mambobinta.

    Ya ce haɗin gwiwa da Dangote zai saka a samu wadataccen man fetur cikin sauki a faɗin ƙasar.

    "Ina farin cikin sanar da cewa matatar Dangote ta amince ta fara sayar mana da man fetur da kuma dizel kai-tsaye domin rarrabawa a defo-defo ɗin mu da kuma sauran gidajen mai," in ji Girima.

    Ya buƙaci mambobin IPMAN ɗin da su mara wa matatar Dangote baya, inda ya ce hakan zai kuma farfaɗo da yanayin hada-hadar man fetur da kuma rage ƙarancinsa da ake samu a ƙasar.

    Abubakar ya ce matakin zai kuma janyo bunƙasar ɓangaren man fetur ɗin Najeriya.

    Matatar ta Dangote ta yi alkawarin fara sayar da man fetur ɗin ga mambobin IPMAN sama da 30,000 da kuma gidajen mai 150,000 a faɗin ƙasar.

  2. Isra'ila na aikata 'kisan kare dangi' a Gaza - Yarima Bin Salman

    Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman (MBS) ya yi Alla-wadai da hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza, inda ya kwatanta hakan da "kisan kare dangi".

    Ana ganin wannan dai shi ne suka mafi zafi da wani jami'in gwamnatin Saudiyya ya yi tun fara yaƙin na Gaza.

    Da yake magana a taron ƙoli na ƙasashen Musulmi da Larabawa, Yariman ya kuma soki Isra'ila kan hare-hare da ta kai Lebanon da Iran.

    Isra'ilar dai ta musanta cewa dakarunta na aikata kisan kare dangi kan Falasɗinawa a Gaza.

    A wani mataki na kyautata alaƙa tsakanin Riyadh da Tehran bayan zamna tankiya a baya, Yarima Bin Salman ya kuma gargaɗi Isra'ila kan kaddamar da hare-hare a Iran.

    Wasu shugabanni sun bi sahun mutumin da ake wa kallo a matsayin shugaban Saudiyya wajen yin kira ga Isra'ila da ta janye baki-ɗaya daga Gaɓar Yamma da kuma Gaza.

    A ɗaya gafen, ministan harkokin wajen Saudiyya ya ce "gazawar al'ummomin ƙasashen waje" ne cewa ba a dakatar da yaƙin Gaza ba, inda ya zargi Isra'ila da haddasa yunwa a faɗin yankin.

  3. An sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin wasu kabilu a Nijar

    An yi nasarar sasanta rikicin zamantakewa da ya ɓarke tsakanin kabilun Hausawa da Fulani da Zabarmawa da kuma Buzaye a yankin Filingé na jihar Tillabery a Jamhuriyar Nijar, waɗanda ke faɗa da juna.

    Lamarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da tilastawa da yawa tserewa garuruwan su.

    Ɓangarorin sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta hanyar rantsuwa da Alkur'ani mai girma a karkashin jagorancin Malaman addini da sarakuna da kuma Hukumomi.

    Sheikh Abubakar Sheikh Usman Sanam na ɗaya daga cikin malamai da suka jagoranci wannan sasantawa, ya shaida wa BBC cewa tun kafin yanzu kabilun na zaune lafiya da juna kafin a fara samun zaman tankiya.

    Ya ce tun da farko shugaban mulkin sojin ƙasar ne Janar Abdulrahman Tchiani ya ba su umarni na neman hanyar sasanci domin warware matsalar da aka samu.

    "Kabilun sun ga abin da ya fi dacewa shi ne zama domin sasanta juna ta hanyar tuntuɓar manyan malamai da sarakuna da kuma shugabannin kabilun," in ji Sheikh Usman.

    Ya ce bayan da aka zo zama domin yin sasanta ɓangarorin, kowaye ya yi ƙorafin cewa ɗaya ɓangare ne ya takale ɗaya, amma malaman sun buƙaci dukkan kabilun da su kai zuciya nesa ta hanyar yafe wa juna.

    "Da aka zo wajen yin sulhu, za ka ga mutum na cewa ɗan wane ne ya kashe min ɗan'uwa ko ya takale ni, amma tun da muka yi musu nasiha kowa ya amince cewa ya yafe duk abin da aka yi masa har ma tare da rungumar juna," in ji Malamin.

    Sheikh Abubakar ya ce duka kabilun sun cuɗanya da juna har ma da auratayya tsakaninsu, inda a gida ɗaya za ka samu ɗaukacin kabilun a ciki.

  4. Trump na ci gaba da naɗe-naɗen muƙarraban gwamnatinsa

    Yayin da Donald Trump ke ci gaba da naɗe-naɗen muƙamai, kafofin watsa labaran Amurka sun yi hasashen cewa zai ba wa sanatan Florida, Marco Rubio muƙamin sakataren harkokin waje.

    Mista Rubio ba ya goyan bayan tallafin soji da Amurka ke ba Ukraine, ya kuma goyi bayan tsare-tsaren Trump na Amurka ce farko, wanda hakan ke nufin ƙasar za ta fitar da hannunta daga yaƙe-yaƙen ƙasashen ƙetare.

    Yaƙin Ukraine shi ne yafi jan hankali a sabuwar gwamnatin, Trump ya bayyana cewa zai kawo ƙarshen yaƙin cikin ruwan sanyi sai dai bai bayyana hanyar da zai bi ba wajen tabbar da hakan.

  5. Sojojin Amurka sun kai hare-hare tare da lalata wurare a Siriya

    Sojojin Amurka sun ce sun kai hare-hare kan wurare tara masu alaƙa da ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran a Siriya.

    Rundunar sojin Amurkar ta ce wurare biyu daga ciki, martani ne na hare-haren da aka kai wa sansanin sojinta a Siriya.

    Sojojin Isra'ila sun kai hare-hare biyu a Lebanon a ranar Litinin- a kudanci da kuma arewacin ƙasar.

    Ma'aikatar lafiyar Lebanon ɗin ta ce aƙalla mutane 15 ne aka kashe.

    Isra'ila ta ce Hezbollah ta harba kusan rokoki 200 a jiya Litinin, sai dai ta samu nasarar kakkaɓe da yawa daga ciki.

  6. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da hantsin Talata.

    Ku kasance da mu a wannan shafi na labarai kai-tsaye domin sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.