Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 12/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Ahmad Bawage da Muhammad Annur Muhammad

  1. Amurka ta ƙaƙabawa kwamandan RSF takunkumi

    Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Amurka ta ƙaƙaba wa wani babban kwamandan RSF na Sudan wasu tsauraran takunkumai, sakamakon samunsa da hannu a take hakkin bil'adama a yankin yammacin Darfur.

    Ma'aikatar baitulmali ta Amurka ta ce Abdel Rahman Joma'a Barakallah ya jagoranci gangamin cin zarafin fararen hula inda ta ce tana da ƙwararan hujjoji cewa a aikata cin zarafin da ke da alaƙa da jima'i.

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ƙaƙaba wa Mista Barakallah takunkumi a makon jiya tare da wani kwamandan RSF Osman Mohamed Hamid Mohamed.

    Rundunar RSF na ta fafatawa da sojojin Sudan don karbe ikon ƙasar tun watan Afrilun shekarar da ta gabata.

  2. Kotun duniya za ta saurari ƙararraki kan yankin Nagorno-Karabakh

    Nagorno-Karabakh

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun duniya ta ce tana da hurumin sauraron ƙararrakin Armeniya da Azerbaijan kan yankin Nagorno-Karabakh da ake takaddama a kai.

    Ɓangarorin biyu sun daɗe suna zargin juna da aikata laifukan da suka saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa .

    Ƙasar Azerbaijan dai ta sake karɓe iko da Nagorno Karabakh a shekarar da ta gabata bayan wasu hare-haren da ta kai da suka yi snadiyar ɗaiɗaita ƴan ƙabilar Armeniyawa kimanin dubu ɗari.

  3. An kama wasu ƴan Tiktok bisa zargin cin mutuncin shugaban Uganda

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Shugaba Yoweri Museveni ya kasance a kan karagar mulki tun 1986

    An tsare wasu ƴan ƙasar Uganda biyu bisa zargin cin mutuncin shugaba Yoweri Museveni, da uwargidan shugaban ƙasar Janet Museveni da ɗan shugaban ƙasar Gen Muhoozi Kainerugaba a dandalin sada zumunta naTikTok.

    Majistare Stella Maris Amabilis ta tasa ƙeyar David Ssengozi mai shekaru 21, wanda aka fi sani da Lucky Choice, da kuma Isaiah Ssekagiri, mai shekaru 28, zuwa gidan yari na Kigo har zuwa ranar Laraba lokacin da za su gurfana a gaban kotu.

    Ana zargin su da kalaman nuna kiyayya da yada munanan bayanai kan dangin shigaban ƙasar da wasu mawaƙan da ke da alaƙa da gwamnatin National Resistance Movement (NRM).

    A ranar Litinin da ta gabata, mutanen biyu sun bayyana a gaban kotu inda suka musanta zargin.

    An gurfanar da su tare da Julius Tayebwa, mai shekaru 19, wanda tuni aka gurfanar da shi a gaban kotu tare da tsare shi a gidan yari bisa zargin aikaita laifuka iri ɗaya.

  4. An sauya ranar wasan Real Madrid da Athletic a La Liga

  5. Fusunoni 15 sun mutu a tarzomar gidan yari a Equador

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rikicin da ya ɓarke a wani gidan yari a Ecuador wanda ya yi sanadin mutuwar fursunoni aƙalla 15 tare da jikkata wasu da dama.

    Bidiyon da aka ɗauka a gidan yarin Litoral da ke birnin Guayaquil da ke kusa da gaɓar teku ya nuna jerin gawawwakin da aka jibge a harabar gidan yarin.

    Ma’aikatar gidan yarin ta jihar ta ce an tura sojoji da ƴansanda domin kwantar da tarzomar a babban gidan yarin na Ecuador.

    Har yanzu dai hukumomin ƙasar ba su fitar da wani cikakken bayani kan waɗanda aka kashe ba amma sun ce ana gudanar da bincike kan abin da ya haddasa kazamin faɗan.

