Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 09/08/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, Juma'a, 09/08/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Muhammad Annur Muhammad da Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Mun fara kwato kayan da masu zanga-zanga suka sace'

    A Najeriya, Hukumomi a karamar hukumar Wudil a jihar Kano na cewa jami’an tsaro suna ci gaba da kwato kayayyakin da wasu bata-gari suka sace a sakatariyar karamar hukumar lokacin zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma.

    Baya ga sace-sacen da aka yi a cikin birnin Kano cikin kananan hukumomin jihar arba’in da hudu Wudil ce lamarin tarzomar ya fi muni inda ake cewa an sace dukiya ta miliyoyin naira.

    Shugabar karamar hukumar Hajiya Bilkisu Yakubu ta shaida wa BBC cewa ba su da ofishoshin da za su yi aiki saboda an lalata tare da kona sakatariyar karamar hukumar.

    Shugabar ta ce jami'an tsaro suna nan suna gudanar da bincike, tare da kwato wasu daga cikin kayayyakin.

    Ta kara da cewa ba waoi kayan gwamnati kadai aka washe ba har ma da wasu kayayyakin na 'yan kasuwa da sauran jama'a da aka sace.

    Hajiya Bilkisu ta ce, ko kadan ba za su iya kiyasin yawan asarar da aka tafka ba a dalilin abin da masu zanga-zangar suka yi.

    Haka kuma ta ce babu wasu da za a iya fitowa fili a zarga da aikata wannan ta'asa, illa dai ta ce bincike zai gano kamar yadda jami'na tsaro suka lashi takobi, ganin yadda suke bi suna kwato wasu daga cikin abubuwan da aka sace.

  2. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da maƙwabtanta da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Juma'a - haji babbar rana.

    Ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan kasancewa tare da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba. Da fatan kamar kullum za ku ci gaba da bibiyarmu sau da ƙafa.

    Mu fara da wannan karin maganar - Allura cikin ruwa mai rabo ka ɗauka.