    Gidan yarin yana ɗauke da mambobin wasu gungun masu aikata manyan laifuka a Ecuador, waɗanda a lokuta da dama ke ci gaba da gudanar da miyagun ayyukansu yayin da suke fuskantar hukunci a gidan yari.

    A watan Satumba ne wasu ƴan bindiga suka harbe darektar gidan yarin El Litoral, María Daniela Icaza, inda suka buɗe wuta kan motarta.

    Rikici tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba da ke hammayya juna, ya yi sanadiyar mutuwar fursunoni sama da dari huɗu da sittin a gidajen yarin Ecuador cikin shekaru uku da suka gabata.

  6. Wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri sun kashe ɗan Sarkin Hausawa a Edo

    Benin

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne sun harbe wani ɗan Sarkin Hausawa har lahira a Benin, babban birnin jihar Edo.

    Rahotanni sun bayyana cewa ɗan mai suna Danladi, an kashe shi ne a shagon abokinsa mai nisan kilomita 100 da ofishin ƴansanda na Esigie da ke ƙaramar hukumar Oredo na jihar ta Edo.

    Wani shaida wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce Danladi na zaune ne a shagon abokinsa lokacin da ƴan ƙungiyar asirin suka isa a cikin wata mota ƙirar jeep GLK Benz tare da harbinsa har sau biyu.

    Ya ce, "Danladi mutumin kirki ne. Shi ne Sarkin Hausawan yankin, mutuwarsa ta janyo gagarumar giɓi a iyalansa da kuma matar da yake shirin aura," in ji shi.

    An ruwaito cewa matashin yana shirin ɗaura aure da amaryarsa a wata mai zuwa kafin afkuwar lamarin.

  7. Isra'ila ta ce ta buɗe sabuwar hanyar shigar da kayan agaji a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Sojojin Isra'ila sun sanar da buɗe sabuwar hanyar shigar da kayan agaji a Gaza, a daidai lokacin da wa'adin da Amurka ta bayar na inganta ayyukan jin-kai ke dab da ƙarewa.

    A watan da ya gabata sakataren harkokin wajen Amurka ya bai wa Isra'ila kwanaki 30 ta tabbatar motocin dakon kaya sun isa Gaza a kowacce rana.

    Cikin wasiƙar da Amurkar ta fitar, ta yi barazanar janye tallafin maƙamai da take bai wa Isra'ila idan ba ta bi umarnin ba.

    Kakakin hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Gaza, ta ce motocin dako 40 ne kawai ke shiga Gaza kowace rana, to amma jami'an Isra'ila sun ce sun yi abubuwan da Amurka ta nemi su yi.

  8. Firaiministan Senegal ya ɗau alwashin ramuwa kan harin da aka kai wa magoya bayansa

    Firaiministan Senegal Ousmane Sonko ya ɗauki alwashin ramuwar gayya kan abin da ya kira harin da abokan hamayya suka kai wa magoya bayan jam'iyyarsa gabanin zaɓen ƴan majalisa da za a gudanar ranar Lahadi.

    An kai wa ayarin Mista Sonko hari yayin ƴaƙin neman zaɓe a watan Oktoba.

    Mista Sonko ya bayyana a shafinsa na facebok cewa an shigar da ƙorafi amma ba wanda aka kama don haka jam'iyyarsa na da damar mayar da martani.

    A ranar Lahadi za a yi sabon zaɓen ƴan majalisa bayan rushe majalisar da shugaban ƙasar Bassirou Diomaye Faye ya yi a watan Satumba.

  9. Yadda sakamakon zaɓen Trump da Harris ya kasance

    ..
  10. Zargin baɗala ya janyo shugaban cocin Anglican ya yi murabus

    Justin Welby

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Justin Welby ya zama Archbishop ɗin Canterbury a cikin watan Fabrairu 2013

    Shugaban cocin Anglican, Justin Welby wanda shi ne Archbishop na Canterbury ya sanar da cewa zai sauka daga muƙaminsa sakamakon wani rahoto kan wani gawurtaccen mai cin zarafin yara da ke da alaƙa da Cocin na Ingila.

    Binciken ya gano cewa Justin Welby, mai shekaru 68, ya kasa ɗaukar mataki kan rahotannin cin zarafin da John Smyth ya yi wa yara maza da samari.

    A wata sanarwa da Mista Welby ya fitar ya ce: 'Bayan neman izinin mai martaba Sarki, na yanke shawarar yin murabus a matsayin Archbishop na Canterbury.'

    Ya ƙara da cewa 'a bayyane yake cewa dole ne in ɗauki alhakin kai na da na hukumomin coci kan rawar da ya taka a wannan batu na cin zarafi.

    Shugaban cocin dai ya fuskanci matsin lamba kan ya yi murabus bayan da aka bayyana cewa ya gaza ɗaukar mataki kan rahotannin cin zarafin da Smyth ya yi wa yara maza da matasa sama da 100.

    Rahoton na Keith Makin ya bayyana yadda Smyth ya tafka wannan mummunar ta'asa tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980.

    An zarge shi da kai hari kan yara maza 30 wadanda ya hadu da su a sansanonin bazara a shekarun 1970 da 1980, a gidansa na Winchester

    Rahoton da aka fitar a makon da ya gabata ya tabbatar da cewa "ya kamata a ce an kai rahotonsa ga ƴan sanda a shekarar 2013, lokacin da aka gabatarwa shugabannin Coci ciki har da Welby cikakkun bayanai game da cin zarafin da ya aikata.

    An bayyana rashin ɗaukar mataki daga Cocin a matsayin "damar da aka rasa don gurfanar da shi a gaban shari'a," in ji rahoton.

  11. Mutum goma sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

    Hatsarin mota

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum 10 a wani hatsarin mota a ƙauyen Yanfari da ke karamar hukumar Taura na jihar.

    Lamarin wanda ya afku a yau Talata, 12 ga watan Nuwamba a daidai hanyar Kano-Hadejia, ya kuma janyo jikkatar wani fasinja ɗaya.

    Wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, ya ce lamarin ya afku ne lokacin da wata motar ƙirar bas da ta fito daga jihar Kano zuwa Hadejia ɗauke fa fasinjoji 11, ta garu da wata tirela har ta kai suka jujjuya.

    "Nan take direban motar tare da wasu fasinjoji tara da ya ɗauka suka mutu," in ji sanarwar.

    Bayan afkuwar lamarin, tawagar sintiri na ƴansandan reshen Taura suka garzaya wajen, inda suka ɗauki gawawwakin waɗanda suka mutu zuwa babban asibitin Hadejia.

    Sun kuma ce sauran fasinja guda da ya jikkata na samun kulawa a cibiyar kiwon lafiya na Majia.

  12. Firaiministan New Zealand ya bai wa iyalan waɗanda aka ci wa zarafi a gidajen reno hakuri

    New Zealand

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiministan New Zealand ya ba da haƙuri a hukumance ga dubban iyalan mutanen da suka fuskanci cin zarafi a jihohi da kuma cibiyoyin bauta da gidajen reno da asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa a cikin sama da shekaru saba'in.

    Firaiministan Christopher Luxon ya shaida wa majalisar ƙasar cewa zaluntar yara da kuma marasa galihu abu ne mai tayar da hankali wanda bai kamata ya faru ba.

    Ya ce, "ina ba da haƙuri a madadin gwamnati ga dukkan wanda aka ci wa zarafi, ko aka cutar, da kuma waɗanda aka manta da su a lokacin da suke ƙarƙashin kulawar gwamnati. Ina neman afuwar dukkan waɗanda lamarin ya shafa a madadina da kuma gwamnatin da ta gabata.

    Neman afuwar na zuwa ne bayan wani bincike da majalisar ta gudanar ya gano cewa ana cin zarafin ƙananan yara, ana kuma tilastawa iyaye mata ba da yaransu ga wasu, yayin da ake azabtar da wasu masu lalurar ƙwaƙwalwa da lantarki.

  13. Gomman mutane sun mutu bayan da mota ta kwace ta faɗa cikin taron jama’a a China

    China

    Asalin hoton, EBU

    Wata mota da ta kwace ta faɗa cikin dandazon jama'a a kofar cibiyar wasanni da ke Kudancin China ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 35.

    Sannan wasu 43 kuma sun jikkata a lamarin da ya faru ranar Litinin a cewar hukumomi.

    Shugaba Xi ya yi kira da a hukunta wanda ya haifar da hatsarin motar.

    Kafofin yaɗa labaran China sun ruwaito cewa cikin mutanen da suka jikkata sun haɗa da tsofaffi da matasa da kuma yara.

    Ƴansanda sun ce sun kama wani yayin da yake ƙoƙarin tserewa, kuma yana cikin dogon suma sakamakon raunuka da ya ji.

    Lamarin ya faru duk da irin tsauraran matakan tsaro a birnin, wanda ke karɓar bakuncin wani bikin jama'a da kuma na sojoji.

    Ƴansanda sun ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa haɗarin ya afku ne sakamakon ɓacin rai da wani magoyin bayan kwallon kafa ya yi, saboda an raba dukiyarsa bayan ya saki matarsa.

    Sai dai saboda da dogon suma da ya shiga, hukumomi ba su samu damar yi masa tambayoyi ba.

  14. Labarai da dumi-dumi, An rantsar da Monday Okpebholo a matsayin sabon gwamnan Edo

    Monday Okpebholo

    Asalin hoton, Monday Okpebholo/Facebook

    An rantsar da Monday Okpebholo a matsayin sabon zaɓabɓen gwamnan jihar Edo.

    Sanata Okpebholo na jam'iyyar APC ya doke abokan karawarsa na jam'iyyar PDP, Barr. Asue Ighodalo da kuma na jam'iyyar Labour Olumide Akpata, a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 21 ga watan Satumba.

    An kuma ranstar da Hon. Dennis Idahosa a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

    Alkalin alkalan jihar ne Daniel Okongbowa ya jagoranci rantsar da su.

    Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar mai barin gado, Godwin Obaseki bai halarci taron rantsuwar ba.

  15. An sake kama fursunoni 51 da suka tsere daga gidan yarin Maiduguri

    Gidan yari

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya ta ce ta sake kama wasu fursononi cikin waɗanda suka tsere daga gidan yari a Maiduguri na jihar Borno lokacin ambaliyar ruwan da aka yi a watan Satumba da ya gabata.

    Kakakin hukumar, Abubakar Umar ya shaida wa BBC cewa an samu nasarar sake kama 51 daga cikin mutanen 271 da suka tsere.

    Ya kuma ce suna aiki haɗin gwiwa tsakaninsu da jami'an tsaro da dama, inda ya ce suna bai wa juna bayanan sirri da zai taimaka musu wajen yin aiki.

    "Lokacin da abin ya faru, fursunoni 271 ne suka tsere. Yanzu mun yi nasarar sake kama 51 daga cikinsu," in ji Umar.

    Ya ce suna ci gaba da ƙoƙari wajen ganin sun kama waɗanda suka rage.

    Bayanan sautiLatsa sama don sauraron rahoton
  16. Kotun kolin Ghana ta yi watsi da hukuncin da ya kori wakilai huɗu daga majalisa

    Kotun kolin Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun kolin Ghana ta yi watsi da hukuncin da kakakin majalisar dokokin ƙasar ya yanke a ranar 17 ga watan Oktoba, da ya kori wakilai huɗu daga majalisa.

    Kotun kolin ta ce hukuncin da kakakin majalisar ya yanke ya saɓa wa kundin tsarin mulki, inda a ranar 7 ga watan Nuwamba 2020 ya ayyana kujerar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Fomena a matsayin babu mai ita bayan ficewar ɗan majalisar daga jam'iyya mai mulki ta NPP.

    Wannan hukunci dai ya ba da damar komawa ci gaba da zaman majalisar bayan shafe makonni na rashin tabbas da kuma ɗage zaman tattaunawa da aka yi kan lamarin.

    Shugaban ɓangaren masu rinjaye da ya kai batun gaban kotu ya ce "wannan lokaci ne da kowa zai fito don nuna goyon baya ga tsarin dimokraɗiyya wanda ke buƙatar ladabi wanda shi ne hanyar da jam'iyyar NPP mai rinjaye ta bi don tabbatar da cewa mun yi komai bisa doka."

    "Muna sa ran takwarorinmu na ɗaya ɓangaren ciki har da shugaban majalisar za su mutunta sakamakon wannan shari'a don kai ƙasa gaba," in ji shi.

    Babban attoni janar na ƙasar Ghana Godfred Yeboah Dame ya shaida wa manema labarai cewa "a duk lokacin da kotu ta yanke hukunci, tana da cikakken tsari kuma dole ne a mutunta matakin da ta ɗauka."

  17. Hikayata 2024: Labarai 15 da suka yi fice a bana

    Hikayata

    A matakin ƙarshe na tantance labaran da suka yi fice a gasar rubutun gajeru ƙagaggun labarai ta mata zalla wato Hikayata ta bana, alƙalan gasar sun zaɓi labarai guda 15 da suka ce su ne suka yi fice a gasar ta bana.

    Harwayau alƙalan sun kuma zaɓi labarai guda uku da suka zama zakaru waɗanda nan gaba kaɗan za mu wallafa su.

    Da farko dai BBC Hausa ta samu labarai kimanin 450 da marubuta suka aiko mata inda kuma bayan tankaɗe da rairaiya aka miƙa labarai 400 ga alƙalai na sahun farko waɗanda duka malaman jami'a ne masana harshen Hausa inda suka tantance suka zaɓi guda 30.

    Daga cikin 30 din ne kuma alƙalan na ƙarshe suka zaɓi guda 15, inda uku daga ciki suka zaman zakaru sannan 12 suka cancanci yabo.

  18. Darajar Bitcoin ta zarta $80,000 karon farko bayan nasarar Trump

    Bitcoin

    Asalin hoton, Reuters

    Farashin kuɗin intanet na bitcoin ya tashi zuwa sama da dala $80,000 (fan 60,000) a karon farko, bayan nasarar da Donald Trump ya yi a zaɓen shugabancin Amurka.

    Hakan na faruwa ne kuma yayin da 'yan jam'iyyar Republican ke shirin kame jagorancin majalisar wakilan ƙasar, bayan tuni ta kame jagoranci a majalisar dattawa.

    Yayin da yake yaƙin neman zaɓe, shugaban mai jiran gado ya ci alwashin mayar da Amurka "babban birni na kuɗin kirifto".

    Yanzu kuma sai ga shi darajar kuɗin intanet mafi girma ta tashi da sama da kashi 80 cikin 100 a shekarar nan.

    Sauran kuɗaɗen kirifto, ciki har da dogecoin - wanda attajirin duniya kuma mai goyon bayan Trump, Elon Musk, ya yi ta tallatawa - na samun tagomashi.

    Kafin zaɓen, Trump ya ce zai ƙirƙiri rumubun rumbun bitcoin kuma ya taimaka wa cibiyoyin kuɗi da ke da alaƙa da intanet - inda ake hasashen zai janye dokokin taƙaita amfani da kirifto.

    Trump ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da zai fara yi shi ne korar shugaban hukumar saka ido kan hada-hadar kuɗi ta Securities and Exchange Commission (SEC), Gary Gensler.

    Mista Gensler, wanda Joe Biden ya naɗa a 2021, shi ne ya jagoranci yaƙi da kuɗaɗen kirifto a Amurka.

    "Idan gwamnatin Trump ta cire dokokin amfani da kirifto, da wuya a ce babu ƙarfafa gwiwa a harkar nan," a cewar Matt Simpson, wani mai sharhi a StoneX Financial, yana mai cewa hakan zai iya ɗaga darajar bitcoin zuwa $100,000.

    Aniyar Trump da ta ƙunshi rage haraji, da rage dokoki kan harkoki, ya jawo ƙarin zuba jari a wasu harkokin tun bayan nasarar tasa.

    Idan har jam'iyyarsa ta yi nasarar kame duka majalisun Amurka biyu, to za su iya samun damar ciyar da ƙudirin gwamnatinsa gaba ta hanyar amincewa da dokoki game da kowane ɓangare na kasuwanci.

  19. Ba na yi wa Tinubu hassada saboda jefa 'yan Najeriya cikin ƙunci ya yi - Atiku

    Atiku Abubakar

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ce ba ya yi wa Tinubu hassada, inda ya ce ya jefa ƴan Najeriya cikin kunci.

    Ɗan takarar shugaban ƙasar karkashin jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, na mayar da martani kan kalamai da fadar shugaban Najeriyar ta yi cewa yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na shugaban ƙasa.

    Wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar ranar Lahadi, ya soki Atiku kan ci gaba da sukar tsare-tsaren tattalin arzikin da shugaban, maimakon mayar da hankali kan matsalolin jam'iyyarsa.

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasar dai ya sha sukar tsare-tsare da gwamnatin Tinubu ta ɓullo da su, musamman na tattalin arziki, inda ya ce babu abin da za su haifar illa jefa ƴan Najeriya cikin kunci da wahala.

    Wata sanarwa da mai taimakawa Atiku na musamman kan yaɗa labarai Phrank Shaibu ya fitar ranar Litinin, Atiku ya ce sai Tinubu ya aiwatar da tsare-tsare kafin yake duba illolin da za su haifar.

    "Tinubu bai shiryawa mulki ba. Sai ya aiwatar da abu kafin yake duba illarsa daga baya. Wannan shi ya sa ya sanar da janye tallafin man fetur ba tare da kawo abin da zai rage wa ƴan ƙasar raɗaɗi ba.

    "Abin mamaki ne a yi iƙirarin cewa Atiku na kyashin Tinubu. Ba zai yi hassada da Tinubu ba saboda irin kunci da ya jefa ƴan Najeriya," in ji sanarwar.

    Atiku ya ce babu wani adalin shugaba wanda yake da zimmar ganin ƴan Najeriya cikin walwala da zai yi hassada da irin gallazawa da ake yi musu.

  20. Taron COP29 ya amince da sabon tsarin rage ɗumamar yanayi a duniya

    COP29

    Asalin hoton, UNFCCC

    Wakilai a taron sauyin yanayi na Cop29 da ake yi a Azerbaijan sun amince da wani sabon tsari na rage ɗumamar yanayi a duniya – ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da aka amince a yarjejeniyar Paris na rage gurɓatacciyar iskar da masana’atu ke fitar wa.

    Tun da farko ƙasashe da dama sun nuna fargaba kan yiwuwar ba wa ƙasashe masu arziƙi damar biyan ƙasashe masu tasowa kuɗi domin su rage gurɓata muhalli a madadinsu.

    Yarjejeniyar za ta ba ƙasashen masu arziƙi damar sanya hannun jari wajen samar da ingantaccen iska a ƙasashe matalauta.

    Shugaban COP29 ya yaba da matakin sai dai yace akwai buƙatar a ƙara jajircewa domin tabbatar da hakan.